Ko komawar gwamnan Zamfara APC za ta rage matsalar tsaron jihar?

Asalin hoton, @Daudalawal001
A ranar Litinin ne Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa rikicin cikin gida da kuma shari'o'in da suka dabaibaye tsohuwar jam'iyyarsa ta PDP ne manyan dalilan da suka sa ya fice daga jam'iyyar ya koma APC.
Gwamnan ya sanar da sauya sheƙarsa daga PDP zuwa jam'iyya mai mulki ta APC a hukumance bayan wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar da ke Gusau.
A wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa ficewar gwamnan zuwa APC ya zama dole saboda muradun al'ummar Zamfara.
Gwamna Dauda Lawal ya ce ya yi baƙin ƙoƙarinsa don ganin ya sasanta rikicin da ke tsakanin ɓangarorin jam'iyyar domin tabbatar da haɗin kai da kuma damar tsayar da ƴan takara a zaɓuka masu zuwa.
Bayan batun siyasa, wani abu da ya ɗauki hankalin mutane shi ne batun cewa komawar gwamnan za ta taimaka masa wajen samun ƙarin haɗin kai da gwamnatin tarayya domin magance matsalolin tsaro.
A wata sanarwa da darakta-janar na harkokin hulɗa da jama'a na ofishin gwamnan, Salihu Anka ya fitar, ya ce, "ta hanyar komawa APC, gwamnan ya ƙara tabbatar da ƙoƙarinsa na ƙara haɗin kai, inganta tsaro da kuma tabbatar da cewa Zamfara ta samu cikakken haɗin kai da goyo bayan gwamnatin tarayya."
Jihar Zamfara na ɗaya daga cikin jihohin da matsalar tsaro ta fi ƙamari a faɗin Najeriya, inda ɓarayin daji ke afkawa garuruwa da kauyuka da kashe mutane da satar wasu domin neman kuɗin fansa, ga kuma sacewa ko kwace amfanin gonar da manoma suka shuka.
Za mu riƙa aiki da fahimta ɗaya - Gwamnatin Zamfara
Suleiman Bala Idris, shi ne mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, kuma ya bayyana cewa komawarsu APC za ta sa su ƙara fahimtar juna da gwamnatin tarayya domin sauƙin gudanar da aiki.
"Dama can Gwamna Dauda Lawal ya daɗe yana ƙoƙarinsa wajen samar da tsaro. Daga daga ciki akwai samar da Askarawa da bayar da motoci ga jami'an tsaro da sauransu."
Suleiman Baya ya ce kasancewar gwamnatin jihohi ba su da iko kan jami'an tsaro, shi ya sa yake da kyau ya zama ana aiki tare.
"A baya an samu saɓani sosai musamman kan fahimtar yaya ya kamata a ɓullo wa matsalar. Wannan ya sa muke ganin komawa APC za ta taimaka wajen ƙara fahimtar juna da samun daidaito a hanyoyin da za a bi domin magance matsalar," in ji shi.
Sai dai ya ce ba maganar jam'iyya ba ce, inda ya ƙara da cewa tun dama gwamnatin jihar Zamfara na neman agajin gwamnatin tarayya kuma tana samu, "amma yanzu baki zai zo ɗaya, shirin zai zama ɗaya."
Batun sulhu da ƴanbindiga
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Daga cikin manyan abubuwan da suka daɗe suna jan hankali shi ne batun sulhu da ƴanbindiga a jihar.
Gwamnan jihar Dauda Lawan ya daɗe yana cewa zai iya yin sulhu da ƴanbindiga da ke addabar jihar ne kawai idan har sun ajiye makamansu.
Batun yin sulhu da ƴanbindiga lamari ne da ke haifar da zazzafar muhawara a Najeriya, bayan shafe sama da shekara 10 ana fama da ayyukan ƴan fashin daji a arewa maso yammacin Najeriya, lamarin da ya yi sanadiyyar rasa dubban rayuka da tarwatsa al'umma da durƙusar da ilimi da kasuwanci.
A wata hirarsa da BBC, Gwamna Dauda ya bayyana cewa "Akwai da yawa waɗanda aka cutar da su, wasu an kashe iyayensu wasu matansu, saboda haka sai a duba me za a yi masu saboda sun rasa dukiyarsu, ba wai kullum a riƙa fitfita ƴanbindiga ba," in ji Dauda.
Ya ƙara da cewa sai ƴanbindigar sun daina kashe mutane kuma sun ajiye makamansu sannan za a iya yin sulhu da su.
A baya dai, Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal Dare ya sha nanata cewa har ba zai yi sulhu da ƴan fashin daji ba.
Yayin zantawarsa da BBC gwamnan ya ce ya ɗauki wannan matsaya ce ganin cewa a bayan an sha yin sulhu da 'yan bindigar, amma ba sa mutunta alƙawurran da aka yi da su a baya.
Komawar na da tasiri?
Kabiru Adamu, masanin tsaro ne kuma shugaban kamfanin Beacon security and consulting, ya ce akwai hanyoyi da yawa da ake iya nazarin matsalolin tsaro, waɗanda a cewarsa suke taimakawa wajen magance matsalar.
"Akwai gundarin abubuwan da ke jawo matsalar tsaro da suke da nasaba da tsaron, akwai kuma waɗanda dalilai ne na siyasa da zamantakewa da tattalin arziki da ɗumamar yanayi da ke jawo matsalar tsaron."
