Yadda ƙasashen Turai ke shirin yin fito-na-fito da Trump kan yunƙurinsa na mallakar Greenland

- Marubuci, Katya Adler
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Europe Editor
- Lokacin karatu: Minti 6
Donald Trump ya ci gaba da jajircewa kan batunsa na son mallakar yankin Greenland.
Ya bayyana a ranar Litinin cewa Amurka na son tsibirin ne kan dalilai na tsaro.
Shin ya shirya ne wajen amfani da ƙarfi don ƙwace yankin, tambayar da ƴan jarida suka yi masa.
"Ba zan ce komai ba," in ji Trump, inda sakon ya ɗan kwantar wa ƴan yankin hankali.
Greenland yanki ne mai ƴanci, da ke mulkin kansa a ƙarƙashin masarautar Denmark - kuma mamba a Tarayyar Turai da Nato. Yanzu shugaba Trump ya dogara ne kan ƙawayen Denmark a waɗannan ƙungiyoyi domin watsi da Copenhagen don ganin Amurka ta karɓi ikon Greenland, ko kuma su fuskanci matsanancin haraji kan kayayyaki da za su shigar Amurka.
Lamari mai tayar da hankali ga tattalin arzikin ƙasashen Turai, waɗanda tuni suke cikin wani hali. Musamman waɗanda suka dogara da shigar da kaya Amurka, kamar masana'antar ƙera motoci ta Jamus da kuma kasuwar hada-hadar kayayyaki ta Italiya.

Asalin hoton, AFP via Getty Images
A ranar Litinin, ministan harkokin kuɗi na Jamus ya ce, "ba za mu bari a ɓata mana suna ba" bayan wani zama da takwaransa na Faransa.
Barazanar Trump ta kasance kamar cin fuska ga gwamnatocin Turai, waɗanda (ban da Tarayyar Turai da Birtaniya) a bara ne suka cimma yarjejeniyar haraje-haraje da Trump.
"Muna rayuwa ne a cikin wani yanayi. Ba mu taɓa ganin haka ba. Abokiyar mu na tsawon shekara 250 na son amfani da batun haraji a matsayin makami," in ji ministan kuɗi na Faransa Roland Lescure.
Takwaransa na Jamus Lars Klingbeil ya ƙara da cewa: "An shata layi... za ka gane cewa a yau ba na faɗan abin da zai faru. Amma akwai abu ɗaya: Dole Turai ta shirya."
Da alama salon da shugabannin Turai ke yi na bin Trump a sannu-a sannu tun bayan komawarsa mulki karo na biyu, ya wuce wa'adinsa.
Bin hanyar lalama da kuma nuna iko
Ya yi wuri a fayyace makomar dangantakar ƙasashen da Amurka, sai dai Tarayyar Turai na fatan tausasa murya yayin haɗuwa da Trump a Switzerland ranar Laraba a taro kan tattalin arzikin duniya.
Tsohon shugaban Amurka Theodore (Teddy) Roosevelt, ya yi imanin cewa idan kana son cimma burinka, kana da buƙatar amfani da diflomasiyya da kuma iko mai ma'ana. A yanzu ta nuna Turai na amfani da duka hanyoyin na lalama da kuma iko.
Shugabannin Turai sun faɗa wa Trump cewa za su mara masa baya wajen ba da fifiko a tsaron yankin Arctic, don haka babu buƙatar ya yi gabansa wajen zuwa sayan Greenland.
A lokaci guda, jami'an diflomasiyya na Turai sun bayyana cewa suna duba yiwuwar lafta wa kayayyakin Amurka harajin yuro biliyan 93 ko kuma taƙaita damar da kasuwannin Amurka ke a shi, ciki har da bankuna da manyan kamfanonin fasaha, idan Trump ya ki saduda kan cewa zai saka musu haraji idan suka ki amincewa da kudurinsa na sayan Greenland.

Asalin hoton, Bloomberg via Getty Images
Waɗannan matakai na ramuwar gayya za su iya yin lahani har ga masu sayan kayayyakin Amurka.
Masu zuba jari a Turai suna da jari a kusan jihohi 50 na Amurka, kuma an ce sun samarwa Amurkawa miliyan 3.4 aiki.
Amincewa da tsaron Amurka
A ranar Litinin, sakataren baitil-malin Amurka Scott Bessent ya bayyana ba tare da wata ƙwarin gwiwa ba.
Da yake magana a birnin Davos, ya ce: "Shugaba Trump na duba Greenland a matsayin wata kadara ta Amurka. Ba za mu bai wa kowaye tsaron mu ba."
Ya gargaɗi Turai kan barazanar lafta haraji a matsayin hanyar ramuwa.
Wasu na nuna damuwa a Turai cewa idan aka ci gaba da yin fito na fito da Trump, lamarin zai iya mayar da ƙasar saniyar ware.
Maganar gaskiya ita ce: Turai na buƙatar Washington domin cimma yarjejeniyar zaman lafiya mai ɗorewa a Ukraine da kuma tsaron nahiyarta. Har yanzu Turai na dogaro da Amurka ainun, duk da alkawarin ƙara yawan kuɗaɗe da ake kashewa a ɓangaren tsaro.

