Abubuwa biyar da za su iya faruwa sanadiyyar yaƙin Isra’ila da Iran

People look at a damaged building in the aftermath of Israeli strikes, in Tehran, Iran.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, An kwashe daren Asabar ana musayar wuta ta sama tsakanin Iran da Isra’ila
    • Marubuci, James Landale
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Diplomatic correspondent
  • Lokacin karatu: Minti 5

A halin yanzu rikicin da ya ɓarke tsakanin Isra’ila da Iran ya takaita ne ga kasashen biyu. Majalisar Dinkin Duniya da sauran kasashe na ta kira kan cewa a yi taka-tsantsan.

To amma me zai faru idan kasashen biyu suka ki jin shawarar yin taka-tsantsan? Haka nan me zai faru idan yakin ya bazu kuma ya fadada?

Ga wasu munanan abubuwa da za su iya faruwa game da yakin.

Shigar Amurka

Duk da ikirarin Amurka na cewa ba ta da hannu a yakin, Iran ta yi amannar cewa da amincewar Amurka aka kai harin kuma akalla ta taimaka wa Isra’ila da shawarwari.

Iran za ta iya kai farmakai kan cibiyoyin Amurka a fadin Gabas ta Tsakiya - kamar sansanin sojojin Amurka na musamman da ke Iraqi, da sansanonin sojin Amurka a kasashen yankin Gulf da kuma ofisoshin jakadancinta.

Duk da cewa an raunana kungiyoyi masu goyon bayan Iran a yankin, kamar Hamas da Hezbollah, amma kungiyoyin da ke mara mata baya a Iraq na nan da karfinsu.

Amurka ta yi fargabar cewa za a iya kai mata wadannan hare-hare shi ya sa ta kwashe jami’anta. A bayanin da ta fitar, Amurka ta gargadi Iran kan abin da zai biyo baya idan hakan ta faru.

Me zai faru idan aka kashe wani ba’amurke a birnin Tel Aviv ko wani yanki sanadiyyar yakin?

Hakan zai iya tilasta wa Donald Trump ya dauki mataki. An dade an zargin Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da kokarin janyo Amurka domin ta taimaka masa ya murkushe Iran.

Masana ayyukan soji sun ce Amurka ce kadai ke da bama-baman da za su iya fasa cibiyoyin nukiliyar Iran da ke can cikin karkashin kasa, musamman ta Fordow.

Trump ya yi wa magoya bayansa alkawarin cewa ba zai taba fara irin yakunan da ke dadewa ana yi ba a Gabas ta Tsakiya. Amma dimbin magoya bayan jam’iyyar Republican ta Donald Trump na goyon bayan gwamnatin Isra’ila da kuma ra’ayinta na cewa yanzu ne lokacin da ya kamata ta tabbatar an samu sauyin shugabanci a Iran.

To amma idan Amurka ta shiga cikin yakin tsundum, hakan na nufin lamarin zai yi matukar rincabewa ta hanyar tsawaita yakin da kuma ta’azzara barnar da zai haifar.

Shigar kasashen yankin Gulf

Idan Iran ta gaza lalata cibiyoyin sojin Isra’ila wadanda ke da matukar tsaro, za ta iya juya akalar yakin kan wasu kasashen yankin Gulf wadanda ta dade tana zargin su da goyon bayan makiyanta.

Akwai wurare da dama da za ta iya far mawa a yankin. An taba zargin Iran da kai hari kan filayen hakar man fetur na Saudiyya a 2019 sannan mayakan Houthi suka kai wasu hare-haren a cikin Hadaddiyar Daular Larabawa a shekarar 2022.

Tun daga wancan lokacin an dan samu fahimtar juna tsakanin Iran din da wasu kasashen yankin.

To sai dai wadannan kasashen na kunshe da wasu sansanonin sojin sama na Amurka. Haka wasu daga cikinsu sun taimaka a asirce wajen kare Isra’ila daga hare-haren makamai masu linzami ma Iran a shekarar da ta gabata.

Saboda haka idan Iran ta kai hari kan wasu kasashen Gulf, akwai bukatar jiragen yakin Amurka su shiga ciki domin kare kasashen da kuma Isra’ila.

