Yadda Amurka ke ƙara jibge kayan yaƙi a kusa da Iran

- Marubuci, Richard Irvine-Brown
- Marubuci, Alex Murray
- Lokacin karatu: Minti 5
Sashen tantance bayanai na BBC ya tabbatar da cewa an ga wani jirgin ruwan yaƙin Amurka ya nufi Gabas ta Tsakiya, yayin da Washigton ke ci gaba da matsa lamba ga Iran kan shirinta na nukiliya da kuma murkushe masu zanga-zanga a baya bayan-nan.
Jirgin na USS Gerald R Ford, wanda shi ne mafi girma a duniya ya nuna cewa yana tekun Moroko ranar Laraba.
A mintuna 48 da ya bayyana inda yake ga jama'a, an ga jirgin ya nufi tekun Mediterranean
Sai dai ba a ga yana tsallake Mashigar Gibraltar ba zuwa Mediterranean sannan an bibiyi wani jirgin na daban da aka ga yana komawa tekun Atlantika ranar Alhamis.
Jami'an Iran da na Amurka sun haɗu don tattaunawa zagaye na biytu ranar Talata, inda aka ce an ɗan samu cigaba tsakanin masu shiga tsakani a Switzerland.
Shugaba Donald Trump ya faɗa ranar Alhamis cewa duniya za ta "gane cikin kwanaki goma masu zuwa" cewa ko Amurka za ta cimma yarjejeniya da Iran ko kuma za a ɗauki matakin soji.
Ranar Litinin, BBC ta tabbatar da sake ganin wani jirgin ruwa - USS Abraham Lincoln ta hanyar hotunan tauraron ɗan'adam da aka ɗauka ranar Lahadi a tekun Oman, mai nisan kilomita 700 daga Iran.
Isar jirage biyu cikin 11 da sojojin ruwan Amurka ke aiki da su ya ƙara saka alamu kan abin da muka sani na girke dakarun soji a Gabas ta Tsakiya cikin makonni da suka wuce, inda BBC ta ƙara bibiyar wasu jiragen ruwan masu tarwatsa abubuwa, na yaƙi da kuma jirage masu saukar ungulu.
Ma'aikata fiye da 5,000 ne ke aikin kula da jiragen ruwan.

Waɗanne irin kayan yaƙi Amurka ta kai Gabas ta Tsakiya?
Jirgin ruwan USS Gerald ya kunna na'urar da ke iya gane inda yake karon farko a 2026 da misalin karfe 12:30 agogon GMT ranar Laraba.
Jirgin ya bayyana wajen da yake har zuwa karfe 1:18 lokacin da ya nufi tekun Mediterranean.
Sai dai, an bi diddigin wani jirgi haɗe da jirgin ruwan wanda ya sauka a Sifaniya ranar Laraba da misalin karfe 1:00 ranar Alhamis lokacin da ya nufi wani yanki.
Bayyanar jirgin ruwan na Gerald na zuwa ne bayan da sashen tantance bayanai na BBC ya gano jirgin ruwan yaƙi na Abraham Lincoln na a tekun Larabawa, kusan kilomita 240 daga tekun Oman, a wasu hotuna da aka ɗauka ranar Asabar.
Ba a jirgin ruwan ba tun bayan da aka ruwaito cewa ya shiga yankin a watan Janairu, sai dai ya kasance yana tsallake teku inda hotunan tauraron ɗan'adam suka yi ƙaranci.
Ana iya ganin kayayyakin soji a kasa da dama wanda kuma aka sha ɗauka a hotuna.

Sashen tantance bayanai na BBC ya bi diddigin jiragen ruwa 12 a Gabas ta Tsakiya: jirgin ruwan yaƙi na Abraham Lincoln, haɗe da wasu guda biyu masu kai hare-haren makamin linzami masu cin dogon zango da kuma wasu jirage uku waɗanda suka ƙware kan yaƙi a kusa da teku waɗanda aka girke a tashar sojin ruwan Bahrain.
Mun kuma kasance muna bin diddigin kayan soji da dama na Amurka da ake kai wa sansanonin sojin Turai da kuma Gabas ta Tsakiya, sun haɗa da:
- Jiragen yaƙi na F-35 da F-22
- Tankokin ba da mai waɗanda ke taimakawa wasu jirage na KC-135 da KC-46
- Wani jirgin sa ido wanda aka tsara zai jagoranci aikace-aikace na E-3
Ta yaya Iran ta mayar da martani?
A matsayin martani ga girke sojoji da Amurka ke yi, Ita ma Iran ta nuna irin karfin da take da shi.
A ranar Litinin dakarun juyin juya-hali suka ƙaddamar da atisayen soji na ruwa a Mashigar Hormuz wanda ke tsakanin Oman da Iran.
An ga kwamandan dakarun na IRCG Manjo-Janar Mohammed Pakpour na sa ido kan wasu jiragen ruwa kafin a ga gwajin makaman linzami daga cikin wani jirgin ruwa, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Tasnim mai alaƙa da dakarun ya ruwaito.
Mashigar dai tana da muhimmanci wajen fitar da mai a duniya. Kusan kashi biyar na mai da ake fitar wa a duniya na bi ta Mashigar.
Hotunan bidiyo da gidan talabijin na Iran ya watsa ranar Alhamis sun nuna yadda aka yi atisayen sojin a Oman tare da Rasha.

Ta yaya za a kwatanta shirin da samamen Venezuela?
Wani ƙwararre kan aikin soji Justin Crump ya shaida wa BBC cewa shirye-shiryen soji da Amurka ke yi a Gabas ta Tsakiya na "ƙara nuna karfinta da kuma ɗorewa" musamman yanda aka gani gabanin kama shugaban Venezuela Nicolas Maduro a watan Janairu, ko kuma lokacin da aka kai wa Iran hari a watan Yunin bara.
Amurka ta aika jirgin ruwan Gerald zuwa yankin Caribbean gabanin far wa Venezuela, wanda yana ɗaya daga cikin jiragen yaƙi takwas da muka bi diddigi a yankin a lokacin.
Amurkar ta kuma girke jiragen ruwa masu haɗari a yankin na Caribbeam, wanda ake gani a matsayin fage na aikace-aikacen jirage masu saukar ungulu kamar yadda aka gani lokacin cafke Maduro.
Sai dai da ma ana ganin sojin Venezuela ba su da ƙarfin kare kansu daga hare-haren Amurka ko kuma mayar da martani.

Asalin hoton, Reuters
Lokacin da Amurka ta kai wa Iran hari a bara a wani samame mai suna Operation Hammer, wanda aka kai kan cibiyoyin nukiliya, tana far wa ƙasa ce da ke ƙarfin soji fiye da Venezuela.
Iran na da ƙarfin sojin da za ta iya kai hare-hare sansanonin sojin Amurka a faɗin Gabas ta Tsakiya.
Ana ganin abubuwa na faruwa kamar lokacin da Amurka ta far wa Iran. An jibge jirage masu tarwatsa abubuwa biyar a tekun Mediterreanean da kuma na Maliya, da wasu jiragen yaƙi uku a yankin.
An kuma aika jerin jiragen yaƙi masu saukar ungulu da masu ba da mai daga Amurka zuwa Turai.
Sai dai jiragen yaƙi na B2 waɗanda aka yi amfani da su wajen far wa cibiyoyin nukiliya na Fordo, Isfahan da kuma Natanz sun tashi ne daga sansanonin sojin Amurka a Missouri.