Ya ce a wannan mahangar ne za a iya cewa komawar Dauda Lawal ba dole ba ne ya taimaka wajen magance matsalar tsaro, inda ya ce sai dai a ɓangaren haɗin kai da za a iya samu.
"A baya ana raɗe-raɗin cewa gwamnan jihar da ƙaramin minista ba sa ga maciji. Amma yanzu da komawarsa, za su iya samun haɗin kai su yi aiki tare."
Kabiru Adamu ya ce akwai matsalolin zamantakewa da ɗumamar yanayi da tattalin arziki, waɗanda a cewarsa mulki mai kyau zai fi amfani sama da canja jam'iyya kawai.
"Irin salon shugabancin da ya nuna ne za su fi muhimmanci, ba wai komawar ba ce kawai. Don haka magance asalin matsalolin ne za su fi muhimmanci. Wani abu mai muhimmanci shi ne ba sayen jirage marasa matuƙa da makamai ba ne magance matsalar tsaro."
Ya ce amfani da tsarin tsaron al'umma waɗanda suke da matakai guda shida, "ciki har da saka jama'a da na'urori da kimiyya da magance matsalolin tattalin arziki da sauransu wajen fuskantar matsalolin da suka fi muhimmanci."
Shin siyasa na da hannu a rikicin?
Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta daɗe tana fama da matsalolin tsaro, lamarin da ya sa ake kallon jihar tamkar wata cibiyar masu garkuwa da mutane a Najeriya.
Sai dai duk da babu tabbas, an daɗe ana alaƙanta matsalar da rikice-rikicen siyasa, lamarin da masu bibiyar lamurran tsaro suke ganin ya taimaka wajen ta'azzara matsalar tsaron tare da kawo cikas ga ƙoƙarin samun nasarar kawar da ita.
A babban zaɓen Najeriya na shekarar 2023 ne Dauda Lawan Dare ya doke Bello Matawalle a zaɓen gwamnan jihar. Sannan daga baya Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya naɗa Matawalle a matsayin ƙaramin ministan tsaron ƙasar.
Ƴan jihar sun yi tunanin za a samu haɗin kai tsakanin gwamnan na ministan, wanda tsohon gwamna ne domin magance matsalolin tsaron, amma sai rigima da cacar-baki suka ɓarke a tsakanin manyan masu riƙe da madafun ikon jihar.
Da farko, Gwamna Dauda ne ya buƙaci Matawalle ya yi murabus a muƙaminsa na minista har sai ya wanke kansa, yana mai zarginsa da taimaka wa ƴan bindiga ta hanyar gayyatarsu gidan gwamnatin jihar da kuma biyansu kuɗin fansa daga lalitar gwamnati.
Sai dai a martaninsa, Matawalle ya musanta zargin tare da cewa shi kaɗai ne ya rantse da Al'Kur'ani cewa ba shi da alaƙa da ƴanbindiga.
Sannan ministan ya ƙalubalanci wanda ya gaje shi ya fito ya rantse da Al'ƙura'ni mai tsarki cewa ba shi da hannu a matsalar tsaron Zamfara.
Shi ma ɓangaren Sanata Abdul'aziz Yari na jam'iyyar APC ya fitar da sanarwa ta martani da gwamna Dauda na jam'iyyar PDP game da kalamansa kan Matawalle.
Cikin sanarwar, Abdul'aziz Yari, ya gargaɗi Gwamna Dauda cewa ya daina ɗora laifin matsalar tsaro kan Bello Matawalle, ya mayar da hankali ga aikinsa.
Ɓangarorin biyu sun daɗe suna sukar juna kan lamurran da suka shafi jihar Zamfara tun bayan zaɓen 2023 da Dauda Lawan Dare na jam'iyyar PDP ya kayar da Bello na jam'iyyar APC.
Masana na ganin wata al'ada ce a Najeriya duk gwamnan da ya hau idan ya gaji matsala zai dinga dora matsalar ne ga wanda ya gada. "Domin shi kansa Bello Matawalle lokacin da yana gwamna ya zargi wanda ya gada Abdul'aziz Yari,"
"Yanzu kuma ga shi yana sa'insa da wanda ya gaje shi Gwamna Dauda – don haka ba sabon abu ba ne a siyasar Najeriya," in ji Barista Audu Bulama Bukarti mai sharhi kan lamurran yau da kullum kuma masanin sha'anin tsaro a Najeriya.
Masanin tsaron ya ƙara da cewa da gwamnan jihar mai ci da kuma ƙaramin ministan tsaro babu wanda Allah ya ɗora wa alhakin matsalar tsaron Zamfara kamar su biyu.
"Alhakin tafiyar da gwamnatin jiha na kan gwamna yayin da kuma ƙaramin ministan tsaro, wakili ne na jihar Zamfra a tarayya. Amma kuma sai ga shi an ga sun koma suna caccakar juna."
"Rashin tsaro matsala ce da ta shafi kowa – ta shafi PDP ta shafi APC da dukkanin ƙabilu da addinai."
"Don haka abin takaici ne yadda ake siyasantar da matsalar tsaron maimakon su hada kansu su yaki matsalar," a cewar Barista Bukarti.











