Sanatocin Najeriya 9 da suka koma ADC a cikin makon nan

Asalin hoton, FB/Multiple
Yayin da a baya-bayan nan gwamnonin jam'iyyun adawa ke tururwar komawa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, ita ma sabuwar haɗakar ADC ta yi gagarumin kamu a majalisar dattawan ƙasar.
A farkon watan Yulin 2025 ne jiga-jigan hamayyar ƙasar suka amince da yin ƙawance a jam'iyyar ADC domin ƙalubalantar shugaba Tinubu na APC a zaɓen 2027.
Tun daga wancan lokacin ne ADC ta riƙa zawarcin manyan ƴansiyasa a ƙasar inda ɗaiɗaikun ƴansiyasa suka riƙa komawa cikinta.
Sai dai wannan mako ya kasance lokaci mafi nasara ga jam'iyyar bayan da ƴanmajalisar dattawa tara suka sanar da komawa cikinta, wanda suka kasance masu riƙe da muƙamai mafiya yawa da suka shiga jam'iyyar a lokaci ɗaya.
Matakin na zuwa ne bayan a ƙarshen makon da ya gabata tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar LP, Peter Obi ya sanar da komawa jam'iyyar a hukumance.
Sanatocin - waɗanda suka fito daga jam'iyyu daban-daban sun sanar da matakin ta bakin shugaban majalisar dattawan ƙasar, a lokacin zaman majalisar na makon.
Waɗanne sanatocin ne suka sanar da wannan mataki?
Aminu Waziri Tambuwal

Asalin hoton, FB/Aminu Tambuwal
Tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma sanatan da ke wakiltar mazaɓar Sokoto ta Kudu ya koma ADC ne bayan ficewarsa daga jam'iyyar PDP.
Tambuwal ya kasance gogaggen ɗan siyasa- wanda ya mulki Sokoto na tsawon wa'adi biyu - 2015 zuwa 2023 - ya kasance ɗaya daga cikin ƴan siyasar da suka fito daga arewacin ƙasar masu faɗa a ji.
Tsohon kakakin majalisar wakilan ƙasar ya ce matakin nasa na komawa ADC ya samo asali ne daga ra'ayinsa cewa Najeriya na buƙatar wani ƙarfin siyasa da ya ginu kan gaskiya da haɗin kai da riƙon amana da kuma jajircewa wajen bunƙasa ƙasar.
Lawan Adamu Usman

Asalin hoton, Lawan Adamu Usman/FB
Ɗan majalisar dattawa mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya ya sanar da komawa ADC bayan ficewa daga PDP.
Sanata Lawan Adamu Usman da aka fi sani da Mr Laa ya kasance cikin sanatocin hamayya da aka fi jin muryarsu a majalisar dattawan ƙasar.
A zaɓen 2023 ne aka zaɓe shi a matsayin sanatan Kaduna ta tsakiya bayan doke ɗan takarar APC mai mulkin jihar, Muhammad Sani Abdullahi da aka fi sani da Dattijo.
Ireti Kingibe

Asalin hoton, Ireti Kingibe/FB
Sanatar - wadda ke wakiltar Abuja, babban birnin ƙasar - ta kasance cikin ƴan majalisar mata da aka fi jin amonsu.
A shekarar 2023 ne aka zaɓi Ireti Kingibe matsayin ƴar majalisar dattawan Abuja a ƙarƙashin jam'iyyar LP, bayan doke Sanata Philip Aduda mai ci na jam'iyyar PDP.
Ireti Kingibe ƙanwa ce ga Ajoke Muhammed, matar tsohon shugaban Najeriya, Marigayi, Murtala Muhammed.
Victor Umeh

Asalin hoton, Victor Umeh/Media
Sanata Victor Umeh mai wakiltar Anambra da tsakiya daga jam'iyyar LP na cikin jerin sanatocin da suka sanar da shigar su ADC a makon nan.
Kafin shigar sa LP a kakar zaɓe da ta wuce ya kasance ɗan jam'iyyar APGA, inda har ya taɓa zama shugabanta na ƙasa.
Sanata Victor Umeh ne shugaban kwamitin majalisar dattawan ƙasar da ke kula da ƴan Najeriya mazauna ƙetare.
Tony Nwoye
Ɗan majalisar dattawan mai wakiltar Anambra ta Arewa ya sanar da fitar sa daga jam'iyyar LP zuwa ADC.
Kafin a zaɓe shi a matsayin ɗan majalisar dattawa, ya kasance ɗan majalisar wakilan ƙasar.
Gogaggen ɗansiyasa ne da ya taɓa tsayawa takarar gwamnan jihar Anambra har sau biyu a 2013 da 2017.
Binos Dauda Yaroe

