Iran ta kaddamar da hari kan Isra’ila

...

Asalin hoton, REUTERS

Iran ta bayyana cewa ta kaddamar da hare-hare kan Isra’ila ta hanyar amfani makaman roka da kuma jirage marasa matuka.

Wata sanarwa daga Dakarun juyin-juya-hali na kasar Iran (IRGC) ta ce “an harba gwamman jirage marasa matuka da kuma makamai masu linzami zuwa cikin yankin kasar Isra’ila.

Dama an shiga fargaba kan yiwuwar barkewar fada tsakanin Iran da Isra’ila tun bayan zargin da Isra’ilar da kai hari kan ofishin jakadancin Iran a Syria ranar daya ga watan Afrilu.

Harin ya yi sanadiyyar kashe jami’an Dakarun juyin-juya-hali na Iran, wadanda suka hada da janar-janar guda biyu da kuma wasu ‘yan kasar Syria shida.

Tun a wancan lokaci ne Iran ta yi gargadin cewa ‘Isra’ila za ta dandana kudarta’.

Sanarwar da Iran ta fitar ta kara da cewa harin na yammacin ranar Asabar martani ne kan “manyan laifukan da Isra’ila ta sha tafkawa” - ciki har da harin ranar daya ga watan Afrilu.

Bayanin ya ce an yi wa wannan hare-hare da Iran ta kaddamar taken “Operation True Promise” a turance.

Sai dai sanarwar ba ta yi karin haske kan yanayin harin ba, baya ga cewa kasar ta harba gwamman makamai zuwa cikin Isra’ila.

Netanyahu ya yi wa kasa jawabi

Jim kadan bayan kaddamar da harin, Firaiminstan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi wa al’ummar kasarsa jawabi.

Ya ce dakarun Isra’ila “a shirye suke ko ma mene ne zai faru.”

Ya kara da cewa “al’ummar Isra’ila, a cikin shekarun nan da kuma ‘yan makwannin da suka gabata Isra’ila ta rika yin shirin ko-ta-kwana kan duk wani hari na kai-tsaye da Iran za ta iya kawowa.

“Mun kunna shingenmu na kariya, a shirye muke ta kowane fanni, ta bangaren kariya da kuma kai farmaki. Isra’ila kasa ce mai karfi. Dakarun Isra’ila na da karsashi. Al’ummar kasar na da karfi.”

Netanyahu ya kuma gode wa kawayen kasar kamar Amurka da Birtaniya wadanda ke mara wa Isra’ila baya a kowane hali.

Ya kara da cewa: “Manufarmu a bayyane take: Duk wanda ya cuta mana mu ma za mu cuta masa. Za mu kare kanmu daga duk wata barazana, kuma za mu yi hakan ne kai tsaye babu wata shakka.”

Fargabar rincabewar yaki a Gabas ta tsakiya

Wannan ne barkewar rikici na zahiri sakamakon mummunar gaba da ke tsakanin Iran da kawayenta da kuma Isra’ila a bangare guda.

Kusan mako biyu ke nan Iran na shirya irin martanin da za ta mayar wa Isra’ila bayan harin da ta kai kan ofishin jakadancin na Iran da ke Damascus a ranar daya da watan Afrilu.

Wannan hari da Iran ta kai na nuna cewa tabbas an cimma matsayar kai harin ramuwar-gayya game da matakin Isra’ila wanda ya yi kaca-kaca da ofishin jakadancin na Iran.

Isra’ila dai na da shingayen kariyar tsaro masu yawa, kuma ta sha alwashin daukar fansa kan duk wani hari da za a kai a kanta.

Babbar barazanar da za a fuskanta a yanzu shi ita ce hare-haren ramuwar gayya tsakanin kasashen biyu za su iya haifar da barkewar fada a yankin Gabas ta tsakiya, wani abu da kasashen yankin da dama ke kokarin kauce mawa tun bayan harin da Hamas ta kai cikin Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba.