Zaɓi biyu da suka rage wa PDP gabanin babban zaɓen Najeriya na 2027

Tambarin jam'iyyar PDP

Asalin hoton, X/PDP

Lokacin karatu: Minti 4

PDP ita ce babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, kuma ɗaya daga cikin mafi daɗewa. Jam'iyyar ce ta mulki Najeriya daga 1999 lokacin da ƙasar ta koma mulkin dimokuraɗiyya har zuwa shekara ta 2015, sai dai rikicin da ke addabar jam'iyyar ta sa ta yi asarar jihohi 31 ga jam'iyyar APC mai mulki.

Jam'iyyar da ya kamata ta zamo barazana, a yanzu tana cikin mawuyacin hali inda ta dare zuwa ɓangarori, hakan ya sanya tana cikin barazana gabanin babban zaɓen ƙasar na 2027.

Yayin da ake faman kai-komo a kotu, yanzu jam'iyyar ta dare zuwa gida biyu, ɗayan ɓangaren na ƙarƙashin gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde da na Bauchi Bala Mohammed.

Ɗayan ɓangaren kuma na yin biyayya ga ministan babban birnin Najeriya, Abuja, Nyesom Wike, wanda ya ƙi fita daga jam'iyyar duk da cewa yana riƙe da muƙami a gwamnatin Bola Tinubu ta jam'iyyar APC.

Yanzu akwai kimanin ƙararraki 9 a gaban kotu game da halin da PDP ke ciki. Lamarin ya sanya gwamnonin jam'iyyar da dama suka fice daga cikinta.

A baya-bayan nan ne kotun ɗaukaka ƙara ta sake tabbatar da hukuncin wata ƙaramar kotu kan cewa kada hukumar zaɓen Najeriya ta amince da zaɓen shugabannin jam'iyyar da aka yi a garin Ibadan na jihar Oyo a ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamban 2025.

A taron na garin Ibadan ne ƴaƴan jam'iyyar suka zaɓi Tanimu Turaki a matsayin shugaban jam'iyyar na ƙasa da kuma Taofeek Arapaja a matsayin sakataren jam'iyyar na ƙasa, da kuma sauran shugabanni.

A lokacin taron ne jam'iyyar ta kori ministan Abuja Nyesom Wike, da Ayo Fayose da wasu manyan jam'iyyar bisa zargin su da ayyukan zagon-ƙasa.

Wasu masu ruwa da tsaki a jam'iyyar sun buƙaci ɓangaren Tanimu Turaki ya amshi hukuncin kotun ɗaukaka ƙara na baya-bayan nan, tare da sulhuntawa da ɓarin Nyesom Wike, ta yadda jam'iyyar za ta sake yin wani babban taro, kasancewar wasu na tsoron cewa hukumar zaɓen Najeriya ta INEC na iya haramta mata fitar da ƴan takara a zaɓen 2027 idan rikicin ya ci gaba.

Yayin da jam'iyyar ke fama da wannan rikice-rikice, jadawalin hukumar zaɓe ya nuna cewa jam'iyyu za su yi zaɓen fitar da gwani ne tsakanin 23 ga watan Afrilu zuwa 30 ga watan Mayun wannan shekara ta 2026.

Wane zaɓi ya rage wa PDP kafin zaɓen 2027?

PDP flag wit pesin inside car

Asalin hoton, Olukayode Jaiyeola/NurPhoto via Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wasu ƴaƴan jam'iyyar na ganin cewa ya kamata a janye duk wasu ƙararraki da ke gaban kotu game da rikicin shugabancin jam'iyyar.

Tsohon shugaban majalisar dattijan Najeriya, Bukola Saraki ya roƙi jagororin jam'iyyar da masu ruwa da tsaki su jefar da makaman yaƙinsu, su sake tsara wani babban taron ƙasa wanda zai yi daidai da dokokin hukumar zaɓe.

"Matsayata ita ce kotun ƙoli ta riga ta yanke hukunci. amma idan muka lura da jadawalin zaɓen 2027 da hukumar INEC ta fitar, a bayyane yake cewa babu lokacin da za mu jira hukuncin kotun ƙoli."

Saraki ya ce idan har ba a warware matsalar jam'iyyar ba, PDP ba za ta iya fitar da ƴan takara ba domin zaɓen 2027.

Ya ce ya kamata jam'iyyar ta mayar da hankali kan gyara kanta a maimakon ɗaukaka ƙarar zuwa kotun ƙoli.

"Na yi amannar cewa hanya ɗaya da muke da ita, ita ce mu janye duk wasu ƙararraki mu yi amfani da tsarin da muke da shi a yanzu, mu gudanar da babban taron ƙasa daidai da jadawalin hukumar zaɓe."

Saraki ya ce shugabannin jam'iyyar waɗanda ba su samu yadda suke so ba daga ƙararrakin da suka shigar a kotu, ya kamata su yi la'akari da 'abin da zai fi dacewa ga jam'iyyar ta PDP a zaɓen 2027 da kuma bayan hakan.'

Saraki ya ce akwai ƴaƴan jam'iyyar da ke son yin takara a zaɓen 2027 ƙarƙashin lemar jam'iyyar, saboda haka wannan lokaci ne da ya kamata a taimaka musu.

A wani ɓangaren kuma, sanata mai wakiltar mazaɓar Kogi ta tsakiya a majalisar dattijan Najeriya, Natasha Akpoti Uduaghan, ita ma ta yi tsokaci kan rikicin na PDP.

Ta ce ya kamata dukkanin ɓangarorin su sasanta da juna sannan su manta da batun ƙararraki a kotu.

Ta ce 'lokaci ne na ƙoƙarin ƙarfafa dimokuradiyya a cikin gida' gabanin babban zaɓen 2027.

Ta ce ci gaba da jan ƙararraki a kotu ba zai fitar da jam'iyyar ba, kuma hakan ba zai yi wa masu son yin takara ƙarƙashin jam'iyyar amfani ba.

"A lokaci irin wannan, ya kamata mu yi watsi da son rai, mu mayar da hankali kan abin da zai amfani jam'iyyarmu da ƙasar baki ɗaya," in ji Natasha.

Masana siyasa na ganin cewa zaɓi biyu da suka rage wa jam'iyyar su ne: ko dai duka ɓangarorin biyu su sulhunta, su watsar da bambance-bambancen da ke tsakaninsu ko kuma babu tabbas kan halin da jam'iyyar za ta faɗa idan ta ci gaba da bibiyar ƙararrakin da aka shigar a kotu.

Jerin jihohin da APC ke mulki da kuma na PDP

Akwa Ibom state govnor Umo Eno, Enugu govnor Peter Mbah, Bayelsa govnor Douye Diri, and Delta state govnor Sheriff Oborevwori

Asalin hoton, Uno Emo/X, Peter Mbah/X, Duoye Diri/X, Sheriff Oborevwori/X

Abia - Alex Otti - Labour Party

Adamawa - Ahmadu Umaru Fintiri - APC

Akwa Ibom - Umo Eno - APC

Anambra - Charles Soludo - APGA

Bauchi State - Bala Muhammed- PDP

Bayelsa - Douye Diri - APC

Benue - Hyacinth Alia - APC

Borno - Babagana Zulum - APC

Cross River - Bassey Otu - APC

Delta - Sheriff Oborevwori - APC

Ebonyi - Francis Nwifuru - APC

Edo - Monday Okpebholo- APC

Ekiti - Biodun Oyebanji - APC

Enugu - Peter Mbah -APC

Gombe - Muhammad Inuwa Yahaya - APC

Imo - Hope Uzodinma -APC

Jigawa - Umar Namadi - APC

Kaduna - Uba Sani - APC

Kano - Abba Kabir Yusuf - APC

Katsina - Dikko Umaru Radda - APC

Kebbi - Nasir Idris - APC

Kogi - Ahmed Usman Ododo - APC

Kwara - AbdulRahman AbdulRazaq - APC

Lagos - Babajide Sanwo-Olu - APC

Nasarawa - Abdullahi Sule - APC

Niger - Mohammed Umar Bago - APC

Ogun - Dapo Abiodun - APC

Ondo - Lucky Aiyedatiwa - APC

Osun - Ademola Adeleke - Accord Party

Oyo - Seyi Makinde - PDP

Plateau - Caleb Mutfwang - APC

Rivers - Siminalayi Fubara - APC

Sokoto - Ahmad Aliyu - APC

Taraba - Agbu Kefas - APC

Yobe - Mai Mala Buni - APC

Zamfara - Dauda Lawal - APC

FCT: Nyesome Wike