'Zargin ƙwace babura 17 na ƴanbindiga ne ya yi sanadin sace mutane a Kajuru'

Kurmin Wali
Lokacin karatu: Minti 4

Sarkin ƙauyen Kurmin Wali da ke ƙaramar hukumar Kajuru na jihar Kaduna - inda aka yi garkuwa da kusan mutum 177 - ya ce ƴanbindiga sun ce musu saboda sun ƙwace babura ne suka sace musu mutane.

Sarkin garin, Ishaku Ishaku E. Sidi ne ya bayyana haka, inda ya ce lamarin ya tayar musu da hankali, sannan ya buƙaci gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki su kai musu ɗauki na gaggawa.

A cewasa, lamarin ya auku ne a ranar Lahadi a lokacin da suke gudanar da ibadarsu ta mako-mako.

"Sun faɗo mana ne a lokacin da muke ikilisiyya (ibada a coci), suka kwashe mana mutane suka shiga daji da su."

Jagoran ƙauyen ya ce lamarin ya firgita kowa a ƙauyen, amma ya ce babu abin da za su yi face neman agajin gaggawa.

"Babu abin da za mu iya yi. Muna roƙon duk wanda zai iya taimaka mana, da ya taimaka mana domin ceto ƴan'uwanmu. Sun ce mana mun ɗauke musu babura 17 ne, kuma sai mun biya baburan kafin su sako mana mutanenmu," in ji Ishaku.

A game da adadin mutanen da aka sace, sarkin ya nanata cewa lallai an yi garkuwa da mutum 177.

"Amma mutum 11 sun kuɓuta sun dawo, amma muna samun jita-jitan cewa an ga wasu amma gaskiya ba su dawo ba, wataƙila suna daji ne ba su ƙaraso ba. Mu ɗai har yanzu waɗanda muke nema mutum 166 ne."

A ƙarshe sarkin ya yi kira da a kai musu ɗaukin abinci da jami'an tsaro da sauran su, domin a cewarsa, su manoma ne, kuma harin ya illata su. "Sannan muna roƙo a taimaka wa matasanmu da sana'a saboda su zama masu dogaro da kai domin gudun kada su zama ɓatagari."

'Yadda na tsira'

Kurmin Wali

Ɗaya daga cikin waɗanda aka sace a harin na ranar Lahadi, Maigirma Shekarau ya ce ana cikin tafiya da su ne ya samo damar sulalewa ya ɓoye a wani gida ya ɓoye har ƴanbindigar suka tafi.

"Yadda abin ya faru shi ne muna cikin coci ne sai muka ji ana ta ihu. Da muka fito sai muka ga ƴanbindiga sun kewaye garin, sai suka kwashe suka shiga daji da mu," in ji shi.

Maigirma ya ce da suka fara tafiya, sai "suka tsaya suka fara mana tambayoyi da duka. Bayan sun gama tambayoyin ne sai muka ci gaba da tafiya."

Ya ce da suka isa wani gari da ake kira Sabon Gida, "dama sun kori mutanen garin babu kowa. A nan ne na samu dama na sulale na shiga wani ɗaki tare da wata yarinya da na riƙe. Bayan kusan awa biyu sai na fito na nemo hanya na dawo gida" in ji Magirma.

Shi ma ya tabbatar da adadin waɗanda aka kwashe, sannan ya ƙara da cewa suna cikin tashin hankali, "domin ba mu san halin da ƴan'uwanmu suke ciki ba."

Kai-koma kan tabbatar da sace mutanen

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tun da farko, a ranar Litinin aka fara samun rahotannin cewa mahara sun shiga ƙauyen na Kurmin Wali tare da sace mutane kimanin 170 a yankin mai fama da matsalar tsaro.

Amma a ranar Litinin ɗin, sarkin Kurmin Wali, Ishaku Dan'azumi ya tabbatar wa BBC cewa maharan sun je ƙauyen ne a ranar Lahadi, inda suka sace mutane sama da 160.

"Sun zo ranar Lahadi wurin karfe 9, lokacin muna coci, suka bazu a garin, suka sa mu a tsakiya.

"Waɗanda suke a hannunsu yanzu 166," in ji Ɗan'azumi.

Shi ma shugaban ƙungiyar CAN a arewacin Najeriya Jospeh Hayab ya tabbatar wa kafafen yaɗa labarai batun sace mutunan a ranar ta Litinin.

Ya ce, "duk da cewa ban cika son ambata adadi ba, amma bayanan da na samu daga yankin na nuna cewa ƴanbindiga sun sace kusan mutum 172, amma guda 9 sun tsere sun koma gida, amma har yanzu ana neman mutum 163," in ji shi.

A ranar Litinin da dare ƴansandan suka fara fitar da sanarwa a kan batun, suna jaddada rashin bayanan da za su tabbatar da rahotannin da jaridun ƙasar da dama suka wallafa cewa an sace mutane fiye da 100 a wuraren ibadar su a ranar Lahadi, tare da kiran rahotannin a matsayin labaran bogi.

Sai dai a wata sanarwar ta daban da ƴansandan suka fitar cikin dare a ranar Talata, rundunar ta ce ba a fahimci sanarwarta ta farko ba ne, tana mai cewa dama can ta nemi a bayar da sahihan bayanai ne masu tabbatar da sunayen mutanen da aka sacen da kuma ƙauyukansu.

Kakakin rundunar ƴansandan Benjamin Hundeyin ya ce binciken da sashin tattara bayanan sirri na rundunar ya gudanar ya tabbatar masu cewa an yi garkuwa da mutanen.

Bai sanar da yawan mutanen da aka sace ba, amma ya ce rundunar ta tura jami'anta zuwa Kajuru da kewaye domin aikin gano wajen da ake tsare da mutanen da aka sace.

Tuni dai ƙungiyoyin fararen hula suka fara martani kan batun, inda ƙungiyar Amnesty International soki hukumomin Najeriya, waɗanda ta ce suna neman ɓoye haƙiƙanin abin da ya faru.

Ƙungiyar ta ce "Dole ne mahukunta su ɗauki matakan gaggawa domin hana ci gaba da garkuwa da mutane masu yawa da ke neman zama ruwan dare a Najeriya.''