Matakai 9 na dokar ta-ɓaci da Tinubu ya ɗauka kan tsaro a Najeriya

Asalin hoton, State House
A ranar Laraba 26 ga watan Nuwamba ne Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro a faɗin ƙasar, inda ya bayar da umarnin a ɗauki matakan gaggawa domin magance matsalolin tsaro da ƙasar ke fuskanta.
Tinubu ya bayar da umarnin ne bayan wasu munanan hare-haren da 'yanbindiga suka kai a faɗin ƙasar, lamarin da ya sa mutane da dama ke kira ga shugaban da ya ɗauki matakin gaggawa.
A cikin kusan mako biyu ne aka yi garkuwa da ɗalibai da masu ibada a faɗin ƙasar, inda aka sace ɗalibai a jihar Kwara da Kebbi da Neja, sannan aka yi garkuwa da wasu mutane a jihohin daban.
Haka kuma rahotanni sun nuna cewa an kashe wani Birgediya Janar Musa Uba, wanda ƴan Boko Haram ɓangaren ISWAP suka kama bayan kwanton ɓauna da suka yi wa tawagarsa, duk da cewa rundunar sojin ƙasar ba ta tabbatar da aukuwar lamarin ba.
A ranar Talata da gabata ne hukumomin Najeriya suka sanar da samun nasarar kuɓutar da ɗaliban sakandare ta mata ta garin Maga da aka sace a makon da ya gabata, sannan wasu daga cikin ɗaliban makarantar St. Mary's sun kuɓuta, yayin da ake dakon sauran ɗaliban, waɗana gwamnan jihar ya ce ana tantama kan adadinsu.
Tun da farko, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tura Ƙaramin Ministan tsaro Bello Matawalle zuwa jihar Kebbi domin jagorantar aikin ceton.
Sai dai Gwamnan Kebbi Nasir Idris ya shaida wa wani taron manema labarai a Birnin Kebbi cewa shugaban ƙasa ne ya ba jami'an tsaro umarnin tabbatar da gano inda yaran suke da kuma amso su, amma ya ce ba a biya kuɗin fansa ba.
Muhimman umarnin da Tinubu ya bayar
A cikin sanarwar da shugaban ya fitar da kansa a shafukansa na sada zumunta, ya ayyana dokar ta-ɓacin ne, sannan ya bayar da wasu matakai da ya ce a ɗauka kan matsalolin tsaron.
Daga cikin muhimman matakan da ya bayar da umarni a ɗauka, akwai:
- Ƴansandan jihohi: Daga cikin muhimman abubuwan da suke cikin sanarwar, akwai batun ƴansanda na jihohi, inda shugaban ya ce majalisar dokoki za su yi gyara a kundin tsarin mulkin ƙasar domin ba jihohin da ke son kafa ƴansanda damar aiwatarwa.
- Ɗaukar ƙarin ƴansanda 20,000: Ya ce a ɗauki sababbin ƴansanda 20,000, ƙari a kan guda 30,000 da ya fara amincewa a ɗauka.
- Amfani da sansanonin NYSC: Tinubu ya ce a yi amfani da sansanonin horar da masu yi wa ƙasa hidima wajen horar da sababbin ƴansandan da za a ɗauka.
- Tsaron gandun daji: Haka kuma shugaban ƙasar ya bayar umarni ga rundunar tsaron farin kaya ta DSS da ta ɗauki ƙarin jami'an tsaron gandun daji domin su shiga dazukan ƙasar su fatattaki ƴanbindiga.
- Ƴansanda masu gadin manyan mutane: Shugaban ya ce ƴansandan da aka cire daga manyan mutane suna buƙatar horo na musamman, don haka ya ce a tsara yadda za a ba su horo na musamman kafin a tura su wajen aiki.
- Tallafi ga dakarun tsaron jihohi: Haka kuma ya bayyana cewa zai yi iya yinsa wajen taimaka wa dakarun jihohi da wasu jihohin suka kafa domin su yi aiki mai kyau.
- Makarantun kwana: Shugaban ya kuma bayar da shawara ga gwamnonin jihohi su duba yiwuwar daina kafa makarantun kwana a ƙauyuka.
- Masallaci da Coci: Haka kuma shugaban ya bayar da shawara ga Masallatai da Coci-coci da su riƙa neman tsaro daga ƴansanda ko sauran jami'an tsaro idan za su gudanar da taruka.
- Kiwo na yawo: Shugaba ya kuma yi kira ga ƙungiyoyin makiyaya da su yi amfani da ma'aikatar kiwo da ya ƙirƙiro ta hanyar daina yawon kiwo, tare da killace dabbobinsu.
Tinubu ya ƙara da cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci yunƙurin haifar da bala'i a ƙasar ba, "waɗanda suke yunƙurin kai mu bango su sani, muna da ƙarfin gwiwar tabbatar da tsaron ƙasarmu da ma tsaron ƴan ƙasar baki ɗaya. Ina kira ga ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri, mu haɗa kai domin magance matsalolin da muke ciki."
Za ta sauya zani?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A game da wannan umarnin na Tinubu, BBC ta tuntunɓi Kabiru Adamu, shugaban kamfanin tsaro na Beacon Security & Intelligence Limited, inda ya ce da wahala a ga sakamako mai kyau.
Ya ce sanarwar ta fi ƙarfi da nuna siyasa, sama da yunƙurin samar da tsaro cikin gaggawa, domin a cewarsa, shugaban bai fayyace abin da yake nufi da dokar ba, ballanta a fahimci abin da yake nufi.
"Maganar gaskiya idan ka duba gundarin sanarwar, abubuwa uku ne masu muhimmanci, kuma a ciki babu wanda za mu gani a cikin ƙanƙanin lokaci kuma saboda girman matsalar, muna so ne mu ga sakamako cikin gaggawa," in ji Kabiru Adamu.
Masanin harkokin tsaron ya ce idan za a ɗauki sababbin ƴansanda guda 20,000, "aƙalla ana buƙatar wata shida, kuma saboda yanayin ƙasar, wataƙila ma a yi sshekara ɗaya. Kuma ka ga lokacin an fara maganar zaɓen 2027. Ke nan akwai tantama."
Ya ce ko maganar jami'an tsaron gandun daji akwai rina a kaba, domin a cewarsa, waɗanda aka horar ba su da yawa, kuma ya ce rundunar tsaron farin kaya ta DSS ma ba ta a gurbi ɗaukar jami'an da yawa.
"Wannan ya sa nake cewa babu wani abu da za a gani a zahiri kan wannan sanarwar ta shugaban ƙasa."
Masanin ya ce maimakon wannan sanarwar, da shugaban ƙasar ya kira taron tsaro na ƙasa ne, sannan ya ce a samu wakilan gwamnonin yankuna da ƙungiyoyin addinai, "domin a samu fahimtar juna."
"Su kansu jami'an tsaron suna buƙatar ƙarin haske, domin sanarwar ba ta fayyace musu komai ba. Idan aka ce dokar ta-ɓaci dole jami'an tsaro na buƙatar ƙarin ƙarfi aiwatar da wasu abubuwa ba tare da tsaiko ba. Misali za su yi aiki a ce sai sun kawo takardar kotu ko wasu abubuwa ba," in ji shi.
Kabiru ya ƙarƙare da cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ne ya ba shugaban ƙasa damar ayyana dokar ta-ɓaci, "sashe 305 sakin layi na 1 da 2 da 3 ne suka nuna cewa shugaban ƙasa zai iya ayyana dokar ta-ɓaci kan tsaro idan ƙasa na fuskantar barazanar yaƙi, amma dole sai majalisa ta amince."










