Afghanistan ta gargarɗi Pakistan kan hare-haren da ta kai kan ƴan ƙasarta

Asalin hoton, EPA
Ana ci gaba da nune-nunen yatsa tsakanin Pakistan da Afghanistan bayan da Islamabad ta kai munanan hare-hare ta sama kan maboyar ƴan ta'adda a ƙasar ta Afghanistan.
Pakistan ta ce ta kai hari kan irin waɗannan sansanoni guda bakwai a ranar Asabar ɗin da ta gabata, tana mai cewa mazaunansu sun aikata ta'asa na baya-bayan nan a Pakistan tare da zargin hukumomin Taliban na Afghanistan da ba su mafaka.
Ƙungiyar Taliban a Kabul ta yi alla-wadai da hare-haren.
Ta ce an kashe ko jikkata fararen hula da dama kuma ta sha alwashin mayar da martani.
Cikin makonni da suka gabata an samu ƙaruwar hare-haren ƴan bindiga a Pakistan ciki har da wanda aka kai a wani masallacin ƴan Shi’a a Islamabad, inda aka kashe sama da mutane 30.



