Yadda rikici tsakanin Bello Turji da abokan gabarsa ya jawo mutuwar 'yan bindiga da dama a Jihar Zamfara

'Yan fashin daji

Asalin hoton, Daily Trust

Bayanan hoto, Rikici tsakanin gungun 'yan fashin daji ya yi sanadiyyar mutuwar 'yan bindiga kusan 30

Rikicin da ya ɓarke tsakanin gungun ƙasurgumin ɗan fashin daji Bello Turji da wasu 'yan fashi abokan gabarsa a Jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya ya jawo kisan jagororin 'yan bindigar da kuma gwamman mabiyansu.

Bayanai sun ce 'yan bindigar da ke kashewa tare da garkuwa da mutane sun fara fafatawa a tsakaninsu tun daga ranar Litinin zuwa Talata lokacin da Bello Turji ya jagoranci wani samame kan tawagar fitaccen ɗan fashi mai suna Dullu.

Bayanan da BBC ta samu sun nuna cewa harin ya yi sanadiyyar kashe Dullu tare da gwamman mayaƙansa kusan 30.

Mazauna yankin sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ƙauyen Maniya da ke Jihar Zamfara, wanda ya yi sanadiyyar kashe gwamman 'yan bindiga daga ɓangarorin biyu.

Bayan Dullu da aka kashe, an kashe wani babban ɗan fashi mai suna Ɗan Maigari.

Abin da ya haifar da rikicin

Bayanai sun bayyana cewa harin da Turji ya kai na ramuwar gayya ne sakamakon kashe wasu 'yan uwansa da gungun Dullu suka yi a kwanakin baya.

"Akwai wasu 'yan uwan shi Turji da aka saka a mota za a kai su Kano daga Ƙaramar Hukumar Shinkafi don a yi musu magani saboda ba su da lafiya, sai tawagar Dullu ta tare su kuma ta buɗe musu wuta," a cewar wani mazaunin yankin da ya nemi a ɓoye sunansa.

Ya ƙara da cewa da ma ana ganin Dullu bai daina kashe-kashen mutane ba, inda shi kuma Turji ake cewa ya tuba.

Yadda aka fafata

Sai dai kuma a wannan arangamar duka ɓangarorin sun ji a jikinsu.

Bayanai sun ce bayan shafe lokaci ana ɓarin wuta tsakaninsu, Bello Turji ya yi nasarar kama Dullu da hannunsa kuma ya kashe shi.

"Mun samu labarin cewa mutum 16 aka ji wa munanan rauni a ɓangaren Turji, waɗanda ba za a iya ɗaukarsu ba a wannan lokaci," in ji majiyar tamu.

"Sun [ɓangaren Turji] faɗa mana cewa sun kashe mutum 29 ko sama da haka, suna cewa mutanen na da yawa shi ya sa ba su tsaya sun ƙirga su ba. Amma dai mutanen za su kai 30 ko ma sama da haka."

Haka nan an ce Turji ya kama wasu daga cikin mutanen a yankin Maniya, inda ya kashe su daga baya.

Gawurtattun 'yan fashin daji da suka nemi sulhu da jama'ar Zamfara

Bello Turji da Auwalu Daudawa

Asalin hoton, DAILY TRUST/OTHER

Bayan shafe tsawon lokaci suna kashe-kashen da sace-sacen mutane da dukiyoyinsu, gungu-gungu na 'yan fashin da suka addabi yankunan arewa maso yammacin Najeriya na neman sulhu da jama'ar yankunan.

Tun a watan Nuwambar 2021 rahotanni ke cewa ƙasurgumin ɗan fashin daji Bello Turji na neman sulhu tsakaninsa da jama'ar yankin Shinkafi da Isa da Sabon Birni, kuma a watan Disamba wata wasiƙa ta ɓulla inda a ciki yake jaddada aniyarsa ta neman sulhun.

Wasu bayanai na cewa shugabannin 'yan fashin fiye da 40 ne ke neman sulhu da jama'ar yankunan da suka addaba.

Sai dai akwai maganganu daban-daban game da dalilan da suka sa suke neman zaman lafiyar a yanzu.

Ga wasu 'yan fashin daji biyar mafiya gawurta da suka nemi sulhu da mutanen garuruwansu.