Mene ne tasirin rashin amincewa da jakadun Najeriya da wasu ƙasashe suka yi?

Asalin hoton, Getty Images
Masana harkar diflomasiyya sun soma tsokaci kan matakin wasu ƙasashen duniya da suka haɗa da Indiya da Jamus da Mexico, na ƙin amincewa da jakadun da Najeriya ta aika masu.
Rahotanni sun ce India da wasu ƙasashen sun ƙi karɓar jakadun da shugaba Bola Tinubu ya aike masu ne saboda saɓa ƙa'idar tura jakadu zuwa ƙasashen waje.
Ƙasashen sun yi dogaro da wani tsharaɗi da ya ce lallai ne duk jakadun da ƙasa za ta aika, zai kasance gwamnatin tana da sauran wa'adin mulki na aƙalla shekara biyu.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ɗauki lokaci mai tsawo kafin fitar da jerin sunayen waɗanda yake so ya naɗa a matsayin jakadun ƙasar a ƙasashen duniya, lamarin da ya janyo mashi suka daga ƙwararru da kuma sauran jama'ar gari.
Ambasada Sulaiman Dahiru, tsohon jakadan Najeriya ne a kasashe takwas, ya kuma shaida wa BBC cewa aikin diflomasiyya aiki ne da ke tafiya a bisa tsari iri ɗaya a duk faɗin duniya, don haka ba zai dace Najeriya ta riƙa yin abubuwa kamar ba ta bin dokokin duniya ba
Ya ce ''A Najeriya, muna jin kamar za mu iya yin abin da muka dama (kan harkar diflomasiyya) kafin Buhari ya sauka daga mulki ya kamata ya dawo da jakadun da ya naɗa, amma Tinubu ya zo ya dawo da waɗannan jakadu kuma sai ya ƙi naɗa nashi.''
Ya jaddada cewa bai kamata gwamnati ta kammala wa'adin mulki kuma ta sauka ba tare da ta cire jakadun da ta naɗa na, amma idan ma za ta bari, to ƙwararrun da ke cikin su ake bari ba ƴan siyasa ba.
Ambasada Dahiru ya ƙara da cewa daga nan ne aka fara samun tangarɗa a harkar diflomasiyyar Najeriya.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Masanin diflomasiyyar ya ce wani kuskuren da Najeriya ta sake yi a game da batun, shi ne bayyana ƙasashen da ta tura da jakadun tun kafin lokacin fara aikin su.
''Ba a fadin inda jakada zai je aiki sai an samu amincewa tsakanin ƙasashen, amma sai aka zo aka fadi ƙasashen da za su yi aikin, kuma ba tare da ƙasashen sun amince ba'' in ji Ambasada Dahiru.
Dangane da yadda huɗɗar diflomasiyya ke kasancewa tsakanin Najeriya da ƙasashen duniya, ta la'akari da jinkirin naɗin jakadun da kuma yadda wasu ƙasashe suka ƙi karɓar waɗanda aka tura masu, Ambasada Dahiru ya bayyana cewa ''Tinubu ya na zuwa ƙasashen duniya kuma ana sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna, amma ba ka da jakada a waɗannan ƙasashen, su wane ne za su sanya hannu kan yarjejeniyar?''
Masanin ya ce dole ne Najeriya ta zage dantse wajen gyara huɗɗar ta da ƙasashen duniya, musamman naɗin jakadun ƙasashen waje ta hanyar biyayya ga dokoki da kuma sharuɗdan da harkar diflomasiyya ta amince da su.
Rawar da Jakadu ke takawa
Jakada, mukami ne mai muhimmaci a ƙasa domin wakili ne kan duk abin da ya shafi lamurran ƙasar a wata ƙasa, domin yana magana ne da yawun ƙasar da yake wakilta da kuma shugaban ƙasa.
Jakada kan taka muhimmiyar rawa musamman wajen janyo ra'ayin masu zuba jari tare da bayar da shawarwari kan fannonin da za su amfani ƙasa.
Sannan jakada ido ne na ƙasa wanda ke kare manufofi da buƙatunta a ƙasashen ƙetare tare da zama babban jigo ga sauran hulɗoɗin ƙasa da sauran hukumomi na duniya.
Rashin jakada, zai sa ƙasa ta rasa dukkanin waɗannan damarmakin tare da kuma rage ƙimarta da tasirinta a harakokin duniya.
Sai dai ba a san yadda ƙasashen duniya suke kallon Najeriya ba, kasancewar ta shafe fiye da shekaru babu jekadunta a ƙasashen na ƙetare, musamman ƙasar da ke dogaro da masu zuba jari na ƙasashen waje da kuma tallafi.
Tsohon jakadan Najeriya Ambasada Suleiman Dahiru, wanda ya yi aiki a ƙasashe da dama ya ce rashin jakadun, babban giɓi ne ga ƙasar musamman ga hulɗoɗinta a ƙasashen ƙetare.
"Ba zaɓi ba ne kuma bai dace ba a ce Najeriya ba ta da jakadu a ƙasashen waje. jami'an diflomasiyya da ta tura ba su da ƙarfin da za su yi gogayya da gwamnatoci, musamman shugabannin ƙasashe," in ji shi.











