Matakan da za ku bi wajen koya wa yara azumin Ramadan

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Khetam Amer
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Arabic
- Lokacin karatu: Minti 4
Sau da yawa yara kan yi ɗokin fara azumin watan Ramadana, inda sukan so su yi koyi da iyayensu wajen gudanar da ibadar, duk da cewa ba lallai ne su iya jure wa yunwa da kuma ƙishirwar da ke tattare da azumin ba.
Saboda haka, wannan labari ya ƙunshi dabarun da iyaye za su yi amfani da su wajen taimaka wa ƴaƴansu fara azumin Ramadana ba tare da yara sun sha wahala ko cutar da lafiya ko tunaninsu ba.
Yaushe ya kamata yaro ya fara azumi?
Tambayar da iyaye za su iya yi ita ce: yaushe ne ya kamata ɗana/ƴata su fara azumi?
Dakta Lubna Hassan, likitar kula da lafiyar iyali ta amsa wannan tambayar a tattaunawar ta da BBC.
Ta ce "Yana da kyau a fara koya wa yaro azumi, musamman a farkon watan Ramadana.
"Yaro zai iya yin azumi daga asuba zuwa tsakiyar rana a makon farko na watan Ramadana, daga nan sai a riƙa ƙara tsawon a hankali, kamar zuwa lokacin sallar azahar, la'asar, sai kuma zuwa faduwar rana. Za a iya ci gaba a hankali har abin ya bi jikinsu."
Wata likitar yara Dakta Batoul Al-Saifi, ita ma ta yi na'am da wannan batu, inda ta shaida wa BBC cewa "Ya kamata a koya wa yara azumi a hankali. Misali, ɗan shekara 7 zai iya yin azumin awa huɗu, ɗan shekara 8 zai iya yin azumin awa biyar, ya danganta da juriyarsu."
Ta ƙara da cewa: "Babu wata shekara guda ɗaya da za a ce a lokacin ne ya kamata yara su fara koyon azumi, domin fara azumin ya dogara ne da abin da iyaye suka gani daga yaransu na ilimi da kuma lafiyarsu."
Ta yaya za a ƙarfafa wa yara gwiwar yin azumi?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Domin fahimtar dabarun da iyaye ke amfani da su wajen ƙarfafa wa yaransu yin azumi mun tuntuɓi wasu iyaye.
Mamar Muhammad ta yi mana bayani kan dabarun da ta yi amfani da su wajen koya wa yaranta biyar azumi a cikin watan Ramadana.
Zama abin koyi:
Ta ce: "Ina ƙarfafa wa ƴaƴana gwiwa wajen yin azumi ta hanyar zama abin koyi gare su, a matsayina ta uwa. Yara sun fi ɗaukar darasi ta hanyar koyi, saboda haka idan suka ga iyayensu na yin azumi cikin sauƙi da walwala, za su zaƙu su gwada yin azumin, za ka ga yaran sun samu ƙwarin gwiwar kwaikwayon iyayensu."
Ƙara yawan ayyukan ibada a cikin gida:
Ta ƙara da cewa: "Ƙara yawan ayyukan ibada a cikin gida na taka muhimmiyar rawa wajen koya wa yara azumi cikin sauri, kamar ta hanyar sauraron karatun Qur'ani da zikirori, sai kuma sanya su su taimaka wajen ƙawata gida a lokacin da Ramadan ya ƙarato.
"Haka nan ma idan aka ba su damar taimakawa wajen hada abincin buɗe-baki da na sahur. Duk waɗannnan za su taimaka wajen ƙarfafa wa yara gwiwar yin azumi."
Haƙuri da nuna fahimta:
Mamar Muhammad ta ce abubuwa biyu na da matuƙar muhimmanci wajen koya wa yara azumi: wato nuna haƙuri da fahimta.
"A farkon koyon azumi yara za su iya shan wahala, yana da kyau kada a nuna musu kamar sun yi kuskure ne idan suka gaza kai azumi har zuwa faduwar rana. Ya kamata iyaye su faɗa musu cewa wannan na daga cikin matakan koyo da kuma girma, saboda haka ya kamata su taimaka wa ƴaƴan, kada su musu faɗa ko kuma su zama masu tsauri gare su.
"Ramadan wata ne da ke ƙarfafa alaƙar ɗan'adam da ubangijinsa kuma lokaci ne na rungumar kyawawan ɗabi'u kamar haƙuri da juriya da nuna fahimta idan wasu na cikin wahala."
Ɗiyar mamar Muhammad, wato Nada, mai shekara 16 ta ce: "Yin azumi a lokacin yarunta abu ne mai daɗi, abin da na koya ke nan daga iyayena."
Ta ƙara da cewa "Taimakawar da muke yi wajen yi wa gida kwalliya idan azumi ya matso da zaman da muke yi a tare muna jin karatu da tarihin abubuwa na addini sun taimaka mana wajen son yin azumi a kowace shekara, kuma hakan ya sa muna ƙosawa watan ya zagayo."
Yabo da jinjina:
A tattaunawarsa da BBC, Abu Ghazi, mai ƴaƴa uku, ya ce: "Kafin zuwan watan Ramadan nakan fara da shirya tunanin ƴaƴana, nakan riƙa yi musu bayani kan amfani da kuma alfarmar watan, da kuma irin tarin lada da yake ƙunshe da su.
"Haka nan mukan saka su cikin duk shirye-shiryen da muke yi na Ramadan, wanda hakan zai sanya su kansu su ji cewar suna son su yi azumi."
Ya ƙara da cewa: "Mukan yabe su a gaban ƴan'uwa da abokai da kuma baƙi, a duk lokacin da suka yi azumi, ko da kuwa azumin rabin rana kawai suka yi. Haka nan nakan ɗauke su zuwa masallaci domin sallar tarawihi. Duk wadannan abubuwan ne suke sanya su, su yi azumi don ƙashin kansu."
Kuskuren da iyaye ke yi
Masanan da muka tattauna da su sun ce yana da kyau iyaye su kula da wasu kura-kurai da wasu ke yi a ƙoƙarin koya wa yaransu karatu:
- Kada a zargi yaro da yin ƙarya, domin zai iya "amfani da wasu dabaru" ya ci wani abu ko ya sha ruwa a ɓoye. Za a iya fada wa yaro kuskurensa cikin lalama, ba tare da tsangwama ko tsoratarwa ba, domin hakan zai iya shafar ɗabi'unsa.
- Kada a ƙi amsa tambayoyin yaro, domin yaro zai iya yin tambayoyi, kamar me ya sa ake yin azumin Ramadana kuma mene ne amfaninsa da wasu tambayoyi da dama. Saboda haka ya kamata iyaye su amsa wadannan tambayoyi cikin sauƙi ta yadda za su gane.











