Atiku, Obi, Amaechi: Wane ne zai yi wa ADC takarar shugaban ƙasa a 2027?

Asalin hoton, Atiku/Amaechi/Obi/X
A ranar Laraba ta jajiberin sabuwar shekarar 2026 ne tsohon gwamnan jihar Anambra wanda kuma ya yi takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar Labour a 2023, Peter Obi ya sanar da komawarsa jam'iyyar haɗaka ta ADC.
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ne ya bayyana haka a wani saƙo da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, inda ya ce komawar Obi jam'iyyar wani babban mataki ne mai muhimmanci a tarihin haɗaka a siyasar Najeriya.
"Ina maraba da komawar Peter Obi cikin jam'iyyar ADC a hukumance, wanda yake cikin ƙoƙarin da muke na samar da haɗaka mai ƙarfi da za ta ƙalubalanci jam'iyya mai mulki. Jam'iyyar da za ta kafa mulkin da zai tabbatar da zaman lafiya da cigaban ƙasa."
Atiku ya ce yana fata komawar Obi cikin jam'iyyar za ta buɗe ƙofar da wasu waɗanda ya bayyana da 'masu kishi' za su biyo domin shiga jirgin haɗakar.
Ƴan Najeriya dai na yin tambayar cewa wane ne a cikin jiga-jigan ƴan siyasar da ke cikin jam'iyyar ta haɗaka zai yi wa jam'iyyar takarar shugaban ƙasa domin ƙalubalantar shugaba Bola Tinubu na jam'iyya mai mulki ta APC a 2027.
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar wanda ya yi takarar neman shugaban ƙasa karo huɗu da Peter Obi wanda ya yi takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar LP a 2023 da tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi tare da wasu gaggan ƴan hamayya su ne fuskokin da aka gani a haɗakar.
Haɗakar ƴan siyasar dai ta tayar da hankalin jam'iyya mai mulki da ma sauran jam'iyyun hamayya, inda masana da ƴan ƙasar ke hasashen rashin jin daɗin jam'iyyun ba zai rasa nasaba da irin ƙalubalantar su da haɗakar za ta yi ba a 2027.
To sai dai furucin da jiga-jigan ƴan hamayyar ke yi dangane da sha'warsu ta tsaya takarar shugaban ƙasa a sabuwar jam'iyyar ta haɗaka na dasa ayar tambaya dangane da ƙarkon da haɗakar ka iya yi.
Ba zan zama mataimakin Atiku ba - Peter Obi

Asalin hoton, Peter Obi/X
A watan Yulin 2025, ɗan takarar shugabancin Najeriya a 2023 a jam'iyyar Labour, Peter Obi ya tabbatar da cewa zai yi takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar ADC, inda ya yi watsi da yiwuwar zama mataimakin Atiku Abubakar.
Obi ya bayyana hakan ne a gidan talbijin na Channels a shirin 'Politics Today'.
"Zan tsaya takarar shugaban ƙasar jamhuriyar Najeriya, kuma na yi imani ina da cancantar yin hakan." In ji Obi.
"..Babu wanda ya taɓa tattauna batun (kasancewa mataimakin Atiku Abubakar). Mutane suna tsammanin abubuwa da yawa. Babu mutumin da ya taɓa magana da ni akan wannan cewa ko zan zama kaza ko kaza".
Dole takarar shugaban ƙasa ta koma Kudu - Amaechi

Asalin hoton, Amaechi/X
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Shi ma tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi kuma wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa inda ya ƙalubalanci Bola Tinubu a zaɓen cikin gida na jam'iyyar APC a 2022, ya sanar da aniyarsa na tsayawa takarar a ADC a 2027.
A 2025, Amaechi ya ce ya yi imanin cewa tsarin karɓa-karɓa tsakanin arewaci da kudancin Najeriya dole ne a mutunta shi.
"Na na yi jagaba wajen yaƙar jam'iyyar PDP? Me ya sa? Saboda akwai yarjejeniya cewa gwamnati a lokacin za ta yi wa'adi guda ɗaya na shekara huɗu. To amma bayan wa'adin na shekara huɗu sai gwmnatin ta karya alƙawari, sai na ce ba zai yiwu ba, rashin adalci ne. Hakan zai lalata al'amura saboda Arewa ita ma za ta rama." In ji Amaechi.
Amaechi ya ƙara da cewa idan aka ba shi damar zama shugaban ƙasa a 2027 to wa'adi ɗaya kawai zai yi. "Ba zan yi fiye da shekaru huɗu ba,...dole ne a ƙyale Kudanci ta kammala wa'adinta. Idan ba a ƙyale Kudanci ta kammala wa'adinta ba to lallai na yi kuskure da na goyi bayan tsarin karɓa-karɓa."
Mece ce matsayar Atiku?

Asalin hoton, Atiku/X
Duk da cewa Atiku Abubakar kawo yanzu bai ce zai tsaya takara ba amma ƴan Najeriya da masu lura da al'amura na ganin takarar ce babban burinsa da ya sa har ya bar jam'iyyarsa ta PDP ya koma haɗakar ta ADC.
Atiku ya yi takarar shugaban ƙasa har karo huɗu, inda biyu daga cikin na cikin gida ne amma ana ganin da wuya a wannan lokaci ya yarda da zama mataimakin ɗaya daga cikin ƴan takarar.
A wata tattaunawa da ya yi da BBC, Atiku ya ce lokacin bayyana aniyarsa ta takara bai yi ba.
Da aka tambaye shi ko zai iya bar wa matashi takarar shugaban ƙasa, sai Atiku ya ce "e zan iya mara wa matashi baya idan har ya kayar da ni a zaɓen fitar da gwani."
Atiku Abubakar ya kasance gaba-gaba wajen sukar lamirin gwamnatin APC musamman dangane da ayyuka da tsare-tsarenta.
"Ai dama yin takarar na ɗaya daga cikin abubuwan da suka sa aka kafa jam'iyyar haɗakar. Babu shakka Atiku Abubakar zai nemi takara ." In ji Malam Kabiru Sufi, masanin kimiyyar siyasa a kwalejin share fagen shiga jami'a.
Makomar ADC

Asalin hoton, Atiku/X
"Ai dama za a yi ta irin waɗannan furuci domin kowa na son gwada damarsa tare da yin kandagarki ta yadda idan burinsa bai cika ba na samun takarar shugaban ƙasa to zai iya samun mataimaki. In ji Malam Kabiru Sufi, masanin kimiyyar siyasa a kwalejin share fagen shiga jami'a.
"To amma ba za a fuskanci alƙiblar wannan sabuwar jam'iyyar ba har sai bayan gudanar da zaɓen cikin gida. Idan an gudanar da sahihin zaɓen da kowa ya gamsu da shi to ƴan takarar ka iya haƙura su yi tafiya tare.
Amma idan kuma ƴan takarar suka fahimci ba a yi adalci ba a gudanar da zaɓen na cikin gida to lokacin jam'iyyar za ta iya fashewa kowa ya rasa." In ji Dakta Mukhtar Bello Maisudan, malami a jami'ar Bayero.
Masanan dai na kallon cewa zaman lafiyar jam'iyyar shi ne gudanar da zaɓen cikin gida na gaskiya wanda kowa zai aminta da shi.
A yanzu haka dai ƴaƴan jam'iyyar ta ADC na zargin gwamnatin Bola Tinubu da fara yin maƙarƙashiya wajen ganin an samu rikici a tsakanin ƴan jam'iyyar.











