Me ya sa ƴanwasan Barcelona ke yawan jin rauni a bana?

Barcelona

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 6

Koshin lafiyar ƴan wasa na ɗaya daga dalilin da suka sanya Barcelona ta taka rawar gani a bara a dukkan fafatawa, sai dai a bana ta gamu da kalubale tun daga farkon kakar da muke ciki.

Yawan ƴan wasan ƙungiyar da ke jinya a kakar nan ta kai ga mai horaswa Hansi Flick ba ya iya zuba fitattun ƴan wasan 11 a lokaci guda.

Sai dai duk da haka ƙungiyar kan yi amfani da matasanta, domin ganin ta taka rawar gani duk da wasu daga manyan ƴan ƙwallonta na jinya.

Hakan bai hana Barcelona zama ta biyu ba a kan teburin La Liga da maki 22 da tazarar biyar tsakani da Real Madrid mai jan ragama.

Fitattun ƴan ƙwallon Barcelona da suka ji rauni a bana

Robert Lewandowski da Dani Olmo da Alejandro Balde da Frenkie de Jong da Fermin Lopez da Lamine Yamal da Raphinha da Ferran Torres da kuma Pedri.

Sauran sun haɗa da Marc-Andre ter Stegen da Gavi da Joan Garcia da Andreas Christensen da kuma Pedri na baya bayan nan da yake jinya.

Bari mu fara da gurbin masu cin ƙwallaye a Barcelona:

Robert Lewandowski ya ɗauki kwanaki yana jinya a raunin da ya ji lokacin da ya buga wa kasarsa Poland wasan neman shiga gasar kofin duniya, daga nan ya koma Sifaniya da rauni.

Kuma karo na biyu da Lewandoeski ke jinya.

Barcelona

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Raphinha

Raunin Raphinha babbar koma baya ce ga Barcelona, wadda ke fatan taka rawar gani a kaka ta biyu da Hansi Flick ke jan ragama, bayan lashe La Liga da Copa del Rey da Spanish Super Cup a kakarsa ta farko a Sifaniya.

Tun farko an sa ran ɗan ƙwallon zai yi jinyar mako uku, kenan sai cikin watan Nuwamba zai koma taka leda.

Lamine Yamal

Wani ɗan wasan gaban da ya yi jinya shi ne Lamine Yamal, wanda kusan wata ɗaya ya yi baya taka leda, koda yake ya murmure amma dai bai koma kan ganiya ba ɗari bisa ɗari.

Haka shi ma Ferran ya ci karo da cikas, wanda ya yi kwana takwas yana jinya.

A fannin masu buga tsakiya

Fermin ya fi kwana 25 yana jinya, yayin da Olmo ya kai kwana 20 kuma har yanzu bai warke ba.

De Jong, yana jinyar kwana 10, wanda shi ma mai tsaron baya ne.

A gurbin masu tsare baya

Balde na jinya kusan wata ɗaya, yayin da ba a san ranar da Christensen zai murmure ba.

Sabon ɗan wasa Garci shi ma ya yi sama da wata yana jiya, wanda ya fara yin atisaye.

Mai tsaron raga Ter Stegen na jinyar sama da wata uku, yayin da Gavi ya kusan wata biyu.

Pedri ya shiga jerin ƴanwasan Barcelona da ke jinya

Pedri

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Ɗan wasan tawagar Sifaniya mai taka leda a Barcelona, Pedri ya ci karo da koma baya, zai kuma yi jinya.

Ranar Laraba Barcelona ta tabbar da cewar matashin mai shekara 22 ya ji rauni.

Sai dai ƙungiyar ba ta fayyace tsawon lokacin da zai yi jinyar ba, balle a san ranar da zai koma murza leda.

Pedri ya buga wa Barcelona wasa 41 a jere.

Kenan ba zai yi wa Barcelona wasan da za ta fuskanci Elche ba, sakamkon jan katin da ya samu a fafatawar El Clasico ranar Lahadi.

Pedri ya yi wasa 213 a dukkan fafatawa a Barcelona, tun bayan da ya koma ƙungiyar daga Las Palmas a 2020 yana da shekara 17 a lokacin.

Raunin da ƴanwasan Barcelona suka ji ya ƙunshi kowanne gurbi

Daga tsakiyar watan Oktoba Barcelona na ɗawainiya da ƴanwasa takwas da suka ji raunin da ya shafi tsoka tun daga fara kakar bana.

Kuma raunukan sun shafi ƴanwasa masu tsare raga da masu tsare baya da masu buga tsakiya da kuma masu cin ƙwallo.

Dalilin da ƴan wasa ke yawan jin rauni

Raunin tsoka/ana yawan jin rauni a wajen nama mai laushi

Yawancin raunin na faruwa ne ta hanyar tsagewar tsoka, tsokar cinya, da kuma raunin ƙashi (maimakon karyewar ƙashi) wanda ke nuna aiki ya yi yawa, gajiya ko rashin murmurewa.

An samu raunuka guda 11 da suka shafi tsokar cinya (cikin watanni kusan 2) a ƙungiyar.

