Abubuwa 10 game da Moroko wadda za ta karɓi baƙuncin gasar Kofin Afirka

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Ousmane Badiane
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Digital Journalist BBC Afrique
- Lokacin karatu: Minti 8
Morocco - wadda take can ƙurya a yankin arewa maso yamma a nahiyar Afirka - tana tsakanin tekun Atalantika da na Bahar Rum, inda take da al'umma miliyan 36.9.
Rabat, birnin na bakwai mafi girma a ƙasar shi ne babban birnin ƙasar, yayin da Casablanca ke zaman babbar cibiya tattalin arziƙi da harkokin kuɗi na ƙasar.
Ƙasar tana da gaɓar teku mai tsawon kilomita 3,500, sannan ta ratsa tsaunukan Atlas, ga ta kuma a kusa da Hamadar Sahara.
Ƙasar tana da wurare na shaƙatawa a bakin tekun Bahar Rum da kuma na Atalantika da tsaunuka na hamada da wurare masu dausayi da shukoki da kuma jigayi.
Gasar Cin Kofin Afirka ta 2025, wadda ƙasar za ta karɓi baƙunci a karo na biyu, harka ce ta wasa da ƙasar ke ɗauka da muhimmancin gaske.
Kamar dai ga sauran ƙasashen Afirka wasan ƙwallon ƙafa shi ne ya fi farin jini a Moroko.
Ƙwallon ƙafa wasa ne da ke zaman wata alama ta haɗa kan ƙasar da kuma tasirin ƙasar a nahiyar Afirka - inda bajintar da tawagar ƙasar - Atlas Lions, ta yi a gasar Kofin Duniya ta 2022, ta ƙara jaddada ta.
A wannan maƙala BBC ta zaƙulo wasu abubuwa guda goma da za su sa ku ƙara sani da fahimtar Moroko, wadda za ta karɓi baƙuncin gasar ta cin Kofin Afirka na ƙwallon ƙafa karo na 35.
Musulunci ne addinin ƙasar

Asalin hoton, Getty Images
Musulunci shi ne addinin da ke matsayin na gwamnati a Moroko, inda sama da kashi 99 cikin ɗari na al'ummar ƙasar Musulmi ne, 'yan Sunni da ke bin mazhabin Malikiyya.
Amma duk da haka doka ta 6 ta kundin tsarin mulkin ƙasar ya tabbatar da 'yanci da bayar da dama mutum ya yi wani addinin da yake so.
Daga cikin mabiya addinan da ba su da rinjaye akwai Kiristoci da suke kashi 1 cikin ɗari na yawan al'ummar ƙasar.
Akwai kuma al'ummar Yahudawa da suke da yawan ɗigo biyu (0.2) cikin ɗari ko kuma a ce mutum 20,000 a cikin al'ummar ƙasar.
Masarautu mafiya daɗewa a duniya

Asalin hoton, Getty Images
Moroko na amfani da tsarin mulki na mulukiyya mai amfani da majalisar dokoki, ƙarƙashin shugabancin sarki, na masarautar Alawi, da ke shugabantar ƙasar tun tsakiyar ƙarni na 17.
Masu sarautar suna da asali na addini, kasancewar an yi imanin cewa suna da alaƙa da iyalan gidan Annabi Muhammad (S.A.W), da kuma shugabanci da suka ratso tun mulkin-mallaka har zuwa zamanin 'yancin kai.
Wannan ɗorewa a mulki ta sa masarautar ta Moroko ta kasance ta biyu mafi daɗewa da har yanzu take mulki, bayan ta Japan.
Sarki Mohammed na shida yana da shekara 36, a lokacin sunansa Sidi Mohammed, kasancewarsa babban ɗan sarki ya gaji mahaifinsa Sarki Hassan na biyu, wanda ya rasu ranar 23 ga watan Yuli, 1999.
Sarki Mohammed na shida ya gudanar da sauye-sauye da dama a ƙasar tun lokacin da ya karɓi jagorancin ƙasar.
Manyan birane huɗu na tarihi: Fez, Marrakech, Meknes, Rabat

Asalin hoton, Carbonell Pagola/LightRocket via Getty Images
A tarihinta Moroko ta yi babban birni na ƙasa har guda huɗu.
Fez, da Marrakech, da Meknes, sai kuma na baya-bayan nan Rabat, kuma dukkanmim waɗannan birane sun kasance mazaunar gwamnati, daga zamanin masarauta zuwa masarauta da kuma yanayi.
Kowanne daga cikin biranen huɗu na ɗauke da abubuwa na tarihi da suka danganci siyasa da tattalin arziƙi da makamantansu.
Jami'ar da ta fi daɗewa a duniya - Al Quaraouiyine

Asalin hoton, Getty Images
Jami'ar Quaraouiyine (ko Al-Qarawiyyin), wadda aka kafa tun a shekarar 859 a birnin Fez, ita ce mafi daɗewa da har yanzu take aiki a duniya , kamar yadda hukumar ilimi da kimiyya da al'adu ta duniya, UNESCO, da kuma kundin bajinta na duniya (Guinness World Records), suna nuna.
Wannan jami'a ta horas da malaman addinin Musulunci da masana da dama tsawon ƙarni daban-daban inda ta taimaka wajen bunƙasar Moroko da kuma al'adun Musulunci.
Ɗakunan karatun wannan jami'a na ɗauke da takardu da muhimman littattafai masu tarihi.
Man Argan mai abin mamaki