Asalin hoton, Binos Dauda Yaroe
A shekarar 2019 ne ɗan majalisar dattawan mai wakiltar mazaɓar Adamawa ta Kudu ya fara zuwa majalisar dattawan ƙasar a matsayin sanata.
Sannan aka sake zaɓen shi a majalisar ƙarƙashin jam'iyyar PDP, kafin sauya sheƙarsa cikin wannan mako.
A cikin watan da ya gabata ne gwamnan jiharsa ta Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya sanar da komawarsa jam'iyyar APC mai mulki.
Mohammed Ogoshi Onawo

Asalin hoton, Mohammed Ogoshi Onawo
Sanata Ogoshi Onawo mai wakiltar Nasarawa da Kudu a majalisar dattawan ƙasar na daga cikin sanatacin PDP da suka koma jam'iyyar ADC cikin wannan mako.
Gogaggen ɗan siyasa ne da ya taɓa zama kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa, kafin a zaɓe shi majalisar wakilan Najeriyar har sau biyu.
A shekarar 2023 ne ya zama sanata bayan doke tsohon gwamnan jihar Tanko Almakura na APC, wanda ke kan kujerar a lokacin.
Augustine Akobundu
Ɗan majalisar dattawan mai wakiltar Abia daga ta Tsakiya jam'iyyar PDP, ya kasance tsohon hafsan soji, da ya kai muƙamin Kanar a rundunar sojin Najeriya.
Ta kuma taɓa riƙe muƙamin ƙaramin ministar tsaron Najeriya ƙarƙashin gwamnatin tsohon shugaban ƙasar Goodluck Jonathan.
A ranar 15 ga watan Nuwamban 2023 ne aka rantsar da shi matsayin ɗan majalisar dattawan ƙasar, bayan da kotun ɗaukaka ƙara ta soke zaɓen Sanata Darlington Nwokocha.
Enyinnaya Abaribe

Asalin hoton, Enyinnaya Abaribe/FB
Ɗan majalisar dattawan mai wakiltar Abia ta kudu - wanda shi ne ɗaya tilo da jam'iyyar APGA ke da shi a majalisar - ya sanar da komawa ADC cikin wannan mako.
Tun a shekarar 2007 Sanata Abaribe ke majalisr dattawan Najeriya, kodayake kafin nan ya taɓa riƙe muƙamin mataimakin gwamnan jihar Abia.
Sanatan ya kasance shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawan ƙasar ta tara.
ADC ta zama babbar jam'iyyar hamayya a majalisar dattawan
Da wannan sauya sheƙar sanatocin tara, yanzu jam'iyyar ta ADC ta ƙwace matsayin PDP na babbar jam'iyyar hamayya a majalisar dattawan.
Jam'iyyar APC mai mulki ce dai ke da gagarumin rinjaye a majalisar inda take da sanatoci 87 cikin mambobin majalisar 106.
Daga nan sai jam'iyyar ADC, wadda a yanzu ke da mambobi tara a majalisar dattawan.
PDP - wadda bayan zaɓen 2023 take da aƙalla sanatoci 36 - yanzu mambobi shida ne kawai suka rage mata a majalisar.
Yayin da jam'iyyun NDC da NNPP ke da sanata ɗai-ɗai kowanensu.
Ko ADC za ta kama hanyar zama babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya?
Dr Kabiru sa'id Sufi mai sharhi kan al'amuran siyasar Najeriya kuma malami a Kwalejin Share fagen shiga jami'a da ke Kano ya ce ko shakka babu za a iya cewa ADC ta kama hanyar samun wannan matsayi.
''Ai dama akan auna ƙarfin jam'iyya ne da zaɓaɓɓu da masu riƙe da muƙamai da ke cikinta, kuma idan aka tafi a haka, ta fara da Majalisar Dattawa, wataƙila nan gaba kaɗan ta samu wannan matsayi a majalisar wakilai,'' in ji shi.
Masanin siyasar ya kuma ce babu mamaki a samu wani gwamna ya koma cikinta, kasancewar har yanzu jam'iyyar PDP na cikin rikici.
''Hukuncin baya-bayan nan da kotu ta yanke kan rikicn PDP na daga cikin abubuwan da suka ja ra'ayin wasu daga cikin waɗannan sanatoci suka koma ADC, don haka ba mamaki ba ne idan ka samu wani gwamna na PDP ma ya koma ADCn'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Me ya kamata ADC ta yi don ƙarfafa matsayinta?
Masanin siyasar Najeriya ya ce abin da ya kamata ADC ta yi domin riƙe wannan kambi shi ne tabbatar da haɗin kai tsakanin mambobinta.
''Ta lura da abin da ya faru da jam'iyyar PDP domin ta koyi darasi, ta zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya'', in ji shi.
Ya ce yana da kyau mambobin jam'iyyar su kauce wa duk wani abu da zai haifar da shakku ko rikici tsakanin mambobin jam'iyyar.
''Dole ne ta mayar da hankali wajen tara mabiya da kyautata wa mambobinta'', in ji masanin siyasar.











