BBC ta samu hotuna da bidiyon yadda aka kashe masu zanga-zanga a Iran

- Marubuci, Merlyn Thomas
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, correspondent, BBC Verify
- Marubuci, Shayan Sardarizadeh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, senior journalist, BBC Verify
- Marubuci, Ghoncheh Habibiazad
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, senior journalist
- Lokacin karatu: Minti 4
Gargaɗi: Wannan labari na ɗauke da bayanai da za su iya tayar da hankalin mai karatu.
BBC ta samu ɗaruruwan hotuna da ke nuna fuskokin masu zanga-zanga da aka kashe yayin zanga-zangar ƙin jinin gwamnati a Iran.
Hotunan waɗanda ba su da kyawun gani, sun nuna gawawwaki sama da 326 cikin jina-jina fuskoki a kumbure - ciki har da mata 18. Hotunan, waɗanda aka ajiye a wani mutuware da ke kudancin Tehran, ita ce hanya ɗaya tilo da iyalai za su iya gane gawawwakin ƴan uwansu da suka mutu.
Ba a iya gane mutanen da suka mutu saboda yanayi mara kyau da gawawwakin ke ciki, kuma an bayyana mutum 69 a Tehran ɗin a matsayin John ko kuma Jane Doe, abin da ke nuifn cewa ba a san asalinsu ba lokacin da aka ɗauki hotunan. Mutum 28 kaɗai cikin gawawwakin aka gane asalinsu har ma da sunayensu cikin hotunan.
An bayyana cewa mutum sama da 100 cikin gawawwakin sun mutu ne ranar 9 ga Janairu, wanda ya kasance ɗaya daga cikin dare mafi muni ga masu zanga-zanga a Tehran zuwa yanzu.
An cinna wuta kan tituna da ke birnin yayin artabu tsakanin jami'an tsaro da masu zanga-zanga, inda masu boren ke rera waƙoƙin adawa da shugaban addini na ƙasar da kuma Jamhuriyar Musulunci.
Hakan ya biyo kiran da Reza Pahlavi ɗan sarkin ƙasar na karshe da ke zaman gudun hijira ya yi na cewa a fito zanga-zanga a faɗin ƙasar.
Hotunan da BBC ta samu kaɗan ne daga cikin dubban masu zanga-zanga da ake kyautata zaton sun mutu a hannun hukumomi a Iran.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
BBC ta kasance tana bibiyar yadda zanga-zangar ke yaɗuwa a faɗin Iran tun bayan ɓarkerwarta a karshen watan Disamba, sai dai toshe hanyoyin intanet da hukumomi suka yi, ya janyo da wahala a iya samun ainihin alkaluman mutanen da suka mutu a zanga-zangar.
Shugaban addini na ƙasar Iran Ayatollah Ali Khamenei ya fito fili ya bayyana cewa dubban masu znaga-zanga ne suka mutu, sai dai ya ɗora laifin haka kan Amurka, Isra'ila da kuma waɗanda ya kira masu tayar da zaune tsaye.
Duk da cewa katse hanyoyin intanet ɗin na shiga mako na uku, sai dai hakan bai hana wasu mutane kalilan samun bayanai ba.
BBC ta samu ɗaruruwan hotunan waɗanda aka kashe da aka ɗauka a wani asibiti a birnin Kahrizak.
Mun yi duba kan hotuna 392 na waɗanda aka kashe inda muka samu damar gano 326 - an ɗauki hotunan wasu fiye da sau ɗaya. Majiyoyi sun yi iƙirarin cewa ainihin alkaluman gawawwaki a mutuwaren ya haura dubbai.
Wani ganau, wanda muka ɓoye sunansa saboda kariya, ya faɗa mana cewa ba su shirya tarbar irin gawawwakin da aka kai zuwa cikin ɗakin ajiye gawarwakin, kuma ya ce sun ga gawarwaki daga masu shekara 12, 13 zuwa 60 da kuma masu shekara 70. "Abun ya yi yawa," in ji shi.
Yayin da ake cikin ruɗani a mutuwaren, iyalai da abokai na ta tururuwar zuwa cikin ɗakin ajiye gawarwakin, kamar yadda aka faɗa mana. Suna ƙoƙarin gano ƴan uwansu yayin da aka liƙa ɗaruruwan hotunan waɗanda suka mutu.

Asalin hoton, User generated content
An haska hotunan a jikin wani allo na wasu sa'o'i, kuma raunukan da yawancin mutanen suka ji sun yi munin da ba za a iya gane su ba. Fuskar wani mutum ta kumbura da kyar ake iya ganin idanunsa. Wani mutum kuma na da bututun taimakon numfashi a bakinsa, abin da ke nuna cewa ya mutu lokacin kualwa.
Raunukan da wasu da lamarin ya shafa ya yi munin da sai da iyalansu suka yi ta kallon hotunan har na tsawon lokaci kafin su iya gane cewa su ne. Wasu lokuta kuma mutane na gane ƴan uwansu ba tare da wahala ba inda suke yanke jiki su faɗi a ƙasa, tare da tsala ihu.
Hotuna da dama sun nuna gawawwakin da ba a rufe su ba inda aka liƙa takardu kusa da fuskokinsu, inda ake gane su ta hanyar sunayensu, wasu lambobi ko ranar da suka mutu.
An faɗa mana cewa wasu lokuta kuma, ana gane gawa ne ta hanyar wani kati da aka saka a kanta.
BBC ta tabbatar da hotunan bidiyo da aka samu daga mutuwaren wanda ya nuna irin mummunan cin zarafi da aka yi wa masu znaga-zangar. Wani bidiyo ya nuna gawar wani yaro, yayin da wani kuma ya nuna na mutum tare da raunin bindiga a kansa. Duka bidiyoyin masu tayar da hankali ne.
Wasu Iraniyawa sun yi ta wallafa sunayen waɗanda jami'an tsaro suka kashe lokacin da suka samu intanet ta hanyar Starlink ko kuma intanet daga ƙasashe makwabta, duk da cewa wannan dama ba ta cika samuwa ba.
Mun yi duba kan sunayen waɗanda aka gane a mutuwaren a kan wani wallafa da aka yi na sunayen waɗanda suka mutu a kafar sada zumunta, kuma mun gano sunaye biyar da suka zo iri ɗaya, sai dai ba za mu bayyana sunayen ba saboda ba mu samu dmaar tuntuɓar iyalansu ba.

Har ila yau, BBC ta bi diddigin zanga-zangar ta adawa da gwamnati zuwa faɗin birane da garuruwa 71 a Iran tun bayan ɓarkewar zanga-zangar ranar 28 ga watan Disamba ta hanyar wani bidiyo da aka tantance, duk da cewa yankunan da aka yi zanga-zangar za su iya fin haka.
Hotuna kalilan da mutane suka samu damar wallafawa sun nuna motocin da suka ƙone ƙurmus a kan tituna, yayin da aka kuma ji ƙarar bindigogi da aka harba a faɗin Tehran lokacin zanga-zangar.
Toshe hanyoyin intanet ya janyo wahala a iya gano yawan alkaluman waɗanda suka mutu a zanga-zangar.
Sai dai, kamfanin dillancin labarai da ke kare hakkin ɗan'adam ta Amurka (HRANA) ya saka alkalumansa cewa mutum sama da 4,000 aka kashe.










