Ta yaya za a kwatanta ƙarfin sojin Iran da na Isra'ila?

Iran's Supreme Leader, Ali Khamenei and Israel's Prime Minister, Benjamin Netnayahu, with images of toy soldiers fighting

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, By Arif Shamim
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Urdu & BBC News Persian
  • Lokacin karatu: Minti 9

A karon farko cikin shekara 20, shugaban jagororin hukumar sanya ido kan makamashin nukiliya na duniya ya bayyana a hukumance cewa yanzu Iran ta karya dokokin hana bazuwar nukiliya na duniya.

Ƙasashe 19 cikin 35 da ke cikin hukumar gudanarwar Hukumar ta makamashin atam ta duniya (IAEA) sun kaɗa ƙuri'ar amincewa da matsayar, wadda Amurka da Birtaniya da Faransa da kuma Jamus suka gabatar.

Matsayar ta ce "jerin gazawar" da Iran ta nuna ta hanyar ƙin bayyana cikakken bayani ga hukumar ta IAEA game da shirinta na nukiliya na nufin ta "saɓa doka". Kuma hakan ya samar da damuwa game da tarin makamashin Uranium da aka inganta da iran ke da shi, wanda shi ne ake amfani da shi wajen haɗa makamin nukiliya.

Iran ta yi watsi da bayanin, inda ta bayyana shi a matsayin "siyasa" kuma ta ce za ta buɗe wata sabuwar cibiyar inganta ma'adanin uranium dinta.

Iran ta dage kai da fata cewa shirinta na sarrafa nukiliya ba na yaki ba ne kuma ba za ta taɓa haɗa makamin nukiliya ba.

Isra'ila na kallon shirin Iran na nukiliya a matsayin babbar barazana sannan kuma Firaminista Benjamin Netanyahu ya sha nuna cewa kamata ya yi a ɗauki matakin soja kan Iran a maimakon na diflomasiyya.

Tuntuni an daɗe ana fargabar ƙazancewar rikici a Gabas ta tsakiya sanadiyyar takun-saƙa da ke tsakanin Isra'ila da Iran.

Iranian missiles on display

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ƙarfin makamai masu linzami da Iran ke da shi na daga cikin ƙarfin sojinta

Wacce ƙasa ce ta fi ƙarfi?

BBC ta duba wannan tambaya ta hanyar amfani da wasu kafofi da aka lissafa a ƙasa, duk da cewa kowace ƙasa na da fannin da ta fi ƙarfi.

Cibiyar Nazarin Dabarun Yaƙi ta Duniya (IISS) ta duba ƙarfin sojin ƙasashen biyu, ta hanyar amfani da alƙaluman hukumomi da abin da ake gani a ƙasa wajen ƙiyasta ƙarfin ƙasashen.

Haka kuma wasu ƙungiyoyi kamar Cibiyar Binciken Zaman Lafiya ta Stockholm, ita ma ta duba wannan batu, sai dai alƙaluman kan bambanta ga ƙasashen da ba su bayar da alƙaluma ba.

Haka ma, Nicholas Marsh daga cibiyar Binciken zaman lafiya ta Oslo (PRIO), ya ce ana kallon IISS a matsayin wadda ke auna ƙarfin sojin ƙasashen duniya.

Israel and Iran's population, Gross Domestic Product (GDP), defence budget and defence as a proportion of GDP (4% for israel and 2% for Iran)

IISS ta ce Isra'ila na zuba kuɗaɗe masu yawa a fannin tsaro a kasafin kuɗinta fiye da Iran, lamarin da ya sa take samun ƙarfi a kowane yaƙi da take yi.

IISS ta ce a shekarar 2022 da 2023, Iran ta zuba kusan dala biliyan 7.4 a fanin tsaro a kasafin kuɗinta, yayin da Isra'ila ta zuba kusan dala biliyan 19.

Don haka kudin da Isra'ila ke kashewa a fannin tsaronta idan aka kwatanta da arzikin cikin gida da ƙasar ke samu (GDP) ya ninka na Iran.

Jirgin F-35

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jirgin F-35 na ɗaya daga cikin manyan jiragen saman yaƙi na duniya

Ƙarfin fasaha

Alƙaluman IISS sun nuna cewa Isra'ila na da jiragen yaƙi 340, lamarin da ke ba ta damar kai hare-hare ta sama.

Daga ciki akwai F-15 wanda ke harba makami mai dogon zango, da kuma jiragen F-35 da ke da ƙarfin hari tare da kai wa jirage masu saukar ungulu hari.

