Rikicin Zamfara: Buhari ya hana hakar gwal

Mining site

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jihar Zamfara na da arzikin gwal da sauran ma'adanai

Gwamnatin Najeriya ta dakatar da dukkanin aikace-aikacen hakar ma'adanai a jihar Zamfara.

Garba Shehu mai magana da yawun fadar gwamnatin Najeriya ne ya tabbatar wa da BBC a yau Lahadi.

Ya ce dakatarwar ta wani lokaci ce kafin gwamnati ta gama nazari.

Babu dai tabbacin dalilin da yasa gwamnatin daukar wannan mataki, amma ana ganin ba zai rasa nasaba da hara-haren 'yan bindiga ba da ya addabi jihar.

Shi ma mai bai wa shugaban kasa shawara kan kafafen sada zumunta Bashir Ahmad ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter.

Ya ce: "Gwamnati ta dakatar da aikin hakar ma'adai a jihar Zamfara da zai fara aiki nan take. Kuma ta umarci 'yan kasashen waje da su bar yankin cikin gaggawa, inda rundunar dawo da zaman lafiya ta 'Puff-Adder' za ta mamaye wajen."

Wannan haramcin dai yana zuwa ne kwana daya bayan da dubban 'yan Najeriya suka yi zanga-zangar matsa wa gwamnati da ta dauki mataki wajen kawo karshen hara-haren 'yan bindiga a jihar ta Zamfara.

Al'umma a jihar sun dade suna fuskantar hara-haren tare da kone garuruwansu daga 'yan fashi masu dauke da manyan bindigogi.

Makonni biyu da suka gabata an kashe mutane sama da 40.

Amma 'yan sanda sun musanta da cewa labarin kanzon-kurege ne.