Adadin mutanen da aka kashe a Najeriya a rabin shekarar 2025 ya zarce na 2024

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kula da haƙƙin ɗan'adam ta Najeriya ta ce adadin mutanen da aka kashe a watanni shidan farkon wannan shekara ya kai 2,266.
Hukumar ta ce adadin ya zarta na mutanen da aka kashe a irin wannan lokaci cikin shekarar 2024, inda aka kashe mutum 2,194.
Sojojin Najeriya na fafutikar ganin sun tunkari matsalolin tsaro daban-daban da ake fama da su a ƙasar, daga Boko Haram a arewa maso gabashin ƙasar, zuwa hare-haren ƴan fashin daji a arewa maso yammacin ƙasar da rikicin ƙabilu da na manoma da makiyaya a arewa maso tsakiya da kuma rikicin ƴan aware a gabashin ƙasar.
Lamari ya yi ƙamari a baya-bayan nan inda aka kashe mutum 606 a watan da ya gabata kacal, ciki har da hare-haren da aka kai a ƙauyukan Yelwata da Dauda a jihar Benue, inda aka kashe kimanin mutum 200.
Shugaban Hukumar kare hakkin bila'adama ta Najeriya, Tony Ojukwu ya yi kira da a ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki kan lamarin.
"Waɗannan ba alaƙaluma ne kawai ba, iyayen wasu ne, ƴaƴan wasu ne, wasunsu su ne ƙarfin iyalansu, an raba wasu da masoyansu, an raba wasu da hanyar samun abinci, an kashe makomar wasu ta hanyar rashin imanin da bai dace ba," in ji Ojukwu.
Hukumar ta sanar da cewa mutum 857 ne aka yi garkuwa da su a watanni shida na farkon 2025, alƙaluman da suka nuna cewa an samu raguwar mutanen da aka yi garkuwa da su idan aka kwatanta da watanni shida na farkon shekarar 2025, inda aka sace mutum 1,461.
Rahoton ya kuma fito da matsalar kai wa jami'an tsaro farmaki , inda aka kashe sama da sojoji 17 a jihohin Kaduna da Neja, da kuma jami'an tsaro na Askarawan Zamfara 40 a arewa maso yammacin ƙasar.
Ƙalubalen da sojojin Najeriya ke fuskanta
Masanin tsaro a Najeriya Dakta Kabiru Adamu ya ce rundunar sojin ƙasar na da tarin ƙalubalen da ke gabanta, wadanda ke yi mata tarnaƙi wajen gudanar da ayyukanta.
Ya kuma ce dole ne rundunar sojin ta magance matsalolin domin samun nasara a ayyukan da ke gabanta.
Wasu daga cikin matsalolin da ke yi wa rundunar sojin tarnaki kamar yadda Dakta Kabiru Adamu ya zayyano sun haɗa da:
- Rashin isassun jami'ai: Ɗaya daga cikin manyan matsalolin da rundunar sojin Najeriya ke fuskanta, ita ce rashin isassun jami'i, a cewar Dakta Kabiru Adamu. ''Yanzu idan ka duba girman Najeriya da irin tarin matsalolin tsaron da ke gaban sojojinta, sai kuma a ce maka duka adadin sojojin Najeriya bai wuce 230,000 ba, to ka ga ai akwai matsala'', in ji shi.
- Rashin wadatattun kayan aiki: Ita ma wannan matsala ce da ke ci wa rundunar sojin Najeriya tuwo a ƙwarya, kamar yadda masanin ya yi ƙarin haske. ''Yaƙi da ƴan'tadda masu iƙirarin jihadi, wadanda galibi ke sajewa cikin mutane, na buƙatar sabbi kayan aiki na zamani na musamman'', in ji shi.
- Rashin inganta walwalar sojoji: Dakta Kabiru Adamu ya ce wani abu da ke zama tarnaki ga ayyukan sojojin Najeriya shi e rashin kula da haƙƙoƙi da walwalarsu. ''Irin albashin da ake biyansu da muhallin da ake ba su da kuma horo, duka na buƙatar a sake nazarinsu'', in ji shi.
- Rashin samun goyon bayan jama'a: Wannan ma na cikin tarin matsalolin da ke gaban rundunar sojin na Najeriya, a cewar Dakta Kabiru Adamu. ''Yadda a wasu lokutan sojojin ke gudanar da ayyukansu, musamman a wurare na bincike, da yadda suke rufe kasuwanni da dai sauran nau'ikan takura wa jama'a ya sa mutane sun fara daina ba su haɗin kai'', in ji shi
- Jinkiri wajen sauya wa jami'a wurin aiki: A ƙa'idar aikin soji akwai adadin lokaci da ba a so soja ya zarta a wurin da aka kai shi domin yaƙi, amma sojojin Najeriya kan kwashe shekaru a wasu wuraren ba tare da sauya musu wurin aiki ba, kamar yadda Dakta Kabiru Adamu ya bayyana.
- Zargin cin hanci da rashawa: Dakta Kabiru Adamu ya ce akwai zarge-zarge masu yawa da ake yi wa rundunar sojin na karkatar da kuɗaɗen da ake ware wa rundunar domin gudanar da ayyukanta. "Akwai cibiyar CISLAC da ƙungiyar Transperency International, wadanda suka yi bincike mai zurfi tare da bayar da shaida kan wasu manyan sojoji da aka kama game da irin wannan laifi na satar kuɗin rundunar, musamman wajen sayen kayyakin sojin'', in ji mai nazarin harkokin tsaron.











