Yadda aka kuɓutar da ɗaliban Kebbi ba tare da 'biyan kuɗin fansa ba'

Asalin hoton, Mustapha Ibrahim/BBC
A ranar Talata da gabata ne hukumomin Najeriya suka sanar da samun nasarar kuɓutar da ɗaliban sakandare ta mata ta garin Maga da aka sace a makon da ya gabata.
An samu nasarar ceto ɗaliban ne bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin ceto su, inda har ya tura Ƙaramin Ministan tsaro Bello Matawalle zuwa jihar domin jagorantar aikin ceton.
Da yake bayani kan ceto ɗaliban, Gwamnan Kebbi Nasir Idris ya shaida wa wani taron manema labarai a Birnin Kebbi babban birnin jihar cewa shugaban ƙasa ne ya ba jami'an tsaro umarnin tabbatar da gano inda yaran suke da kuma amso su.
"Muna ƙara gode wa Shugaba Ƙasa Bola Tinubu da dukkanin jami'an tsaro da suka bi umarnin shugaban ƙasa wajen ceto waɗannan yara an amso su.''
Sai dai kuɓutar da ɗaliban ya haifar da muhawara mai zafi a tsakanin al'umma, musamman bayan sanar da cewa an ceto su ne ba tare da biyan kuɗin fansa ba, lamarin da ya sa wasu ke tambayar abin da ake nufi da ceto waɗanda aka sace ba tare da biyan kuɗi ba, kuma ba ƙwato su aka yi da ƙarfin bindiga ba.
A ranar Litinin ta makon jiya ce dai ƴanbindiga suka sace ɗaliban su 25 daga sakandiren ƴan mata ta gwamnati da ke garin Maga a ƙaramar hukumar Danko-Wasagu a jihar Kebbi, sannan suka kashe mutum biyu a makarantar.
'Ba a biya kuɗi ba'
Yayin jawabinsa a taron manema labaran, Gwamna Idris ya ce a iya saninsa babu ko kobo da gwamnatinsa ta biya domin ceto ɗaliban.
''Bayanan da aka ba mu shi ne ba a biya kuɗin fansa ba kafin a sake su. Mu dai gwamnatin jihar Kebbi ba mu bayar da ko kwabo ba. Saboda haka su waɗannan jami'an tsaro sun tabbatar mana su ma ba da kuɗi suka je karɓo yaran nan ba,'' in ji gwamnan.
Shi ma ƙaramin ministan tsaro a Najeriya ya tabbatar da ceto ɗaliban makarantar na Maga, inda ya ce sun ceto su lafiya ƙalau.
"Mun yi aikin ne bisa umarnin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu na a tabbatar da ceto ɗaliban. Ina yaba wa jami'an tsaronmu da jami'an tattara bayanan sirrinmu bisa aiki da ƙwarewar da suka nuna."
Ana cikin jimamin aukuwar wannan ne sai aka samu labarin sace wasu ɗalibai sama da 265 daga makarantar St. Mary da ke jihar Neja, da kuma jerin wasu sace-sacen mutane da dama a jihohin Kwara da da kuma Kano a baya-bayan nan.
'Biri ya yi kama da mutum'
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Domin sanin me ake nufi da ceto waɗanda aka yi garkuwa da su ba tare da biyan kuɗin fasa ba, mun tuntuɓi Dr Kabiru Adamu, shugaban kamfanin Beacon Consulting Limited da ke nazari kan matsalolin tsaro, inda ya ce akwai hanyoyi da dama.
A cewarsa, idan aka ce 'non-kinetic approach' da ake magana, "wasu hanyoyi ne ko dabarun yaƙi ba tare da amfani da ƙarfi ba."
Masanin ya ce daga cikin dabarun akwai:
- Yaɗa labarai: "Amfani da fasaha ko dabara wajen yaɗa labarai ta yadda za ka karya gwiwar abokin yaƙin, ya zama ya tsorata tun kafin ma a fara yaƙin."
- Taimakon al'umma: "Amfani da hanyoyin taimakon jama'a domin sassauta musu zuciya, su rungumi fahimtarka ko abin da kake so su gane. Misali, idan matsalarsu lafiya ce a gina musu asibiti, idan kasuwa ce a gina musu, da ma sauran ababen more rayuwa da suke buƙata."
Sai dai Kabiru Adamu ya ce duk da Najeriya ma tana amfani da dabarun, sukan yi amfani da masu shiga tsakani domin ceto waɗanda aka yi garkuwa da su.
"Duk da cewa babu tabbas, amma lallai akwai magana mai ƙarfi cewa akan yi amfani da kuɗaɗe wajen ceto mutane.
"Zai yi wahalar gaske a iya gane an yi amfani da kuɗi, amma dai biri ya yi kama da mutum: saboda idan ta ƙarfi aka ƙato su to dole za a yi harbe-harbe, kuma dole a samu waɗanda aƙalla suka ji rauni ko mutuwa. Amma duk lokacin da aka yi irin wannan ba a samun haka. Na biyu kuma, ba a samun labarin an kama waɗanda suka yi laifi."
Biyan kuɗin fansa a Najeriya
Game da me ya sa gwamnati ba za ta iya fitowa ta bayyana ko ta biya kuɗin fansa ba, masanin tsaron ya ce abu ne mai wahalar gaske.
"Akwai matsayar gwamnati a hukumance. Ko a watan Afrilu na 2024 Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya wallafa a wata mujallar ƙasa da ƙasa yana jaddada matsayar gwamnatinsa ta ƙin biyan kuɗin fansa, inda ya nuna abin da aka yi a Chibok da Ƙanƙara cewa ya shafi martabar ƙasar," in ji Kabiru Adamu.
Sai dai masanin harkokin tsaron ya ce duk da cewa biyan matsala ne, abin da zai biyo bayan biyan ya fi muhimmanci.
"Babu gwamnatin da za ta fito ta bayyana cewa ta biya kuɗin fansa domin karɓo ƴan ƙasarta, amma abin da ya fi muhimmanci shi ne a hana sace mutanen. Amma idan an riga an sace ko dai a ƙwato su da ka ƙarfi ko a biya," in ji shi.
Ya ƙara da cewa ya kamata gwamnati ta lalubo abubuwan da za a yi bayan biyan domin kare sake aukuwar lamarin.











