Jihohin Najeriya da suka fi yin kasafin kuɗi mai tsoka a 2026

Gwamnonin wasu jihohin Najeriya

Asalin hoton, Social handles

    • Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 5

Yayin da aka shiga wata na biyu a shekarar 2026, tuni gwamnonin jihohin Najeriya suka fara gudanar da wasu daga cikin ayyukan da suka tsara cikin kasafin kuɗin shekarar.

A wanann shekarar jihohin sun ƙara kuɗaɗe masu yawa cikin kasafinsu na shekarar da muke ciki, wani abu da ke nuna yadda jihohin ke samun ƙarin kuɗaɗe daga tarayya.

Jihohi da dama sun kafa hujja da burin gudanar da manyan ayyukan ci gaba wajen ƙara yawan kuɗaɗen da za su kashen a 2026.

Haka ma wasu jihohin sun ce ƙaruwar hauhwar farashin kayyaki da raguwar darajar kuɗin na daga cikin dalilan da suka kasafin kuɗaɗen nasu ya ƙaru.

A wannan shekarar jihohin ƙasar da dama ne suka yi kasafin da ya haura naira tiriliyan ɗaya, kamar yadda wasu bayanai da ƙungiyar BudgIT mai nazari kan kasafin kuɗi a ƙasar suka nuna.

Bisa dogaro da alƙaluman na BudgIT mun zaƙulo jihohin ƙasar 10 da suka yi kasafin kuɗi mai tsoka a 2026

Abia — ₦1.016 trillion

Jihar da ke yankin kudu maso gabashin Najeriya na daga cikin jihohin ƙasar 10 da suka yin kasafin kudi mai gwaɓi a wannan shekarar ta 2026.

Bayanai daga shafin BudgIT mai nazari kan kasafin kuɗaɗe a Najeriya sun nuna cewa jihar ta yi kasafin kuɗin da ya kai naira tiliyan 1.016.

A cewar BudgIT, jihar ta ware naira biliyan 811.8 domin gudanar da manyan ayyuka, yayain da ta ware naira biliyan 204.4 domin gudanar da ayyukan yau da kullum.

A lokacin gabatar da kasafin gwamnan ya ce fannonin ilimi da gina tituna ne za su fi laƙume kuɗaɗe masu yawa.

Bisa ƙiyasin yawan jama'a na 2022, jihar na da yawan al'umma miliyan 4.143.

Niger — ₦1.31 trillion

Gwamna Bago na gabatar da kasafi

Asalin hoton, Facebook

Jihar Neja - wadda ke yankin Arewa ta Tskiyar Najeriya - ta shiga jerin jihohin ƙasar da suka yi kasafi mai gwaɓi a 2026.

Bayanai daga alƙaluman BudgIT na cewa jihar ta yi kasafin kuɗin da ya tasamma naira tiriliyan 1.310.

Jihar ta ware naira biliyan 761.6 domin gudanar da manyan ayyuka, yayin da ta ware naira biliyan 270.3 domin ayyukan yau da kullum.

Neja na da yawan al'umma miliyan 6.78 bisa ƙiyasin yawan jama'ar jihar na 2022.

A lokacin da yake gabatar kasafin kuɗin, gwamnan jihar Mohammed Umar Bago ya ce fannonin noma da ilimi da kuma lafiya ne za a fi bai wa fifiko.

Akwa Ibom — ₦1.390 trillion

Gwamnan Akwa Ibom

Asalin hoton, Akwa Ibom Governor

Jihar Akwa Ibom da ke kudu maso kudancin Najeriya ta kasance cikin jihohin ƙasar masu gwaggwaɓan kasafi a 2026.

Alƙaluman BudgIT sun nuna cewa jihar ta gabatar da kasafin kudin naira tiriliyan 1.390.

Bayan da ƙungiyar ta fitar sun nuna cewa jihar ta ware wa fannin manyan ayyuka naira tiriliyan 1.035, yayin da fannin yau da kulluma ya samu naira biliyan 353.9.

A lokacin sanya hannu kan kasafi, gwamnan jihar, Umo Eno ya ce fannonin gina tituna da ilimi da lafiya za a fi bai wa fifiko.

Imo — ₦1.43 trillion

Jihar Imo ta shiga jerin jihohin ƙasar da suka yi kasafin kudi mai tsoka a 2026.

A cewar alƙaluman BudgIT, jihar ta yi kasafin naira tiriliyan 1.43 a wannan shekarar.

