Zan yi sulhu da ƴanbindiga ne kawai idan sun miƙa wuya - Dauda

Asalin hoton, facebook/Dauda Lawal
Gwamnan jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya, Dauda Lawan Dare ya ce zai iya yin sulhu da ƴanbindiga da ke addabar jihar ne kawai idan har sun ajiye makamansu.
Hakan na zuwa ne yayin da wani sulhu da gwamnatin jihar Kaduna - wadda ke fama da matsalar tsaro iri ɗaya da ta Zamfara - ta yi da irin waɗannan ƴan fashi, lamarin da ake ganin ya kawo zaman lafiya a sassan jihar da suka daɗe suna fama da tashin hankali.
Batun yin sulhu da ƴanbindiga lamari ne da ke haifar da zazzafar muhawara a Najeriya, bayan shafe sama da shekara 10 ana fama da ayyukan ƴan fashin daji a arewa maso yammacin Najeriya, lamarin da ya yi sanadiyyar rasa dubban rayuka da tarwatsa al'umma da durƙusar da ilimi da kasuwanci.
A hirarsa da BBC, Gwamna Dauda ya bayyana cewa ba wai ba za a iya yin sulhu da ƴanbindigar ba ne, "Amma ko da za ka yi sulhu ka yi shi a kan gaskiya, ai.
"Akwai da yawa waɗanda aka cutar da su, wasu an kashe iyayensu wasu matansu, saboda haka sai a duba me za a yi masu saboda sun rasa dukiyarsu, bawai kullum a riƙa fitfita ƴanbindiga ba," in ji Dauda.
Ya ƙara da cewa sai ƴanbindigar sun daina kashe mutane kuma sun ajiye makamansu sannan za a iya yin sulhu da su.
Gwamna Dauda ya bayyana cewa suna samun nasara a yaƙin da suke da ƴanbindiga, "An kashe ƴan ta'adda fiye da 50 a ranar Juma'a a garin Tingar Fulani, wajen Zurmi da Shinkafi."
"Akwai manya-manyan kachalloli da yanzu haka sun tafi lahira, wadanda suke tare da Bello Turji, akwai Sani Mainasara da Sani Black da Kachallah Auta, Audu Gajere da Kabiru Jangero, Dangajere da makamantansu, duk an hallakasu," a cewar Dauda Lawal.
Gwamnan ya ce wannan nasara da ake samu za a ci gaba da samunta har sai na kai ƙarshen lamarin, Kodai su aje makamansu ko kuma mu ba zamu bar su ba."
A baya dai, Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal Dare ya sha nanata cewa har ba zai yi sulhu da ƴan fashin daji ba.
Yayin zantawarsa da BBC gwamnan ya ce ya ɗauki wannan matsaya ce ganin cewa a bayan an sha yin sulhu da 'yan bindigar, amma ba sa mutunta alƙawurran da aka yi da su a baya.
''An yi sulhun nan a baya ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba, amma an kasa cimma ake abin da ake so'', in ji gwamnan.
Duk da dai ikirarin hukumomi na yaƙar ƴanbindiga a yankin arewa maso yammaci, kusan a kullum sai an kai hari musamman a jihohin Zamfara da Katsina da Sokoto da Kaduna.
Jihar Zamfara na ɗaya daga cikin johohin da matsalar tsaro ta fi kamari a faɗin Najeriya, inda barayin daji ke afkawa garuruwa da kauyuka da kashe mutane da satar wasu domin neman kuɗin fansa, ga kuma sacewa ko kwace amfanin gonar da manoma suka shuka.