Haka nan IISS ta ƙiyasta cewa tana da jiragen yaƙi kusan 320. Tana da jiragen tun shekarun 1960 ciki har da F-4 da F-5 da kuma F-14 - wanda ya yi fice a shekarar 1986.

Amma Nicholas Marsh na cibiyar PRIO ya ce ba a san ko har yanzu tsoffin jiragen na tashi ba, saboda kayan gyaransu na wahalar samu.

Sojojin Ruwan Amurka ne suka fara amfani da jirgin F-14, shekara 20 da suka gabata amma har yanzu ana aiki da shi a Iran

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sojojin Ruwan Amurka ne suka fara amfani da jirgin F-14, shekara 20 da suka gabata amma har yanzu ana aiki da shi a Iran

Na'urar kakkaɓo makamai masu linzami

Na'urorin kakkaɓo makamai masu linzami su ne ƙashin bayan tsaron Isra'ila.

Injiniyan makami mai linzami, Uzi Robin ne ya samar da na'urar kakkabo makamai masu linzami a ma'aikatar tsaron ƙasar.

A yanzu shi ne babban mai bincike a cibiyar nazarin dabarun tsaro a Birnin Kudus, ya kuma shaida wa BBC yadda ya ji ya samu ''kariya'' a lokacin da na'urorin suka kakkaɓo makamai masu linzami da jirage masa matuƙa da Iran ta harba wa Isra'ila a shekarar da ta gabata.

"Na samu gamsuwa, na kuma yi murna, na'urorin na ƙoƙarin kakkaɓo makamai''

Na'urorin kakkaɓo makamai na Isra'ila sun lalata fiye da makamai masu linzami 300 da jirage marasa matuƙa da Iran ta harba a makon da muke ciki.

Asalin hoton, Amir Cohen / Reuters

Bayanan hoto, Na'urorin kakkaɓo makamai na Isra'ila sun lalata fiye da makamai masu linzami 300 da jirage marasa matuƙa da Iran ta harba a bara.

Nisan da ke tsakanin Iran da Isra'ila

Isra'ila na da nisan fiye da kilomita 2,100 daga Iran. Makamanta masu linzami na daidai wurin da za ta harba wa ƙasar, kamar yadda editan hukumar tsaron ƙasar Tim Ripley ya shaida wa BBC.

Tasawirar Iran da Isra'ila

Ana kallon shirin makamai masu linzami na Iran a matsayin wanda ya fi girma tare da faɗi a yankin Gabas ta Tsakiya.

A shekarar 2022, Janar Kenneth McKenzi na Hukumar tsaron Amurka, ya ce Iran na da makamai masu linzami fiye da 3,000.

Haka ma cibiyar kula da tsaron makamai masu linzami ta CSIS, ta ce Isra'ila na sayar wa wasu ƙasashen duniya makamai masu linzami.

Iranian missile or drone fired at Israel

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Iran ta harba makamai masu linzami fiye da 300 da jirage marasa matuƙa zuwa Isra'ila a ranar 13 ga watan Afrilun 2024

Makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa na Iran

Iran ta fara babban aikin ƙera makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa tun bayan yaƙin da ta yi da makwabtanta daga shekarar 1980 zuwa 1988.

Ta kuma ƙera makamai masu cin gajere da dogon zango da kuma jirage marasa matuƙa, waɗanda da yawansu ta harba wa Isra'ila a bara.

Masu nazari sun ce a Iran ne aka ƙera makamai masu linzami da 'yan tawayen Houthi suka harba wa Saudiyya.

Iranian consulate building in rubble

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, An lalata ginin ofishin jakadancin Iran a Syria a wani hari ta sama da aka kai ranar 1 ga watan Afrilun 2024, lamarin da ya yi sanadin mutuwar wani babban jami'in sojin Iran

Hari da makamai masu cin dogon zango

Tim Ripley ya ce ba lallai ne Isra'ila ta iya yaƙin ƙasa da Iran ba.

"Babbar damar da Isra'ila ke da ita ita ce ƙarfin sama da kuma tarin makamai da ake amfani da su ta sama, don haka tana da damar kai hari ta sama zuwa duka wuraren da take da niyyar kai wa a Iran''.

Mista Ripley ya ce Isra'ila za ta iya kashe jami'ai tare da lalata rijiyoyin man Iran ta sama.

A baya an kashe manyan sojoji da manyan fararen hula a wasu hare-hare ta sama, ciki har da harin da aka kai wa ginin ofishin jakadancin Iran a Syria, wanda shi ne ya haddasa harin na Iran.

Isra'ila ba ta ɗauki alhakin harin ba da kuma sauran hare-haren da aka kai wa manyan jami'an Iran.

