Shugaba Biden ya sha alwashin kare Isra’ila daga harin Iran

...

Asalin hoton, REUTERS

Shugaba Biden ya yi wa Isra'ila alƙawarin samun cikakken goyon baya, yayin da ake ci gaba da fargabar cewa Tehran za ta ƙaddamar da harin ramuwar kisan da aka yi wa babban kwamandan sojin Iran.

A farkon watan nan ne, wani hari da aka kai a Syria ya tarwatsa ofishin jakadancin Iran.

Shugaba Biden ya yi gargaɗin cewa Iran ta na barazanar ƙaddamar da hari mai muni a kan Isra'ila, lamarin da kuma hukumomin Amurka ke tsoron cewa zai iya faruwa kowanne lokaci.

Zaman ɗar-ɗar ya ƙaru a Washington game da kausasan kalaman da hukumomi a Tehran ke amfani da su, inda suka sha alwashin rama harin da suke zargin Isra'ila ta kai a kan ginin fishin jakadancin Iran da ke birnin Damascus.

Mr Biden dai ya ce goyon bayan Amurka ga Isra'ila mai ƙarfin gaske ne, kuma Amurkan za ta yi duk abin da ya dace wajen tabbatar da tsaron ƙawar ta.

Shugaban Amurkan na magana ne sa'oi bayan jagoran Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya sake jaddada cewa Isra'ila za ta girbi abin da ta shuka game da harin da ta kai ofishin jakadancin Iran.

Ya ce: "Suna barazanar kai hare-hare kan Isra'ila. Kamar yadda na shaidawa Firaiminista Netanyahu, a tsaye muke damin kare Isra'ila daga wannan barazana ta Iran. Bari ma in ƙara jaddawa; Za mu yi duk abin da ya dace domin tabbatar da tsaron Isra'ila."

Da alama dai Amurka tana aikewa da saƙo ne cewa duk da banbancin ra'ayi da ke tsakanin su a game da yaƙin Gaza,Washington a shirye take ta mayar da martani mai zafi a kan duk wani hari da aka kai wa Isra'ila.

Jakadan Iran a Damascus ya ce mutum 13 harin ya kashe ciki har da mambobin sojojin juyin-juya hali na Jamhuriyar musulunci ta Iran guda bakwai, da 'yan kasar Syria shida.

Daga cikin mutanen akwai birgediya janar Mohammad Reza Zahedi, wanda jigo ne a cikin dakarun Ƙurdawa.