Ribadu ya yi gargaɗi ga ƴanbindiga su miƙa wuya

Asalin hoton, Twitter
Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta APC a Najeriya ta yi gargaɗi ga ƴanbindiga da suka addabi al'ummomin arewacin kasar su gaggauta miƙa wuya tare da dakatar da kashe mutanen da basu ji ba ba su gani ba.
Babban mai ba shugaban ƙasar shawara kan sha'anin tsaro Malam Nuhu Ribadu ne ya yi wannan gargaɗin a hirarsa da BBC inda ya bayyana irin nasarorin da gwamnatinsu ta samu a fannin tsaro.
"Muna ganin waɗanda suke ta'addancin nan, lokaci ya yi su tsaya su daina su bari," in ji Ribadu.
Malam Ribadu ya yi wannan gargaɗin ne duk da ya yi ikirarin cewa gwamnatinsu ta yi nasarar kawar da barazanar tsaro musamman hare-haren ta'addanci a Najeriya.
Gargaɗin na zuwa yayin da wasu sassan ƙasar musamman yankin arewacin ƙasar ke fama da hare-haren ƴanbindiga masu satar mutane domin kuɗin fansa da kuma barazanar Boko Haram.
A hirarsa da BBC, Malam Ribadu ya ce yanzu lokaci ne da gwamnatinsu ke ganin ya kamata ta fito ta bayyana irin nasarorin da ta samu a fannin tsaro.
"A baya, ƴanta'adda sukan yi kai hare-hare a gidajen yari da jirgin ƙasa da sansanonin soji, amma tun da gwamnatin nan ta hau mun yi maganin hakan."
"Yanzu ba wuri ɗaya da za a ce an kai harin ta'addanci tun da wannan gwamnati ta hau baya ga wanda ake yi a Borno," in ji Malam Ribadu.
Ya ƙara da cewa, sun yi nasarar kashe shugabannin ƴanbindiga da dama. Amma a cewarsa, "shugabanni da aka kashe da ake kira kacalla sun kai 300"
"Yanzu mutane da dama na zuwa gonakinsu kuma wurare da dama da a can baya ba a isa a shiga ba yanzu ana zuwa," a cewar mai ba shugaban Najeriya shawara kan sha'anin tsaro.
Sai dai duk da wannan ikirarin na gwamnatin Najeriyar, har yanzu wasu sassan ƙasar musamman yankin arewa maso yammacin ƙasar na fama da hare-haren ƴanbindiga da suke satar mutane domin kuɗin fansa.
Ko a ƙarshen makon nan ƴanbindiga sun yi wa wasu al'ummar yankin Kauran Namoda a jihar Zamfara yankan Rago.
Kuma har yanzu ana zaman ɗarɗar a wasu yankuna na jihohin Benue da Filato sakamakon rikici mai nasaba da ƙabilanci.
Sannan har yanzu ƙungiyar Boko Haram na ci gaba da haifar da barazana a yankin arewa maso gabashin Najeriya.











