Bidiyon yadda Iran ta kai hari sansanin sojin Amurka da ke Bahrain
Bidiyoyin harin ramuwar gayyar Iran a yankin Gabas ta Tsakiya na ci gaba da ɓulla.
Akwai sansanonin sojin amurka masu yawa a yankin gabas ta Tsakiya, da za a iya kai wa hari.
Bahrain na ɗaya daga ƙasashen yankin Gulf da dama da Iran ta kai wa hari bayan hare-haren amurka da Isra'ila a ƙasarta.
Iran ta kai hari babban sansanin sojin ruwan Amurka da ke ƙasar ta Bahrain.