Alƙaluman sun nuna cewa fannin manyan ayyukan zai laƙume naira tiriliyan 1.201, yayain da ayyukan yau da kullum zai laƙume naira biliyan 238.5.

A lokacin sanya hannu kan kasafin kuɗin gwamnan jihar, Hope Uzodimma ya ce kasafin zai fi bayar da fifiko ga fannonin ayyukan more rayuwa da samar da ayyuka da kuma inganta rayuwar al'umma.

Kano — ₦1.47 trillion

Abba Kabir Yusuf

Asalin hoton, Kano State govt

Jihar Kano - da ke yankin arewa maso yammcin ƙasar - jiha ta biyu a arewacin ƙasar bayan Neja da kasafinsu ya haura naiya tiriliyan ɗaya.

Bayanai BudgIT sun nuna cewa jihar ta yi kasafin kuɗin da ya kai naira tiriliyan 1.47.

Fannonin ilimi da abubuwan more rayuwa da lafiya ne kan gaba a kasafin.

Jihar Kano dai na da yawan al'umma kimanin miliyan 15.46, bisa ƙiyasin yawan jama'a na 2022.

Enugu — ₦1.62 trillion

Jihar Enugu ta kasance jiha ta uku cikin jihohin kudu maso gabashin ƙasar da suka yi kasafi mai gwaɓi a 2026.

Bayanai daga alƙaluman BudgIT sun nuna cewa jihar ta yi kasafi na naira tiriliyan 1.62.

Inda ta ware wa manyan ayyukan naira tiriliya 1.300, yayain da ayyukan yau da kullum ya samu naira biliyan 321.

Yayin gabatar da kasain gwamnan jihar, Peter Ndubuisi Mbah ya ce fannonin da kasafin zai fi bai wa fifiko sun haɗa da ilimi da lafiya da ayyukan more rayuwa da fannin sufuri.

Delta — ₦1.664 trillion

Gwamnan delta na gabatar da kasafin kuɗi

Asalin hoton, Delta State Govt.

Jihar Delta mai arzikin man fetur da ke kudu maso kudancin Najeriya na kan gaba wajen yin kasafi mai gwaɓi a 2026.

Alƙaluman BudgIT mai sanya idanu kan harkokin kasafin kuɗi a Najeriya sun nuna cewa jihar ta yi kasafin naira tiriliyan 1.66 a wannan shekara.

A cewar BudgIT jihar ta ware naira tiriliyan 1.165 domin gudanar da manyan ayyuka, yayin da ta ware naira biliyan 499 ga fannin gudanarwar yau da kullum.

Yayin sanya hannu a kan kasafin, gwamnan jihar Sheriff Oborevwori ya ce kasafin ya bayar da fifiko ga fannonin samar da abubuwan more rayuwa da inmganta birane da tattalin arziki.

Ogun — ₦1.668 trillion

Jihar Ogun- wadda ke yankin kudu maso yammcin Najeriya - ce jiha ta takwas cikin jihohin ƙasar 10 da suka fi yin kasafi mai gwaɓi a 2026.

Jihar mai yawan manyan masana'antu a ƙasar ta yi kasafin da ya kai naira tiriliyan 1.66.

Yayin da ta ware wa manyan ayyuka naira tiriliyan 1.044, yayin da fannin gudanarwar yau da kullum ya samu naira biliyan 624.8.

Rivers — ₦1.854 trillion

Jihar Rivers ce jiha ta uku a yankin kudu maso kudancin Najeriya da kasafinta ya haura naira tiriliyan ɗaya.

Rivers - wadda ta fi kowace jiha ɗimbin arzikin man fetur a Najeriya - ta yi kasafin da ya kai naira tiriliyan 1.854.

Fannonin ayyukan more rayuwa da ilimi da lafiya ne manyan ɓangarorin da suka fi samun kuɗaɗe.

Lagos — ₦4.237 trillion

Gwamnna Legas

Asalin hoton, Babajide Sanwo-Olu

Jihar Legas ce ta fi kwoace jiha kasafi mai yawa cikin jihohin Najeriya a 2026.

Legas mai mayan tasoshin ruwa da masana'atu ta ware naira tiriliyan 4.337 a cewar alƙaluman BudgIT.

Jihar ta ware wa fannin manyan ayyukan naira tiriliyan 2.185, yayin fannin gudanarwar yau da kullum ya sam u naira tiriliyan 2.052.

Fannonin da suka fi samun fifiko sun haɗa da inganta rayuwar al'umma da gina abubuwan more rayuwa da kuma inganta tattalin arziki.