Me ya sa Bello Turji ke neman sulhu da gwamnati?

Bello Turji

Asalin hoton, FB/Sheik Ahmad Gumi

Bayanan hoto, Bello Turji
Lokacin karatu: Minti 4

A ƙarshen mako ne aka ga wani bidiyon ɗan bindigar nan da ya addabi wasu yankuna na arewacin Najeriya - Bello Turji - na yawo a shafukan sada zumunta, inda a ciki yake kira da yin sulhu tsakanin shi da gwamnati.

Ba kamar yadda ya saba bayyana a akasarin bidiyoyin da ya saki a baya ba, inda yake barazana da tutiya, a wannan karon ya bayyana ne jikinsa a sanyaye.

Turji ya bayyana ne a cikin bidiyon sanye da kayan sojoji, inda yake tsaye, sanye da kayan sojoji tare da wasu mutum biyu - ɗaya a hagunsa ɗaya kuma a hannun damarsa - yana bayani kayamar yadda ya saba yi a kai a kai.

Wannan na zuwa ne bayan ƙaimin da sojojin Najeriya suka ce sun ƙara sanadiyyar matalar tsaro, inda a baya-bayan nan suka sanar da kashe ɗaya daga cikin na hannun damar Turji, wato Kachalla Yellow Danbokolo.

Turji na ɗaya daga cikin manyan ƴan fashin daji da hukumomin Najeriya ke nema ruwa a jallo, waɗanda suka daɗe suna far wa ƙauyuka a arewa maso yammacin Najeriya, lamarin da ya yi sanadin rasa ɗimbin rayuka da kuma gurgunta aikin noma da al'umma suka dogara da shi.

Me Turji ya ce a bidiyo?

A cikin bidiyon da ya fitar, wanda ɗan jarida mai nazari kan tsaro, Mannir Fura Girke ya tabbatar cewa an ɗauke shi ne a ranar 5 ga wannan wata na Juli, an ji Turji, cikin murya maras karsashi na cewa: "muna wa Allah godiya cikin wani yanayi da muka tsinci kanmu, cikin wani yanayi dai ga shi nan."

Mutanen da ba su tsoron Allah sun so su cutar da mu amma mun yi nasara a kansu, saboda haka muna cikin ƙoshin lafiya.

Haka nan ɗan bindigar ya yi magana kan kisan da jami'an tsaro suka yi wa na hannun damansa Kachallah Danbokolo.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Daga nan sai Turji ya ce "muna kira ga gwamnatinmu mai albarka ta bari mu zo mu zauna lafiya, dukkan mu ƴan ƙasa ne, ta yi wa kowa adalci...yanda kowa zai miƙa kayan shi ga gwamnati a zo a zauna lafiya domin a gudu tare a tsira tare."

"Muna kira ga gwamnatinmu mai albarka, daga gwamnatin tarayya har zuwa ga gwamnatin jihar Zamfara, wannan kashe-kashen ya kamata ta duba, ya isa.

"Saboda haka muke mata(gwamnati) kyakkyawan zaton za ta bai wa al'ummar da aka zalunta hakkokinsu domin a samu zaman lafiya, a yi kiwo, a yi noma, a yi kasuwanci, kowa ya shiga inda yake buƙata, Allah sa wannan gwamnan zai gane kiran da muke yi mashi," in ji Turji a cikin bidiyon mai tsawon kusan minti biyar.

Sai dai tun ba yau ba, gwamnan jihar Zamfara ta sha nanata cewa Dauda Lawal ya sha nanata cewa ba zai taɓa yin sulhu da ƴan fashin daji ba.

Batun yin sulhu da ƴan fashin daji na daga cikin muhawara mafi zafi da ake tafkawa a jihohin da ke fama da matsalar tsaro a Najeriya, musamman a arewa maso yammacin ƙasar.

Me ya sa Turji ke neman sulhu?

Masana harkokin tsaro na ganin cewa dole ce ta sanya riƙaƙƙen ɗan fashin dajin Bello Turji ya fara neman sulhu da gwamnati.

Masani kan tsaro a arewacin Najeriya, Mannir Fura Girke ya ce "abin da ya sa ya fito yana waɗannan maganganun jikinsa ne ya yi la'asar saboda galibin makusantarsa an kashe su".

"Kuma ya tabbata 'operation ɗin da ake yi a yanzu da gaske ake yi".

Fura Girke ya ce a yanzu Bello Turji ba ya iya kai hare-hare a wuraren da ya saba kamar a baya.

"Sannan kusan manya-manyan kwamandojinsa da suke taimaka masa wajen ta'addanci yanzu an kashe su, ka ga idan idan tura ta kai bango kansa za a faɗa ke nan, don haka dole ya nemi yadda zai zauna da gwamnati domin a yi sulhu da shi," in ji Fura Girke.

Masanin tsaron ya ce kisan da aka yi wa Kachalla Dan Bokolo ba ƙaramin illa ba ce ga Bello Turji kasancewar "shi Dan Bokolon ya fi shi hatsabibanci".

Ko ya kamata a yi sulhu da Turji?

Masanin tsaro Mannir Fura Girke na ganin cewa bai kamata gwamnatoci su gaskata Bello Turji ba kasancewar "an sha yin sulhu da shi yana karya alƙawari."

"A shekara ta 2021 an yi sulhu da shi, wadda Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya jagoranta amma abin bai yi ba, sannan gwamnatin da ta gabata ta tsohon gwamna Bello Matawalle ta zauna da shi lokuta daban-daban amma dun ya tayar da yarjejeniyar," in ji Fura Girke.

Masanin ya ce "don haka ina ganin bai da wani amfani a yi sulhu da shi."

Wane ne Bello Turji?

An haifi Muhammadu Bello wanda aka fi sani da Kacalla Turji a yankin Ƙaramar Hukumar Shinkafi da ke cikin Jihar Zamfara kuma take kan iyaka da Ƙaramar Hukumar Isa a Sokoto.

Yankin na Shinkafi da kuma garuruwan Isa da Sabon Birni na Jihar Sokoto na maƙotaka da juna.

"A Shinkafi ya taso kuma a nan ne mahaifnsa ke zuwa da shi cin kasuwar dabbobi da sauransu kamar kowane Bafulatani," in ji Dr. Murtala.

Binciken da masanin ya yi ya nuna cewa shekarun Turji sun kama daga 27 zuwa 35.

"Shi ma mahaifinsa Usman wanda aka fi sani da Mani na Marake ɗan asalin yankin ne, mai arzikin dabbobi, kuma mutum ne bawan Allah da ke da tarihi na zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya."

Mahaifyarsa kuma, an fi saninta da 'yar Kagara - ta yankin Isa - wadda ke da alaƙa da babban yaron Turji mai suna Ɗanbokolo.