Sai dai ba ta musanta zarginta da kai harin ba.

Islamic Revolutionary Guard Corps (IRGC) Navy's speedboats move during an exercise in Abu Musa Island, in this picture obtained on 2 August 2023

Asalin hoton, IRGC handout / Reuters

Bayanan hoto, Jiragen ruwan dakarun juyin juya halin Iran yayin da suke atisaye a tsibirin Abu Musa

Dakarun sojin ruwa

Rundunar sojin ruwan Iran na da kusan jiragen ruwa 220, yayin da Isra'ila ke da kusan 60, kamar yadda rahoton cibiyar IISS ya nuna.

A man paddles in front of a German-made Sa'ar 6-class corvette of the Israeli navy docked at the Red Sea port city of Eilat on 16 April 2024

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, IISS ta ce Isra'ila na da jiragen sojin ruwa kusan 60
 The Iranian president in 2008, Mahmoud Ahmadinejad (centre) visits the Natanz uranium enrichment facilities on 8 April 2008 300 km south of Tehran - Ahmadinejad announced on Iranian state television during the visit that Iran had begun the installation ofs6,000 new centrifuges, adding to to the 3,000 centrifuges already at the facility

Asalin hoton, Iranian government / Getty Images

Bayanan hoto, A shekarar 2008, shugaban Iran na wancan lokacin, Mahmoud Ahmadinejad, ya bayyana cewa an samu karuwar samar da makamashin uranium a tashar nukiliyarta da ke Natanz

Barazanar makamin nukiliya

Ana ɗaukar Isra'ila a matsayin wadda ta mallaki makamain nukiliya, amma tana ci gaba da ƙin bayyana hakan.

Amma ba a tunanin Iran ta mallaki makamin, duk da zarge-zargen mallakar makamin da ake yi mata, Iran ta musanta zargin cewa za ta yi amfani da makaminta na nukiliya, wanda ta ce na zaman lafiya ne don zama na yaƙi.

Girman ƙasashen da yawan al'ummominsu

Iran ta fi Isra'ila girman ƙasa da yawan al'umma, inda take da kimanin mutum miliyan 89, saɓanin Isra'ila mai kusan miliyan 10.

Haka kuma Iran ta ninka Isra'ila yawan sojojin da ke bakin aiki, inda take da sojoijin da ke bakin aiki kusan 600,000, yayin da Isra'ila ke da sojoji 170,000 kamar yadda IISS ta nuna.

A ballistic missile with a man standing next to it - the missile is almost as wide as him

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wani makami mai linzami da ya faɗi a tekun Dead Sea bayan da Iran ta ƙaddamar da harin makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa a 2024

Mene ne 'yaƙin Isra'ila da Iran'

Duk da cewa Isra'ila da Iran ba su taɓa yin yaƙi a hukumance tsakaninsu ba, ƙasashen sun sha yin sa-in-sa tare da nuna wa juna yatsa.

An sha kisan manyan jami'an Iran a wasu ƙasashe ta hanyar wasu hare-haren da ake ɗora alhakinsu kan Isra'ila, ciki har da Iran, yayin da ita kuma Iran ke kai hari zuwa cikin Isra'ila ta hanyar amfani da ƙawayenta.

Ƙungiyar Hezbollah da ke Lebanon ce ke yin mafi yawan yaƙin Iran kan Isra'ila daga Lebanon. Iran ba ta musanta mara wa Hezbollah baya ba.

Haka ma goyon bayan da take bai wa Hamas a Gaza. Hamas ta kai hare-haren 7 ga watan Oktoba kan Isra'ila tare da jefa makaman rokoki daga Gaza zuwa cikin Isra'ila na tsawon gomman sekaru.

Isra'ila da ƙasashen Yamma sun yi amanna cewa Iran na samar da harsasai da bindigogi da kuma horo ga maƙayan Hamas.

Houthi fighters sitting around a flag

Asalin hoton, Houthi militants handout / EPA

Bayanan hoto, Mayaƙan Houthi na kai hare-hare kan jiragen ruwa a Tekun Maliya

Ana kallon mayaƙan Houthi a Yemen a matsayin wata kafar da Iran ke amfani da ita. Saudiyya ta ce makaman da mayaƙan Houthi ke harba mata an ƙera su ne a Iran.

Ƙungiyar da ke samun goyon bayan Iran na da ƙarfi a Iraƙi da Syria. Haka nan, Iran na goyon bayan gwamnatin Syria, inda aka ce tana amfani da Syria wajen kai hari Isar'ila.

Ƙarin masu rahoto: Ahmen Khawaja, da Carla Rosch, da Reza Sabeti da kuma Chris Partridge