Yadda ƴanbindiga suka sace ɗalibai mata a Kebbi

Asalin hoton, Mustapha Ibrahim/BBC
Hukumomi a jihar Kebbi, arewa maso yammacin Najeriya sun tabbatar da harin da wasu ƴan bindiga suka kai a Makarantar Sakandiren Ƴanmata da ke garin Maga, inda suka kashe aƙalla ma'aikaci ɗaya da sace ɗalibai.
Lamarin ya faru ne da asubahin Litinin lokacin da ɗaliban ke shirin tashi sallar asuba.
Bayanai sun ce maharan sun far wa makarantar ɗauke da muggan makamai inda suka yi ta harbi kafin daga bisani su tafi da ɗalibai, waɗanda ba a riga an tantance adadinsu ba.
Wannan ne hari na baya-baya da irin waɗannan ƴan bindiga suka riƙa kaiwa a makarantu suna sace ɗalibai a jihohi daban-daban na ƙasar, musamman yankin arewacin ƙasar mai fama da ayyukan ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai.
Makarantar kwanan ta ƴanmata na a garin Maga a yankin ƙaramar hukumar Danko/Wasagu a jihar.
Yadda abin ya faru

Asalin hoton, Getty Images
Ɗaya daga cikin malaman makarantar da ya zanta da BBC ya kuma buƙaci a sakaya sunansa ya ce maharan sun kashe malami guda da maigadin makarantar a lokacin harin.
Malamin ya ce maharan sun far wa makarantar a lokacin da ɗaliban tsaka da barci.
''Sun shigo makarantar ne daga yamma, riƙe da muggan makamai, inda suka yi awon gaba da ɗalibai masu yawa'', kamar yadda ya bayyana.
''Kawo yanzu muna nan muna tantance yawan ɗaliban da suka sace, saboda a lokacin da suka kawo harin ɗalibai da dama sun ɗimauce, lamarin da ya sa suka warwatsu, sai da safen nan ne suke dawowa'', kamar yadda malamin ya shaida wa BBC.
Shugaban Ƙaramar hukumar Danko/Wasagu, Hon. Hussaini Aliyu Bena ya ce maharan sun je makarantar ne a ƙafa ba a kan babura ba, kamar yadda suka saba kai hare-hare a yankunan.
Ya kuma danganta harin da yadda wasu al'umomin Zamfara da suka yi iyaka da ƙaramar hukumar suka yi sulhu da ƴanbindiga.
Sai dai ya ce a bayanin da suka samu babu labarin rasa rai, sai dai ya ce maharan sun harbe mai gadin makarantar, wanda yanzu a cewarsa ke asibiti ana yi masa magani.
Aliyu Bena ya ce kawo yanzu an tura jami'an tsaro zuwa makarantar da keyawenta domin kwantar wa jama'a hankula tare da shirye-shiryen ceto ɗaliban da ke hannun maharan.

Asalin hoton, Mustapha Ibrahim/BBC
'Ɗalibai 25 aka sace'
Sai dai wasu majiyoyin jami'an tsaro sun tabbatar da sace ɗalibai 25 a lokacin harin.
A baya-bayan nan jihar Kebbi ta shiga jerin jihohin Najeriya masu fama da matsalar hare-haren ƴanbindiga.
Sace ɗalibai a makarantu ba baƙon al'amari ba ne a Najeriya.
A watan Yunin 2021, ƴan bindiga sun sace ɗalibai aƙalla 50 a Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke birnin Yauri, a jihar ta Kebbi.
A shekarar 2014 ne dai mayaƙan Boko Haram suka fara ƙaddamar da hari kan makarantar sakandiren ƴanmata da ke Chibok a jihar Borno, inda suka sace ɗaruruwan ɗalibai.
Daga lokacin ne kuma ƴanbindiga masu satar mutane suka riƙa ƙaddamar da hare-haren kan makarantu tare da sace ɗalibai.
Jami'an tsaro sun bazama
Rundunar ƴansandan Najeriya a jihar Kebbi ta bayyana cewa an tura dakaru na musamman, wadanda suka hada da ƴansanda da sojoji da kuma ƴan bijilante domin nemo ƴan makarantar da aka sace.
Mai magana da yawun rundunar ƴansanda a jihar ta Kebbi, Nafiu Abubakar Kotarkoshi ya sake tabbatar da cewa maharan sun shiga makarantar ne da kimanin ƙarfe hudu na asuba a ranar Litinin.
Ya ce ƴansandan da ke makarantar sun yi musayar wuta da ƴan fashin dajin, sai dai duk da haka sun samu nasarar kwashe wasu daga cikin ɗaliban suka tsallaka ta katanga.
Sai dai bayan kai harin, rundunar ƴansandan ta sake tura ƙarin jami'anta zuwa makarantar.
Hare-hare kan makarantu a Najeriya
- Sakandiren mata ta Chibok
A ranar 14 ga watan Afrilun 2014 ne mayaƙan Boko Haram suka kai wani hari makarantar sakandaren mata da ke Chibok a jihar Borno, inda suka sace ɗalibai masu yawa.
Mayaƙan ɗauke da manyan bindigoyi sun shiga garin da tsakar dare suka tashi mazauna da ƙarar harbi kafin su kutsa cikin ɗakunan kwanan ɗalibai suka loda su a motoci sannan suka yi awon gaba da ƴanmata 276.
- Sakandiren mata ta Dapchi
A watan Fabrairun 2018 ne wasu da ake zargi mayaƙan Boko Haram ne kuma suka kai hari makarantar mata da ke garin Dapchi na jihar Yobe sannan suka sace ɗalibai 110.
Lamarin ya faru ne kusan shekara huɗu bayan sace ƴanmatan makarantar Chibok.
- Sakandiren Kankara
A watan Disamban 2020 ne wasu ƴan bindiga suka kai hari makarantar sakandaren kimiyya ta maza da ke garin Kankara na jihar Katsina da ke arewacin Najeriya.
Ƴan bindigar sun sace ɗalibai fiye da 300 inda suka yi doguwar tafiya da su zuwa wasu dazuka da ke jihar Zamfara wadda ita ma ke fama da matsalar rashin tsaro.
- Makarantar mata ta Jangebe
A cikin watan Fabrairun 2021 ma ƴan bindiga sun kai hari makarantar kwana ta mata da ke garin Jangeɓe a jihar Zamfara wato GGSS Jangebe, inda suka sace kimanin ɗalibai 317.
Wani shaida a lokacin ya tabbatar wa BBC cewa an sace 'yan mata kusan 300 ne sakamakon kirga dukkan 'yan makarantar da suka rage bayan ɓarayin sun tafi.
- Makarantar Kuriga
A farkon watan Maris ɗin 2023 ne wasu ƴan bindiga suka yi wa makarantar firamare da ƙaramar sakandiren Kuriga - da ke yankin ƙaramar hukumar Chikun a jihar Kaduna - ƙawanya tare da awon-gaba da wasu ɗalibai kimanin 287 da malaminsu guda ɗaya, kodayake shi malamin ya samu kuɓuta.
A lokacin da gwamnan jihar Uba Sani ya kai ziyara garin, malamin da ya kuɓutar ya shaida masa cewa, maharan sun zo makarantar ne daidai lokacin da aka kammala taron ɗalibai wato (Assemly).