Asalin hoton, Getty Images
Yayin da yake ƙara nanata goyon bayansa ga Denmark da kuma ƴancin Greenland, Firaministan Birtaniya, Sir Keir Starmer ya ce "Burin Birtaniya ce wajen ganin mun ci gaba da aiki da Amurkawa idan aka zo ga batun tsaro da kuma tattara bayanan sirri.
"Babban alhakina shi ne tsare lafiyar kowaye a Birtaniya kuma hakan na buƙatar mu samu kyakkyawar dangantaka da Amurka," in ji shi.
Sai dai, idan Turai ta ci gaba da lallaɓa shugaba Trump, maimakon fito masa kai-tsaye yayin da yake barazana ga ƴancin ƙawarsa a Nato (Denmark) da kuma lafta takunkuman tattalin arziki kan sauran ƙawayensa idan suka mara wa Copenhagen, to nahiyar na cikin babbar barazana.

Asalin hoton, Shutterstock
A ranar Litinin, wata babbar jami'iar diflomasiyya a Turai Kaja Kallas, ta wallafa a shafin X cewa, "Ba mu da burin shiga faɗa da Amurka, amma za mu tsaya kan matsayar mu".
Putin da ƙungiyar samar da zaman lafiya
Ba Rasha ce kaɗai ke kallon wannan dambarwa daga gefe ba, sai dai har da China.
Ƙasashe masu ƙarfin iko na ci gaba da mamaye duniya, ciki har da Rasha da China, akwai kuma Indiya, Saudiyya, kai har ma da Brazil.
China na fatan dambarwar Trump a ƙawayensa za su ƙara saka Beijing ta zama babbar ƙawa da kuma za ta ɗauke ɗimbin masu zuba jari zuwa wajenta.
Canada, wadda Trump ya yi barazanar mayar da ita jihar Amurka ta 51, ba ta daɗe da amincewa da wata takaitacciyar yarjejeniyar kasuwanci ba da China. Tana son rage barazanar da Washington ke yi mata.

Asalin hoton, AFP via Getty
Shugaban Amurka bai mutunta ƙungiyoyi irin Nato da kuma Majalisar Ɗinkin Duniya ba waɗanda ƙasashen yamma masu ƙarfi suka kafa bayan yaƙin duniya na biyu, don tabbatar da an bi tsarin dokoki na duniya.
Wasu sun yi nuni ga ƙungiyar samar da zaman lafiya da Trump ke ƙoƙarin kafa wa a yanzu, kuma yana son gudanar da bikin saka hannu kan lamarin a birnin Davos ranar Alhamis. Shugabannin duniya da dama da kuma manyan ƴan kasuwa za su halarci bikin.
An tsara cewa ƙungiyar za ta saka ido wajen sake gina Gaza bayan yaƙin Isra'ila Isra'ila na shekara biyu da ya ɗaiɗaita yankin, wanda ta yi da nufin wargaza mayaƙan Hamas, bayan hari da ƙungiyar ta kai ranar 7 ga Oktoban, 2023.

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Dangantaka ta yi tsami
Tsare-tsaren Trump yana girgiza irin waɗanannan ƙungiyoyi na duniya.
Mambobin Turai da ke cikin ƙungiyar Nato sun bayyana cewa dole ne su riƙa biyan kuɗaɗe masu yawa wajen tsaron ƙasashensu. Ba Trump ne shugaban Amurka na farko ba da ya ce su yi haka, duk da cewa matakinsa ya fi yin tsauri.
Sai bayan da Trump ya yi barazanar cewa Amurka ba za ta ci gaba da tsaron ƙasashen da ba sa kashe kuɗi a tsaronsu, kafin nan ne dukkan mambobin Nato ban da Sifaniya suka amince da ƙara yawan kuɗin da suke kashe wa.
Idan muka koma can Greenland, kuri'ar jin ra'ayi ta nuna cewa kashi 55 na Amurkawa ba a son a sayi tsibirin sannan kashi 86 kuma sun yi adawa da ɗaukar matakin soji don karɓe yankin da Amuka ke son yi.
Denmark da sauran ƙasashen Turai na son jan ra'ayin ƴan majalisar Amurka wajen ganin an kare ƴancin Greenland da kuma Denmark.

Asalin hoton, Getty Images
Dangantaka ba ta kai ga karye wa ba, duk da cewa ta lalace. Har yanzu Donald Trump na ɗaukar waya daga abokansa da suka haɗa da Firaministar Italiya, Giorgia Meloni da Starmer, har ma ga sakatare-janar na ƙungiyar Nato Mark Rutte. Har yanzu hanyoyin sadarwa na buɗe.
Amma idan Turai na son galaba kan Trump, dole sai sun haɗa kai.











