Wane ne Ayatollah Ali Khamenei, jagoran addini na ƙasar Iran?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, BBC News Persian
- Lokacin karatu: Minti 5
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya ƙi amincewa da yunƙurin Isra'ila na kashe jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei a yaƙin da take yi da Iran, lamarin da kafofin watsa labaran Amurka suka ruwaito yana cewa "bai dace ba."
Bayan burin da Isra'ila ke da shi na tarwatsa abin da take kira babbar barazanar da shirin Iran na mallakar makamin nukiliya ke yi ga ƙasarta a matsayin dalilin hare-haren na yanzu, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyanhu, ya ce kawo sauyin gwamnati a Iran ma na cikin burinsu.
Netanyahu ya sha faɗa a baya cewa akwai buƙatar ƴan ƙasar su tashi tsaye wajen ƙwatar ƴancinsu daga jagoran.
A wannan maƙalar, za mu yi nazarin wane ne jagoran addinin, da irin ƙarfin ikonsa a ƙasar, da kuma rawar da iyalansa suke takawa a siyasar ƙasar.

Asalin hoton, EPA-EFE/Shutterstock
Ayatollah Ali Khamenei shi ne jagoran addini na Iran na biyu bayan juyin-juya halin ƙasar da aka yi a shekarar 1979, kuma tun a shekarar 1989 yake riƙe da muƙamin.
Matasan ƙasar yawanci sun taso ne suna ganin sa a matsayin jagoran addininsu.
Yana riƙe ne da madafun iko mai ƙarfin gaske - yana da ikon hawa kujerar na-ƙi a kan duk wani matakin ƙasar, sannan yana da ikon zaɓa ko naɗa wanda yake so a wata kujerar mulkin ƙasar.
Shi ne jagoran askarawan ƙasar, ciki har da dakarun juyin juya-halin ƙasar wato Iranian Revolutionary Guard Corps (IRGC).

Asalin hoton, Anadolu/Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
An haife shi ne a garin Mashhad, birni na biyu mafi girma a Iran a shekarar 1939.
Shi ne na biyu a wurin mahaifansa masu ƴaƴa takwas, kuma mahaifinsa ya kasance malamin Shi'a.
Ya fara karatu ne da koyon karatun Ƙur'ani tun yana ƙarami, inda ya zama malami yana da shekara 11.
Duk da cewa yana daga cikin masu bayar da fatawa kan al'amura, a yanzu haka za a iya cewa aikinsa ya fi tasiri a siyasance.
Khamenei mutum ne da Allah ya yi wa baiwar iya tsara magana sosai, kuma ya kasance kan gaba wajen sukar gwamnatin Shah ta Iran, sarkin da aka hamɓarar a juyin juya-halin ƙasar.
Yawancin rayuwar Khamenei ta kasance a ƙarƙashin ƙasa ne ko a gidan yari. Sau shida ana kama shi a zamanin mulkin Shah, inda ya fuskanci uƙuba.
Shekara ɗaya bayan juyin juya-hali a 1979, sai Ayatollah Ruhollah Khomeini ya naɗa shi babban limamin Juma'a na birnin Tehran.
Daga baya sai aka zaɓe shi a matayin shugaban ƙasa a 1981, kafin shugabannin addinin ƙasar suka zaɓe shi a shekarar 1989 domin ya maye gurbin Ayatollah Khomeini, wanda ya rasu yana da shekara 86.
Yaya ƙarfin ikon ɗansa Mojtaba?
Ali Khamenei bai cika fita ƙasashen waje ba - yana gudanar da ƙaramar rayuwa ne a tsakiyar Tehran tare da maiɗakinsa.
An ce yana son rubutacciyar waƙa da lambu. Khamenei ya samu matsala a hannunsa na dama a wani yunƙurin kashe shi da ya tsallake a shekarun 1980s.
Shi da maiɗakinsa, Mansoureh Khojasteh Baqerzadeh suna da yara shida - maza huɗu da mata biyu.
Ba kasafai ake ganin iyalan Khamenei ba, kuma babu takamaimen bayani game da rayuwarsu.
A cikin yaransa, akwai Mojtaba, wanda shi ne na biyu, wanda ya fi fice, kuma ya fi taka rawar gani a harkokin jagoran.

