'Abin kunya' da 'takaici' - hargitsin da ya lalata nasarar Senegal

Security personnel block angry fans over a penalty decision against Senegal during the Africa Cup of Nations final

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Magoya bayan Senegal sun yi arangama da jami'an tsaro bayan bai wa Moroko fenareti
    • Marubuci, Keifer MacDonald
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport journalist
  • Lokacin karatu: Minti 6

Senegal ta ɗauki kofin Afirka karo na biyu, bayan doke Moroko a wasan ƙarshe - to amma wasan na cike da abubuwa, ciki har da ficewa daga fili da ƴan wasan Senegal suka yi bayan bai wa Moroko bugun fenareti ana dab da tashi daga wasan.

Alƙalin wasan Jean Jacques Ndala ya bayar da fenaretin a minti na 98 da taimakon na'urar VAR, saboda ƙetar da El Hadji Malick Diouf ya yi wa Brahim Diaz na Moroko a da'irar gidan Senegal.

Lamarin ya tayar da hargitsi a cikin filin, inda har kocin Senegal Pape Thiaw, ya umarci ƴanwasansa su fice daga fili.

To sai dai tsohon ɗan wasan Liverpool - wanda shi ne jigon ƴanwasan ƙasar - Sadio Mane ya ƙi amincewa da shawarar koci, inda ya tsaya a filin ya riƙa ƙoƙarin kiran takwarorin nasa su tsaya a ƙarasa wasan.

Har ma ya bi wasu ƴan wasan zuwa ɗakin da sauya tufafi ya kuma kirawosu suka dawo cikin filin.

Bayan kusan jinkiri na kusan minti 17, duka ƴan wasan sun koma cikin filin, inda aka buga fenaretin.

Sai dai ɗan wasan gaban Real Madrid, Diaz da ya buga fenaritin ya kasa ci, duk da cewa shi ne ya fi kowa zura ƙwallaye a gasar.

Bayan ƙarin lokaci ɗan wasan gaban Senegal Pape Gueye ya zura ƙwallon da ta bai wa Senegela nasara a wasan, inda ta ɗauki kofin karo biyu cikin shekara biyar.

A hirarsa da manema labarai bayan kammala wasan, kocin Moroko, Walid Regragui ya ce abin da Senegal ta yi ''abin kunya'' ne kuma zubar da ''kimar Afirka'' ne

Shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Duniya, Fifa, Gianni Infantino ya yi Allah wadai da ''munanan abubuwan da suka faru'', cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Instagram.

Senegal lift the Afcon trophy after beating Morocco

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Senegal ta ɗauki kofin Afirka na biyu cikin shekara biyar, bayan da suka fara ɗauka a 2021
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Shi kuwa Thiaw, an soke hirarsa ta manema labarai bayan da ruɗani ya tashi a ɗakin hirar labaran.

Am ma a wata hira da BeIN Sport, ya amince cewa bai kamata ya umarci ƴanwasansa su fice daga fili ba.

"Bai kamata mu yarda ba," in ji shi. "Ba na son yin tsakaci kan duka abubuwan da suka faru, amma ina mai bayar da haƙuri kan abin da ya faru.

"Bayan na fahimci kuskure ne abin da na yi na faɗa musu su koma fili, idan abu ya faru dole ka ɗauki hukunci cikin fushi. Amma yanzu mun amince da kuskurenmu''.

"Bai kamata mu yi hakan ba, amma tun da mun riga mun yi muna neman afuwa ga hukumar ƙwallon ƙafa."

Thiaw, mai shekara 44, da fari ya ji haushi alƙalin wasan saboda soke ƙwallon da Ismaila Sarr ya ci saboda ƙetar da aka yi wa Hakimi a lokacin da aka fara ɗauko ƙwallon.

Bayan kammala wasan, Mane ya ce ''Ƙwallon ƙafa wani abu ne na musamman, duniya na kallonku, don haka dole mu nuna halin dakkatu.

"Ina ganin rashin buga wasan zai zama mafi muni fiye da fenaretin da aka bayar Na gwammace mu yi rashin nasara a maimakon ficewa daga filin'', in ji shi.

Tsohon mai tsaron ragar Chelsea Mendy, wanda a yanzu ke wasa a Al-Ahli ta ƙasar Saudiyya ya ce yana ''alfahari'' yadda ƴanwasan Senegal suka koma fili bisa umarnin Mane, kuma suka yi nasarar ɗaukar kofin.

"Mun amsa kiransa, mun dawo kuma mun yi nasara, don haka muna alfahari da hakan ."

Wanda ya zura ƙwallon da ta bai wa Senegal nasara, Gueye ya ce "Mun ji kamar ba a yi mana adalci ba. Kafin bayar da fenaretin mun ci ƙwallo amma ba aje aka duba na'urar VAR ba''.

"Sadio [Mane] ya ce mana mu koma fili, kuma mun koma. Daga nan Edouard [Mendy] ya kama fenaretin, mun sake mayar da hankali, kuma yi nasarar zura ƙwallo'', in ji shi.

'Ba za mu lamunci rikici a wasanni ba'

Bayan taya Senegal murnar ɗaukar kofin da jinjina wa Moroko kan ƙoƙarinta na ɗaukar nauyin gasar, Shugaban Fifa ya nuna rashin jin daɗinsa kan abubuwan da suka faru a filin.