Manyan wasanni da gajerun lokutan murmurewa

Wasanni a gasar La Liga daga gida da buga gasar kofunan ƙalubale da ta Turai, da yi wa tawaga ta ƙasa da ƙasa wasanni: ƙungiyoyi a zamanin yau ba su da "lokacin hutu".

Barcelona ta fuskanci matsaloli sakamakon kiran da kasashe suke yi musu don buga wasanni sai su koma ƙungiyar da matsaloli.

Misali, Lamine Yamal ya buga wa tawagar Sifaniya wasa, sai kuma ya ji raunin da ya koma Barcelona ya yi jinya.

Ƙarancin ƴanwasa

Da zarar ƙungiya ta rasa manyan ƴanwasanta da ke jinya, sai ta koma amfani da waɗanda ke da lafiya, sai su kuma wasannin su yi musu yawa su fara jin rauni da kuma tarin gajiya.

Yawan Fama raunin da bai kammala warkewa ba

Wasu yanwasa na fama da raunin da suke yawan fama shi misali na tsokar cinyar kafa, inda ƙungiya kan ɗora su kan tsarin da za su bi su warke su koma taka leda.

Misali, Ronald Araujo, an dora shi kan tsari na musamman domin ya samu saukin raunin.

Haka shi ma Gavi da yake fama da rauni a gwiwa, wanda an san zai ɗauki lokaci kafin ya koma taka leda.

Akwai rashin jituwa tsakanin ƙungiya da ƙasa kan amfani da ƴanwasa

Ana ta samun takaddama tsakanin tawagar ƙasa da ƙungiya kan yadda kasa za ta riƙa amfani da ɗan wasa idan kuma ya ji rauni ta hakura da shi.

Raunin da Yamal ya ji ta kai ga kociyan Barcelona ya caccaki Sifaniya da cewar sun yi amfani da matashin fiye da kima, kuma sun ja musu kunnen cewar zai iya jin rauni.

Yawan atisaye da kuma gajiyar da ke bin wasu ƴanwasa kafin fara kaka

Wasu ƴanwasa kan fara cin karo tun daga atisayen tunkarar kakar bana ga yawan tafiye-tafiyen ƴanwasa a duk mako, wani lokaci a jirgin sama sannan su buga wasanni, kenan babu isashen hutu a tare da su.

Saboda haka Barcelona na bukatar inganta yin atisaye da rage yawan shi da sauya ƴanwasa akai-akai, watakila sai ta samu sauƙin yawan rauni.

Raphinha

Barcelona

Asalin hoton, Getty Images

Raunin da ya ji: Raunin tsokar cinyar kafa

Ranar da ake sa ran zai koma wasa: Tun farko an sa ran zai koma wasa ranar 26 ga watan Oktoba a wasan Real Madrid, amma sai hakan bai yiwuba.

Ɗan wasan tawagar Brazil na fama da wannan raunin da ya ƙi warkewa da wuri, wanda tun farko ba a ɗauka zai yi doguwar jinya ba.

Joan Garcia

Barcelona

Asalin hoton, Getty Images

Raunin da ya ji: Raunin gwiwa

Ranar da ake sa ran zai koma wasa: Ranar 23 ga watan Nuwamba a karawa da Athletic Bilbao.

Har yanzu sabon ɗan wasan da ta ɗauka Garcia na jinya, bayan tiyatar da aka yi masa a gwiwa, kuma rauni ne mai wuyar sha'ani da ake sa ran zai warke a cikin watan Nuwamba.

Marc-Andre ter Stegen

Barcelona

Asalin hoton, Getty Images

Raunin da ya ji: Ciwon baya

Ranar da ake sa ran zai koma wasa: Ba a fayyace ba.

Mai tsaron ragar Barcelona na jinya sakamakon ciwon baya, kenan ana cewa Ter Stegen ɗan kasar Jamus zai koma taka leda a farkon kakar baɗi.

Gavi

Gavi

Asalin hoton, Getty Images

Raunin da ya ji: Gwiwa

Ranar da ake sa ran zai koma wasa: Ba a fayyace lokaci ba.

Gavi zai ci gaba da jinya watakila mako huɗu zuwa biyar, saboda raunin gwiwa, wanda ake ganin ɗan kasar Sifaniya na bukatar tiyata.

Robert Lewandowski

Lewandowski

Asalin hoton, Getty Images

Raunin da ya ji: Raunin tsokar cinyar kafa

Ranar da ake sa ran zai koma wasa: Ya fara atisaye

Lewandowski, wanda ake sa ran zai bar Barcelona a karshen kakar bana, ya ji rauni wanda tun farko aka ce sai cikin Nuwamba zai koma fili, amma an ce ya fara atisaye shi kaɗai.

Dani Olmo

Dani Olmo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dani Olmo

Kalal raunin da ya ji: Yagewar tsokar dunduniya

Ranar da ake sa ran zai koma wasa: Ranar 9 ga watan Disamba a wasan Celta Vigo.

Olmo ya ji raunin yagewar tsokar dunduniya a lokacin da yake buga wa tawagar Sifaniya tamaula, wanda ake cewa sai cikin watan Nuwamba zai murmure.