Yadda 'ƴan bindiga ke karɓar zinari a matsayin kuɗin fansa' a Zamfara

Asalin hoton, FB/Dauda Lawal
Garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa ba sabon abu ba ne a arewa maso yammacin Najeriya, sai dai a lokuta daban-daban ƴan fashin kan sauya salon ayyukan nasu domin yin ɓadda-bami ko sajewa da yanayi.
Sau da yawa sukan daɗe suna amfani da wani salo kafin bayani ya fito fili saboda yadda suke gudanar da ayyukan nasu a cikin ƙauyuka, da kuma barazanar da sukan yi wa al'umma.
A bisa yadda aka saba a arewa maso yamma, masu garkuwar kan karɓi kuɗaɗe, babura da kuma kayan abinci daga dangin waɗanda suke garkuwa da su kafin su sako su.
Sai dai wani sabon bayani da ya ɓulla a yanzu shi ne yadda suka koma karɓar zinari a matsayin kuɗin fansa ko kuma a matsayin harajin da sukan ƙaƙaba wa mazauna ƙauyuka.
Wata kungiya mai zaman kanta mai suna Zamfara Circle Community Initiative ta yi zargin cewa a yanzu ƴan bindgar suna sanya wa ƙauyuka harajin zinari.
Shugaban ƙungiyar, Aminu Lawal ya ce: "Muna da kwamitin da ke tattaro mana bayanai kan abubuwan da suke faruwa idan aka kai hari, ko aka buƙaci kuɗin fansa, ko kuma aka dora wa ƙauyuka haraji.
"Ɗaya daga cikin wannan kwamitin ne ya kawo mana rahoton cewa a ƙauyuka huɗu da ke ƙaramar hukumar Zurmi - watao Gidan Shaho da Marmaro da Rimni da kuma Dada - an saka musu cewa za su biya haraji da gwal ba da kudi ba."
A cikin bayanin da ya yi, Lawal ya ce a cikin wannan mako ne aka sanar da ƙauyukan game da biyan harajin.
Me ya sa suka zaɓi zinari?

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar Zamfara Circle Community Iniative ta ce tana ganin akwai abubuwa uku da suka sanya ƴan fashin dajin suka koma karɓar zinari a matsayin kudin fansa da na haraji:
- Darajar gwal ba ta faɗuwa kamar ta tsabar kuɗi
- Sauƙin safara
- Sauƙin cinikayyar makamai tsakanin ƙasa da ƙasa
Jiha mai arziƙin zinari

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Zamfara jiha ce da aka yi ittifakin na da ɗimbin albarkatun Zinari da ma sauran albarkatun ƙasa.
Yawanci masu aikin haƙar albarkatun na yi ne ba bisa ƙa'ida ba kuma ba a kan tsari ba.
A shekara ta 2020, gwamnan jihar Zamfara na lokacin, Bello Matawalle, ya taɓa cewa gwamnatin jihar tana shirin samar da wata taskar adana zinari.
"Na sanar da shawarar da gwamnatina ta yanke na samar da wata taskar zinari ta jihar Zamfara. Wannan na daga cikin ƙaƙarinmu na haɓɓaka tattalin arziƙin jihar da ƙarfafa tattalin arziƙi da walwalar al'umma a yanzu da kuma nan gaba," kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X.
Haka nan wata sanarwa da gwamnatin ta fitar ta ce: "Akwai wasu da suka nuna aniyar haɗa hannu da jihar, har ma suka yi tayin bayar da naira biliyan biyar ta yadda gwamnatin Zamfara za ta riƙa samar musu da curin zinari na tsawon wani lokaci."
Sai dai a watan Afrilun 2019 ne gwamnatin Najeriya ta haramta duk wani aiki na haƙar zinari da sauran albarkatun ƙasa na tsawon shekara biyar a jihar sanadiyyar matsalar tsaro.
Inda gwamnatin ta ɗage haramcin a cikin watan Disamba na shekara ta 2024.
Matsalar tsaron jihar Zamfara

Asalin hoton, Getty Images
Sama da shekara 10 ke nan jihar Zamfara - wadda ta yi fice a harkokin noma - ke fama da matsalar tsaro ta ƴan fashin daji, lamarin da ya haifar da ɗimbin asarar rayuka da dukiya da kuma durƙusar da ayyukan tattalin arziƙi
A ranar 7 ga watan Yulin 2014 kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato rundunar ƴansandan Najeriya na cewa faɗa tsakanin makiyaya masu satar shanu waɗanda ke haye kan babura da ƴan sa-kai ya haifar da asarar rayukan aƙalla mutum 72 a ƙauyen Ƴar Galadima da ke jihar Zamfara.
Dag baya matsalar ta ci gaba da gawurta, inda ta fantsama zuwa jihohin arewacin Najeriya da ke maƙwaftaka, kamar Katsina da Kaduna da Sokoto da Kebbi da kuma Neja.
A cikin watan Yulin 2016 tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da wani aikin sojin ƙasar da aka yi wa laƙabi da 'Operation Harbin Kunama a yankin Dansadau na jihar ta Zamfara domin yaƙi da matsalar.
Sai dai har yanzu matsalar ta ki ci ta ƙi cinyewa.
Ko a wannan mako an samo rahotannin yadda ƴan bindigar suka yi wa mutane 38 "yankan rago" a ƙaramar hukumar Kauran Namoda da ke jihar ta Zamfara.
Sai dai a lokacin wani taro a birnin Kaduna a cikin makon, mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan lamurran tsaro, Nuhu Ribadu ya yi ikirarin cewa gwamnati ta yi nasara a yaƙin da take yi da matsalar tsaro a ƙasar.
"A baya, ƴanta'adda sukan yi kai hare-hare a gidajen yari da jirgin ƙasa da sansanonin soji, amma tun da gwamnatin nan ta hau mun yi maganin hakan," in ji Ribadu a tattaunawarsa da BBC sa'ilin taron.
Sai dai shugaban ƙungiyar Zamfara Circle community initiative, Aminu Lawal ya shaida wa BBC cewa girmar matsalar tsaro a jihar ya yi muni.
"Ina sanar da ku cewa dukka fadin jihar Zamfara na cikin matsalar tsaro," in ji Lawal.
Ya ambato cewa wasu manyan hanyoyin da ke cikin jihar, kamar Gusau zuwa Ƙaura, da Gusau zuwa Maru da kuma Gusau zuwa Tsafe sun kasance masu hatsari duk kuwa da sasaucin da aka samu a baya.










