Yadda ƴanbindiga suka kashe gomman masu azumi a Zamfara

Asalin hoton, Getty Images
A ranar Alhamis da yamma ne ƴanbindiga suka kai hari a garin Anka da ke ƙaramar hukumar Anka ta jihar Zamfara, inda suka kashe aƙalla mutum 41, sannan suka yi garkuwa da wasu waɗanda ba a tantance ba.
Harin ya zo ne awanni baya wasu ƴanbindiga da ake zargin ƴan ƙungiyar Lakurawa ne sun kashe aƙalla mutum 35 tare da lalata ƙauyuka bakwai a hare-haren da suka kai a yankin arewa maso yammacin Jihar Kebbi, kamar yadda ƴansanda suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP a ranar Alhamis.
Mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar, Bashir Usman, ya ce ƴan ƙungiyar sun kai farmakin ne a yankin Bui na ƙaramar hukumar Arewa da misalin ƙarfe 1:15 na rana a ranar Laraba.
Usman ya ce adadin waɗanda suka mutu yana da yawa idan aka haɗa da mutanen da suka fito daga ƙauyukan Mamunu da Awasaka da Tungan Tsoho da Makangara da Kanzo da Gorun Naidal da Ɗan Mai Ago domin kare kansu daga harin.
Bayan faruwar lamarin, an tura jami'an tsaro da sojoji tare da 'yan sa-kai zuwa yankin domin daƙile harin da kuma dawo da zaman lafiya.
Harin ya zo ne kwanaki kaɗan bayan gudanar da gagarumin bikin kamun kifi na Argungu a jihar ta Kebbi, wanda ya samu halartar manyan baƙi, ciki har da shugaban Najeriya Bola Tinubu.
Ana dai zargar ƙungiyar Lakurawa da kai hare-hare a yankuna da dama na jihohin Kebbi da Sokoto da ke arewa maso yammacin ƙasar.
Suna kai hare-hare tare da garkuwa da mutane da sace dabbobi, sannan suna saka "haraji" a wasu ƙauyukan.
Gwamnatin Najeriya ta ce hare-haren da gwamnatin Amurka ta ƙaddamar a jihar Sokoto, ta kai ne a kan maharan ƙungiyar.
Ana dai tunanin ƴan ƙungiyar na da alaƙa da ƙungiyar IS, wadda ke da ƙrfi a ƙasashen Nijar da Mali.
Yadda harin ya auku
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wani mazaunin ƙauyen Kanzo na jihar Kebbi ya ce sun ji ƙarar bindiga suna cikin gidajensu, lamarin da ya sa mutane suka riƙa gudu domin neman mafaka, inda harsasai suka samu wasu daga cikinsu.
Ƴansanda sun ƙara da cewa maharan sun kuma kwashe shanu a yayin farmakin.
A nasa bayanin, Lurwanu Marafa Anka Nagambo mai wakiltar Anka da Kewaye a majalisar jihar Zamfara, ya ce ƴanbindigar sun kashe aƙalla mutum 40.
"Ina jajanta wa waɗanda harin ya rutsa da su a daren jiya. Amma tun kafin daren jiya ma, mutanen yammacin ƙaramar hukumata, musamman mazaɓu uku suna fama tashin hankali," in ji shi.
Ya ƙara da cewa yawancin mazauna ƙauyen yawanci a daji suke kwana maimakon gidajensu.
"Mahara sun kai wannan wani harin ne tun misalin ƙarfe 4 a yamma a babura 40 a wani gari da ake kira Dutsen Ɗan Ajiya a Zamfara, inda suka kashe kusan mutum 40, an yanka wasu, an harbe wasu, an kwashe dukiya an kwashe abinci," in ji shi.
Ya ƙara da cewa gwamnati na iya ƙoƙarinta musamman wajen taimakon ma'aikata, inda ya ce ko a kwanakin baya gwamnan ya gayyaci ministan tsaron ƙasar domin ƙaddamar da kayan aiki.
Ya ce maharan sun kashe aƙalla mutum 40, sannan ya ce mutanensa suna fuskantar tashin hankali matuƙa.
A nasa ɓangaren, ɗan majalisa mai wakiltar Bukuyum ta Kudu a majalisar jihar Zamfara Alhaji Hamisu, ya ce da misalin ƙarfe 5:30 na yamma ne aka kira shi, aka faɗa masa ce an hango ƴanbindiga za su shiga garin.
"Ƴanbindiga ne sama da 100 da suka taso daga wani gari da ake kira Dando da ke dajin Bukuyum ta Kudu, sun kai Bakin Kwalta, daidai Gadar Manya da ke ƙarƙashin Anka."
Ya ce ya yi ƙoƙarin kiran jami'an tsaro, "inda na kira sojoji domin jirgi ya kai agaji, kuma muna faɗa musu halin da ake ciki. Har ɓarayin suka isa Bakin Gulbin Barayar Zaki, suka tsallaka Tundar Dutsi suka yi sansani."
Ya ƙara da cewa a lokacin ne jami'an tsaro suka kira shi, suka ce ya bincika domin ba sa so su kai hari kan fararen hula.
"Da na bincika, sai na faɗa musu cewa akwai babura kusan 100, maharan ne kawai, sannan a bayansu akwai maharan suna tafiya a ƙafa tare da mata, sai na faɗa musu cewa duk wanda suka gani a babur, ɓarawo ne. Amma dai ba su kai hari kan ƴanbindigar ba."
Ɗanmajalisar ya ce har zuwa kusan ƙarfe takwas na dare suna yawa da jami'an tsaron, kuma yana magana da mutanen ƙauyen.