A demonstrator holds an anti-war sign during a protest against Israeli strikes on Iran

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wani mai zanga-zanga rike da allon da ke dauke da sakon adawa da hare-haren Isra’ila kan Iran a birnin New York na Amurka

Idan Isra’ila ta gaza lalata shirin nukiliyar Iran

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Idan hare-haren Isra’ila suka gaza fa? Idan cibiyoyin nukiliyar Iran suna can cikin karkashin kasa ne kuma suna da kariya mai inganci ne?

Me zai faru idan yawan tataccen makamashin uranium din Iran ya kai kashi 60% na inganci kuma yawansa ya kai kilogiram 400 - wanda kiris ke nan ya rage ya kai na hada makami, wanda zai iya hada bama-bamai 10 - aka gaza lalata shi?

Ana tunanin cewa yana iya yiwuwa suna can karkashin kasa ne a boye.

Isra’ila ta kashe wasu masana ilimin nukiliya na Iran amma babu yadda za a yi ta lalata kwarewar da Iran ke da ita.

Me zai faru idan hare-haren Isra’ila kan Iran suka sanya shugabannin Iran suka yi tunanin cewa hanya daya tilo ta kare yiwuwar hakan a gaba ita ce hanzarta mallakar makamin nukiliya?

Ko kuma kila sabbin shugabannin sojin Iran sun fi wadanda aka kashe taurin kai da rashin tsantseni?

Abin da zai iya faruwa shi ne hakan zai tursasa wa Isra’ila ci gaba da kai hare-hare, lamarin da zai sanya a yi ta ba-ta-kashi ta hanyar kai wa juna hare-hare a fadin yankin. Isra’ila na da wani shiri game da hakan, wanda ta yi wa lakabi da “mowing the grass” a turance, wato yin saisaye.

Durkushewar tattalin arzikin duniya

A yanzu haka faraahin man fetur ya tashi.

Idan Iran ta rufe mashigin Hormuz lamarin zai kara takaita safarar man fetur.

Haka nan me zai faru idan a daya bangaren yankin Larabawa - mayakan Houthi a Yemen suka nunka hare-harensu kan jiragen da ke ratsawa ta Maliya?

Su ne na karshe a cikin kungiyoyi masu goyon bayan Iran da ke da tarihin daukar kasada ba tare da la’akari da abin da zai iya zuwa ya dawo ba.

Yanzu haka kasashen duniya da dama na fama da tsadar rayuwa. Tashin farashin man fetur zai iza wutar tashin farashin kayan masarufi baya ga rudanin da tattalin arzikin duniya ke ciki sanadiyyar haraje-harajen da Trump ya lafta wa kasashen duniya.

Kuma kada a manta, mutum daya wanda ke cin gajiyar tashin farashin man fetur a duniya shi ne shugaba Vladimir Putin na Rasha, wanda zai samu karin biliyoyin daloli na kudaden shiga cikin kankanin lokaci, wanda kuma zai yi amfani da su wajen yakinsa a Ukraine.

Faduwar gwamnatin Iran

Me zai faru idan Isra’ila ta cimma burinta na tale-tale, wato karya mulkin ‘yan juyin juya halin Musulunci na Iran?

Netanyahu ya yi ikirarin cewa manufarsa ita ce lalata shirin nukiliyar Iran. Amma a cikin jawabinsa na ranar Juma’a ya fada karara cewa daya daga cikin manyan manufofinsa shi ne sauya gwamnati a Iran.

Ya shaida wa “mutanen Iran” cewa manufar hare-haren shi ne “share muku hanyar samun ‘yancin kanku” daga abin da ya kira “muguwar gwamnatin danniya”.

Kawar da gwamnatin Iran abu ne da zai yi wa wasu dadi a yankin, musamman Isra’ilawa. To amma gibin da za a bari fa? Wadanne munanan abubuwa ne za su biyo baya? Idan aka samu barkewar rikici a Iran ya abin zai kasance?

Mutane da dama za su iya tuna halin da Iraqi da Libya suka fada bayan kawar da gwamnatocinsu.

Abubuwa da dama sun dogara ne kan yadda yakin zai kasance a ‘yan kwanaki masu zuwa.

Ta yaya Iran za ta rama kuma wane irin karfi za ta yi amfani da shi?

Sannan wane irin kwaba Amurka za ta yi wa Isra’ila?

Wadannan ne za su tantance abin da zai biyo baya.