Asalin hoton, Getty Images
Man Argan wanda ake yi daga 'ya'yan itacen argan, bishiyar da ake samu a yankin kudu maso yammacin Moroko, na da daraja sosai kuma ya kasance wata alama ta ƙasar.
Man wanda ake nema sosai wanda ake abinci da shafa, a yanzu ya zama wata alama ta ƙasar ta Moroko.
Man ya zama wata hanya da matan karkara suke dogaro da kai, ta yadda suke yinshi daga 'ya'yan itace ta hanyoyi na gargaji.
Bishiyar ta argan wadda ake samu a yankunan hamada na, Agadir, da Essaouira, da Tafraout, da Taroudant na Moroko, na jure wa zafi da fari, kuma tana iya rayuwa tsawon shekara 150 zuwa 200.
Arzikin dabino

Asalin hoton, Getty Images
Ana samun bishiyoyin dabino a yankuna irin su Goulmima, da Zagora, da kuma kwarin Draa, inda bishiyoyin ke yi saboda zafi da kuma kasar yankunan.
Dabino na da muhimmanci a rayuwar yau da kullum a Moroko, a fannin abinci da kuma al'ada.
Ana noman dabino, wanda ke da muhimmanci na al'ada da kuma addini, a Moroko tun shekaru dubbai.
A lokacin azumin Ramadan, dabino na da muhimmanci sosai a ƙasar da ma sauran ƙasashen Musulmi, inda ake buɗa-baki da shi da ruwa, kamar yadda Sunnar Annabi Muhammad (SAW) ta tanada.
Dabino na daga cikin kayan amfanin gona a ciki da wajen ƙasar, kasancewar Moroko na fitar da shi waje.
Abota da shan shayi

Asalin hoton, Getty Images
Ba ta yadda za ka yi magana a kan Moroko ba tare da ka ambato fitaccen shayinta ba - na na'ana.
Shayi ne da za ka gani kusan a kodayaushe a ko'ina, wanda ya zama wata alama ta ƙasa, da kuma zama wata hanya ta kyautata wa da al'ummar ta Moroko ke yi wa baƙinsu.
Ana amfani da wannan shayi wajen buɗe taruka na tattaunawa ta abokan ciniki ko iyalai ko kuma kammala cin abinci na ciyayyar iyali.
Ba a dai san lokacin da aka fara wannan ala'ada ta shayin ba a Moroko, amma an yi amanna ta somsa ne daga ƙarni na 17 a zamanin mulkin Sultan Moulay Ismail, a lokacin da ake bayar da sha'ayi a matsayin wata kyauta ta diflomasiyya ga Turawan Ingilishi.
A yau Moroko ta kasance ɗaya daga cikin manyan ƙasashen da suka fi sayen ganyen shayi a duniya, musamman na China (koren ganyen shayi).
Cin kasuwar dare

Asalin hoton, Getty Images
Kasuwannin dare na Marrakech ba ba wurare ba ne kawai na yawo ko shaƙatawa - wasu kafafe ne na tattalin ariƙi da kuma alama ta al'ada ta Moroko.
Da dare ya yi birnin Marrakech na juyewa ya zama wani fili mai ban sha'awa, inda kasuwannin dare musamman wadda take dandalin Jemaa el-Fna inda suke zama wata cibiya ta rayuwar birni.
Masu ziyara daga ko'ina a duniya na tururuwa zuwa waɗannan kasuwanni na dare, domin sayen kayayyaki da kuma kashe ƙwarƙwatar idanuwansu.
Birnin yin fim da ke hamada

Asalin hoton, Getty Images
Ouarzazate ƙaramin gari ne da ke yankin kudu maso gabashin Moroko, a daidai inda hamadar Sahara ta fara.
Tsawon gomman shekaru wannan yankin ya kasance cibiyar haɗa fina-finai ta Atlas Studios, wadda tana ɗaya daga cikin manyan wuraren yin fina-finai a duniya bayan Hollywood da ke Amurka.
Hakan ya sa wajen ya zama wajen da ake yin fitattun fina-finai da shirye-shirye na talabijin.
An yi fina-finai irin su Gladiator da Lawrence of Arabia da Kundun da kuma The Mummy har ma irin su Game of Thrones.
Ƙwallon ƙafa sabuwar hanyar fice a duniya

Asalin hoton, Getty Images
Tun bayan da ya hau gadon sarauta a 1999, Sarki Mohammed na shida ya mayar da ƙwallon ƙafa wata hanya ta ciyar da ƙasar gaba da fitar da ita a idon duniya ta zama mai tasiri, ta hanyar samar da kayayyaki da wuraren wasan na zamani da masu koyarwa ƙwararru da kuma bunƙasa wasan har na mata.
Wannan mataki ya samar da kyakkyawan sakamako, kamar nasara mai tarihi ta tawagar Morokon inda ta je wasan kusa da ƙarshe na gasar cin Kofin Duniya ta 2022, da komawar ƙasar mataki na 14 a tsakanin ƙasashen duniya a jadawalin ƙwarewa na Fifa, da kuma nasarar ƙasar a gasar cin Kofin Duniya ta 'yan ƙasa da shekara 20 inda ta doke Argentina 2-0 ta ci kofin.
Yanzu Moroko na zama wata tauraruwa a wasan ƙwallon ƙafa a duniya, inda za ta karɓi baƙuncin wasan cin Kofin Afirka na bana - 2025, sannan za ta karɓi baƙuncin haɗin gwiwa na gasar Kofin Duniya na 2030, tare da Sifaniya da Portugal.