Cikin saƙon da ya wallafa a shafin nasa na Istagram, Infantino ya ce ''Ba za mu lamunci fita daga fili ba a lokacin d ake tska da wasa, haka nan ba za mu yarda ta tayar da rikici a wasaninmu ba, domin hakan bai dace ba''.

Yana mai cewa dole ne a yi biyayya ga hukuncin alƙalin wasa a koyaushe idan ana cikin fili, rashin biyayya ko yaya ka iya haifar da mummunan hatsari.

Infantino, mai shekara 55, ya ce dole ne a yi "tir da abin da ya faru, kuma kada ya sake faruwa", kuma haƙƙi ne kan ƴan wasa da tawagogi su bayar da kyakkyawan misali a kowane lokaci.

Shugaban an Fifa ya buƙaci hukumar ƙwallon ƙafar Afirka Caf ta ɗauki matakan ladabtarwa da suka dace kan wadanda suka saɓa dokokin hukumar.

A nata ɓangare ita ma hukumar ƙwallon ƙafar Afirkan CAF ta yi ''allah wadai da halin rashin ɗa'a da suka faru a wasannin gasar, musamman inda aka riƙa farmakar alƙalan wasa ko masu shirya wasa''.

Cikin sanarwar ta hukumar ta fitar ta ce za ta yi nazarin bidiyoyin abubuwan da suka faru tare da ɗaukar matakan ladabtar da suka dace kan waɗanda aka samu da laifi.

'An ƙare gasar ta mummunar hanya'

Fans scuffle with security personnel as they storm the field after a penalty decision against Senegal during the Africa Cup of Nations

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban Fifa da hukumar Caf sun yi allah wadai da abin da ya faru a ranar Lahadi.

An kammala gasar ta yanayi maras kyau, wanda hakan tamkar kunyata Afirka ne a idon duniya.

Na yi mamakin abin da ya faru lokacin wasan, inda na ga wasu magoya bayan na koƙarin shiga fili, lamarin da ya hargitsa duka filin.

Sannan ƴanwasan Senela suka fice daga filin. Wannan abu mai muni ne a Gasar Kofin Afirka.

Idan ka dubi abubuwan da suka faru a tsawon makonnin gasar, an samu jayayya mai yawa - fiye da gasannin da aka yi a baya, musamman kan hukunce-hukuncen alƙalan wasa da na'urar VAR ke yi.

An samu wasu ƴanjarida da magoya baya suka riƙa zargin cewa alƙalan wasa suna fifita Moroko.

'Jajircewa da ƙoƙarin Mane'

Duk da munanan abubuwan da suka faru a wasan na ƙarshe, an samu wani abin burgewa a wasan daga Sadio Mane.

Shi ne kaɗai ɗan wasan Senegal da ya ƙi ficewa daga filin, a maimakon haka ya riƙa kiran takawarorinsa ƴanwasa su koma fili.

Ya kuma je har cikin magoya bayan Senegal a wajen fili bayan tashi daga wasan, yana mai roƙonsu su kwantar da hankali, su daina hayaniya

Senegal ta nuna 'damuwa' kan tsaro kafin wasan

Kafin wasan na ranar Lahadi a birnin Rabat, hukumar ƙwallon ƙafar Senegal, ta bayyana ''fargabarta'' kan tsaron ƴanwasanta.

Dandazon magaoya baya sun mamaye zakarun Afcon na 2021, a lokacin motarsu ta zol domin daukarsu a babban birnin ƙasar ranar Juma'a.

Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta kuma yi ƙorafi kan rashin kyawun otal ɗin daka sauke su, da adadin tikitin da aka ware wa magoya bayansu, da kuma zargin rashin ba su wurin atisaye a birnin na Rabat.

Hukumar ƙwallon ƙasar Senegal din ta ce ''rashin tsaro'' ya jefa ƴanwasanta a ma'aikata cikin ''hatsari''.

Ficewa daga fili 'kunyata Afirka ne'

Tsohon ɗan wasan Najeriya Efan Ekoku ya soki matakin da Thiaw da wasu ƴanwasansa suka ɗauka, yana mai cewa ƙaurace wa wasa da suka yi na ɗan lokaci ''abin kunya ne ga ƙwallon ƙafar Afirka''.

"Fenaretin da aka bayar yana kan daidai," kamar yadda Ekoku ya shaida wa kafar yaɗa labarai ta E4.

"Abin da El Hadji Malick Diouf ya yi ganganci ne kuma babban kuskure, amma tun da an yi hukunci ya kamata ƴanwasa su bi doka'', a cewarsa.

"BAi kamata ku fice daga fili ba. Duk da cewa hakan bai yi muku daɗi ba, amma ya kamata ku yi biyayya da doka da hukuncin alƙalin wasa, lallai wannan bai dace ba'', in ji shi.

Haka shi ma ɗan wasan Najeriya da ya taɓa lashe gasar a 2013 John Obi Mikel ya ce ya "fahimci damuwar da suke ciki" amma fita ficewa daga fili "ba shi ne masalaha ba".