Su wane ne a cikin bidiyon mutanen da ake garkuwa da su 'a Zamfara'?

Asalin hoton, Other
Wani bidiyo mai tayar da hankali ya ɓulla a shafukan sada zumunta na Najeriya, inda ya nuna wasu tarin mutane da ake zargin an yi garkuwa da su ne, suna neman taimako.
Mutanen, waɗanda ake zargin cewa an sace su ne a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin ƙasar, an nuna su ne suna zaune a wani wuri da ba a iya tantancewa ba, wasu daga cikinsu suna ɗaure da sarƙa.
Haka nan an rufe wa wasu daga cikin su fuskoki, inda aka ware mata da yara daban da maza.
Kayan da suke sanye da su sun nuna alamar jin jiki, yayin da mazan kuma suka yi gashi a fuska.
Waɗanda suka yi magana a bidiyon sun yi roƙo mai sosa zuciya, inda suka yi kira ga gwamnatin jihar ta fara tattaunawa da waɗanda ke garkuwa da su, domin su sake su.
Sun yi ikirarin cewa ana tsare da kimanin mutum 200 ne, a inda suka bayyana da "dabar ƴan fashin daji".
Wannan bidiyo ya tayar da hankalin al'umma da dama da suka gan shi a ƙasar ta Najeriya, inda garkuwa da mutane domin neman kudin fansa ta yawaita.
Mutane da dama na tambayar ta yaya ƴan fashin suka samu damar kora mutane masu yawa haka ba tare da jami'an tsaro sun gan su ba?
Kuma hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan wasu ƴan fashin daji sun kashe aƙalla mutum 35 a ƙauyen Banga da ke ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda a jihar ta Zamfara.
Gwamnatin jihar Zamfara ta ce ta lashi takobin hukunta wadanda suka aikata hakan, to sai dai har yanzu ba a ji labarin kama wani ba a kann hakan.
Daga ina bidiyon ya fito?
A bayanin da ya yi wa BBC, ɗan jarida mai zaman kansa kuma mai lura da matsalar tsaro a Najeriya da ƙasashe maƙwafta, Mannir Fura-Girke ya ce bidiyon ya fito ne daga wani ɗan bindiga da ake kira Kachalla Dan Sadi.
Kuma ya tabbatar da cewa mutanen da ke cikin bidiyon an kama su ne a ƙauyuka da dama na ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda da ke jihar Zamfara, kamar Cambarawa da kuma Sabon Garin Ƙaura.
Ya ce Kachalla ya fitar da bidiyon ne "da gangan domin a tsorata jama'ar yankin su amince da shirin sulhu da shi. Hanyar barazana ce, kuma hakan ya saɓa da dokokin ƙasa."
Ya ƙara da cewa ɗan fashin dajin ya kama mutanen ne a lokaci daban-daban cikin makonni biyu da suka gabata, "Wasu ya kama su ne sati biyu da suka wuce, wasu kuma kwana goma."
Martanin gwamnatin Zamfara

Asalin hoton, X/Dauda Lawal
Ahmed Manga, mai bai wa gwamnan jihar Zamfara shawara kan tsaro ya ce gwamnatin jihar na sane da bidiyon kuma yanzu haka ta sha alwashin ceto mutanen.
"Ya yi wannan bidiyo ne da ya yi da harshe biyu, kasancewa an biyo masa ta hanyar sulhu cewa a zo a yi sasanci ya rabu da mutane, ba ya yi ba ne don Allah."
Sai dai Manga ya ba wai gwamnatin jihar Zamfara ba ta buɗe kafar tattaunawa ne da ƴan bindiga ba, kamar yadda ta sha bayyanawa.
Gwamnan jihar Dauda Lawal Dare ya sha nanata cewa gwamnatinsa ba za ta yi sasanci da ƴan fashin daji ba duk kuwa da cewa akwai wasu jihohi masu maƙwaftaka da suka rungumi hakan.
Wasu na kallon matakin gwamnatin na ƙin yin sulhu matsayin darasin da ta koya daga matakin da ta ɗauka a baya na yin sulhu, lamarin da ya wargaje ba tare da nasara ba.
Me bidiyon ke nufi?
Daga bayanan da aka gani a bidiyon, Fura-Girke ya bayyana cewa mutanen da ke hannun Kachallan na cikin tsananin damuwa.
"Za ka fahimci suna cikin ƙunci, babu abinci, kuma akwai alamar tsangwama. Ba za a ce suna cikin ƙoshin lafiya ba," in ji shi.
Bidiyon ya kuma nuna waɗanda aka kama suna roƙon gwamnati da masu ruwa da tsaki su fanshe su. Sai dai, Fura-Girke ya bayyana hakan a matsayin wani salo na tilastawa.
"Shi ya tursasa musu su yi kira ga gwamnati da ta amince da sulhu. Ba don suna so ba, sai dai don tsoro da wahala da suke ciki," in ji shi.
Mai sharhin ya ce akwai dalilin da yasa Kachalla ke son sulhu.
"Yana jin tsoron kar a yi masa irin yadda aka yi wa sauran Kachalloli – an hallaka su. Don haka yana son ya gabatar da kansa a matsayin wanda za a iya sulhu da shi," in ji Fura-Girke.
"Amma ni a ganina, bai kamata gwamnati ta amince da sulhu da shi ba."
Wane ne Kachalla Dan Sadi?
A cewarsa Fura-Girke, Kachalla Dan Sadi ɗan asalin ƙauyen Gidan Ruga ne a ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda.
Ya yi makarantar firamare, ya fara sakandare amma bai kammala ba. "Mahaifiyarsa ƴar'uwar Buharin Daji ce – fitaccen shugaban ƴan bindiga wanda shi ne tushen fashin daji a arewacin Najeriya," in ji Fura-Girke.
Bayan ya daina makaranta, ya koma wajen Buharin Daji. "Ya taso a hannunsa, kuma saboda yana da ilimi na boko, ya riƙa yi masa ayyukan da suka shafi karatu da rubuce-rubuce lamarin da yasa ake masa kallon ɗaya daga cikin manyan yaransa."
Daga bisani, bayan kashe Buharin Daji da shekaru da yawa, Kachalla Ɗan Sadi ya kafa tasa dabar, inda ya tara matasa domin ci gaba da ayyukan ta'addanci, kamar yadda Fura-Girke ya tabbatar wa BBC.