Asalin hoton, NurPhoto/Getty Images
Mojtaba ya yi karatu ne a makarantar Alavi High School a Tehran, wadda makaranta ce ta ƴaƴan manya.
Tun kafin ya fara karatu a fitacciyar makarantar Shi'a ta Qom ya auri ƴar gidan Gholam-Ali Haddad-Adel - wanda shi ma fitaccen ɗan ra'ayin riƙau ne - lokacin yana da shekara 30.
A tsakankanin shekarun 2000 ne Mojtaba ya fara fitowa fili, duk da cewa ba a cika jin sunansa a kafofin sadarwa ba.
Sunan Mojtaba ya ƙara amo ne bayan zaɓen 2004 da ya tayar da ƙura, lokacin da Mehdi Karroubi - fitaccen ɗantakara a zaɓen ya zarge shi da hannu wajen maguɗi domin samun nasarar Mahmoud Ahmadinejad, a wata wasiƙa da ya rubuta zuwa Ayatollah Khamenei.
A tsakankanin 2010 ƙarfinsa ya fara faɗaɗa, inda aka fara masa kallon ɗaya daga cikin masu ƙarfin faɗa a ji a ƙasar.
Da dama daga cikin ƴan ƙasar na kyautata zaton Mojtaba ne zai gaji mahaifin nasa a matsayin jagoran addini a ƙasar. Amma wasu majiyoyi sun musanta hakan a hukumance.
Duk da Ali Khamenei ba sarki ba ne, kuma ba zai iya gadar da mulkinsa ba, Mojtaba yana da farin jini a tsakanin mutanen jagorarn masu ra'ayin riƙau, ciki har da ofishin jagoran addinin ƙasar.
Yayan Mojtaba wato Mustafa Khamenei shi ne babban ɗan jagoran addinnin. Matarsa ƴar Azizollah Khoshvaght ce, wanda shi ma fitaccen malamin Shi'a ne a ƙasar.
Mustafa da Mojtaba duk sun shiga cikin dakarun da suka fafata a yaƙin Iran da Iraq a shekarun 1980.

Asalin hoton, AFP/Getty Images
Ɗan Ali Khamenei na uku shi ne Masoud, wanda aka haifa a shekarar 1972. Yana auren Susan Kharazi, ƴar fitaccen malamin Shi'a Mohsen Kharazi, kuma ƴaruwar tsohuwar jakadiyar ƙasar, Mohammad Sadegh Kharazi.
Masoud Khamenei bai cika shiga cikin harkokin siyasa ba.
Ya taɓa aiki a ofishin da ke kula da ayyukan mahaifinsa, inda ya jagoranci harkokin watsa labarai da farfaganda. Shi ne kuma yake jagorantar rubuta littafin tarihin mahaifin nasa.
Ɗan ƙaraminsu, Meyasam an haife shi ne a 1977, kuma shi ma malamin addini ne kamar sauran.
Matarsa - wadda ba a san sunanta ba a hukumance - ƴa ce ga Mahmoud Lolachian, wanda fitaccen attajiri ne wanda yake amfani da dukiyarsa wajen taimakon addini da malaman ƙasar.
Ƴaƴansa mata biyu
Babu bayanai sosai game da ƴaƴansa mata biyu.
Bushra da Hoda ne ƙanana a cikin yaran, kuma duk an haife su ne bayan juyin juya-hali na 1979.
An haifa Bushra a 1980 kuma tana auren Mohammad-Javad Mohammadi Golpayegani, ɗan Gholamhossein (Mohammad) Mohammadi Golpayegani, wanda shi ne shugaban ma'aikatan ofishin Khamenei.
Hoda, wadda ita ce autar gidan baki ɗaya an haife ta ne a 1981. Tana auren Mesbah al-Hoda Bagheri Kani, wanda ya karanci kasuwanci kuma yake koyarwa a Jami'ar Imam Sadiq University.
Tacewa: Alexandra Fouché












