Me ya rage wa manyan mutane bayan janye musu ƴansanda?

Jami'an ƴansanda

Asalin hoton, Nigeria Police

Lokacin karatu: Minti 3

Tun bayan da umarnin da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bai wa babban sifeton ƴansandan ƙasar na janye duka jami'an ƴansandan da ke tsaron manyan ƴansiyasar ƙasar (VIPs), ake ta muhawara kan batun.

Yayin da wasu ke son barka da matakin, wasu kallonsa a matsayin barazana da manyan ƴansiyar, musamman a daidai lokacin da ƙasar ke fuskantar barazanar tsaro.

A ranar Lahadi ne shugaban ƙasar Bola Tinubu ya bayar da umarnin a lokacin wani zama na musamman da manyan jami'an tsaron ƙasar a fadarsa da ke Abuja.

Tinubu ya ce ya ɗauki matakin ne domin jami'an ƴansanda su tafi domin gudanar da muhimmanin aikin da ake ɗauke su yi, wato tsaron rayukan ƴan ƙasar.

Matakin na zuwa ne bayan da ƴanbindiga suka sace ɗalibai a makarantun jihohin Kebbi da Neja cikin makon da ya gabata.

Se wane ne VIPs?

Dokta Kabiru Adamu, Shugaban kamfanin Beacon Security mai nazarin al'amuran tsaro a yankin Sahel ya ce abin da ake nufi da VIPs, wato manyan mutane su ne masu riƙe da muƙaman gwamnati.

''Sun ƙunshi mutanen da aka zaɓa ko aka naɗa a matsayin muƙaman gwamnati'', in ji shi.

Sun haɗa tun daga kan shugaban ƙasa, zuwa mataimakinsa da gwamnoni da mataimakansu da shugaban majalisar dattawa da kakakin majalaisar wakilai.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

''Haka ma sun haɗa da duka ƴan majalisar dokoki da ministoci, da sauran masu riƙe da muƙaman gwamnati'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Kodayake ya ce akwai wasu daga cikinsu kamar shugaban ƙasa da ke samun kariyar sojoji.

Dokta Kabiru Adamu ya ce a ƙa'ida waɗannan su ne kawai mutanen da ya kamata ƴansanda su bai wa tsaro.

Sai dai ya ce amma a yanzu abin na neman taɓarɓarewa , inda ƴan kasuwa ko masu kuɗi ke samun jami'an ƴansanda a matsayin masu ba su kariya.

''Abin ya kai har da iyalan irin waɗannan mutane ana tura musu ƴansanda domin ba su kariya'', in ji masanin al'amuran tsaron a Najeriya.

Akwai mawaƙa da dama da manyan taurarin fina-finai a ƙasar da ke samun rakiyar ko kariyar ƴansandan.

To sai dai Kabiru Adamu ya ce kai-tsaye doka ba ta ba su damar samun kariyar ƴansanda ba.

To amma masanin tsaron ya ce akwai hurumin dokar ƙasa da ta bai wa kowa damar idan yana fuskantar wata barazana, ya rubuta wa rundunar ƴansanda domin sanar da ita, tare da neman jami'ai domin ba shi kariya.

Me doka ta ce kan bai wa VIPs kariya?

Dokta Kabiru Adamu ya ce a cikin tanade-tanaden aikin ƴansanda akwai mutanen da saboda muƙamansu suna buƙatar a ba su kariyar.

''Haka ma a ƙarƙashin tsarin dokar ƙasa, akwai mutanen da doka ta bai wa ƴansanda damar ba su kariya, saboda muƙaman da suke riƙewa'', in ji shi.

''Alal misali akwai muƙaman ADC da CSO da ake bai wa mau riƙe da muƙamai, kamar gwamnoni da duka waɗannan jami'an ƴansanda ne'', in ji Dokta Kabiru Adamu.

Wane zaɓi ya rage musu?

Cikin sanarwar da Shugaba Tinubu ya fitar ya buƙaci manyan mutane su koma rundunar samar da tsaro ta fararen hula, wato sibil difense domin samun jami'an da za su ba su kariya.

Sibil Difense hukuma ce da ke ɗaukar jami'ai tare da ba su cikakken horon samar da tsaro, musamman a cikin gida.

Jami'an hukumar na da kayan aiki da suka haɗa da makamai da motoci, sannan suna da kayan sarki, kamar dai sauran jami'an tsaron ƙasar.

Jami'ai

Asalin hoton, Social Media

Jami'an sibel defense za su iya kare VIPs?

Dokta Kabiru Adamu ya ce jami'an wannan hukuma za su iya bayar da kariya ga fararen hular da ake buƙata, la'akari da yanayin aikinsu na bayar da kariya da muhimman wurare a cikin ƙasar.

''Ai dama tun a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe, Shugaba Tinubu ya ɗauki alƙawarin bai wa rundunar sibel difense hurumin bayar da kariya ga manyan mutane a ƙasar'', in ji shi.

Ya kuma ce sau biyu Tinubu yana bayar da umarnin bayan karɓar ragamar mulki, amma sai matakin ya riƙa samun tangarɗa daga waɗanda Dokta Kabiru Adamu ke ganin su ake bai wa kariyar.