Abin da muka sani kan hare-haren Isra'ila kan cibiyoyin nukiliyar Iran

Asalin hoton, Getty Images
A daren Juma'ar nan ne Isra'ila ta ƙaddamar da jerin hare-hare kan Iran, waɗanda ta ce ta kai su ne kan 'cibiyoyin' nukiliyar Iran.
Yayin da ake sa ran harin ramuwar gayya 'nan ba da jimawa ba', tuni Isra'ila ta ayyana dokar ta ɓaci a ƙasar.
Cikin waɗanda harin ya kashe har da babban hafsan dakarun juyin-juya halin ƙasar - babbar rundunar soji mafi ƙarfi a ƙasar - Hossein Salami, tare da wasu ƙwararru a harkar nikiliyar ƙasar, kamar yadda kafar yaɗa labaran Iran ta wallafa.
Amurka ta ce ba ta da hannu a hare-haren, wanda ya shafi babbar cibiyar nukiliyar Iran.
Yaushe kuma a ina aka ƙaddamar da harin?
An bayar da rahoton jin ƙarar harbe-harbe a Tehram, babban birnin ƙasar da misalain ƙarfe 3:30 na dare agogon ƙasar.
Kafofin yaɗa labaran Iran sun ce hare-haren sun faɗa kan unguwannin jama'a, yayain da aka ji ƙarar fashewa a arewa maso gabashin birnin. Sai dai BBC ba ta iya tabbatar da sahihancin rahotonnin ba.
A Isra'ila, ƙarar ƙararrawar ankararwa ce ta tayar da mutane a daidai lokacin, tare da turawa mutane saƙon gargaɗi ta waya.
Sa'o'i bayan hare-haren farko, an samu rahoton fashewa a cibiyar nukiliyar Iran da ke Natanz - mai tazarar kilomita 225 daga kudancin Tehran - a cewar kafofin yaɗa labaran ƙasar.

Asalin hoton, Getty Images
Me Isra'ila ta ce?
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya ce hare-haren - da ya kira da ''Operation ɗan zaki ya girma'' - an kai su ne kan cibiyoyin sojin Iran domin kakkaɓe abin da ya kira ''barazana ga wanzuwar Isra'ila''.
Ya ce hare-haren za su ''ci gaba nan da kwanaki masu zuwa...''
"A watannin baya-bayan nan, Iran na ɗaukar matakan da a baya taɓa ɗauka ba, ta hanyar mayar da makamashin uranium dinta makamin yaƙin.
"Idan ba a dakatar da ita ba, Iran ka iya ƙera makamin nukiliya cikin ƙanƙannin lokaci. Zai iya kasancewa cikin shekara guda, zai iya kasancewa cikin ƴan watanni, ƙasa da shekara guda. Kuma hakan babban hatsari ne ga Isra'ila da barazana ga wanzuwar Isra'ila.''
Isra'ila dai ta ce jiragen yaƙi 200 ne suka kaddamar da farmakin cikin dare a Iran inda ta ce sun kai hare-hare a wurare 100.
Wani jami'i a rundunar sojin Isra'ila ya faɗa wa BBC cewar Iran na da isassun kayayyakin da za ta iya ƙera bama-boma nukiliya ''cikin kwanaki''.

Asalin hoton, .
Me Iran ta ce?
Kakakin rundunar sojin Iran, ya ce Amurka da Isra'ila za su ''ɗanɗana kuɗarsu'', sakamkon hare-haren, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.
"Dakarun sojinmu za su mayar da martani kan wannan hari na Yahudawa," a cewar kakakin na rundunar sojin ƙasar, Abolfazl Shekarchi.
Me Amurka ta ce?
Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya ce babu hannun ƙasarsa a hare-haren, kuma Amurkan ba ta bayar da kowane irin taimako ba wajen ƙaddamar da hare-haren.
Ya ce babban abin da Amukr at sanya a gaba shi ne kare dakarun ƙasar da ke yankin Gabas ta Tsakiya.
Shugaba Trump ya shaida wa kafar Fox cewa ya yi gargaɗi ga Isra'ila na kaucewa kai harin wanda ya ce zagon kasa ne ga tattaunawar da ake yi da Iran na taƙaita shirinta na nukiliya.
Me ƙasashen duniya ke cewa
Gwamnatin Saudiya ta yi allawadai da hare-haren na Isra'ila a cibiyoyin nukiliyar Iran, inda a cikin wata sanarwa daga ma'aikatar harakokin wajen Saudiyya ta bayyana harin a matsayin wanda ya saɓa ƴancin Iran da tsaronta da saɓa dokokin kasa da kasa.
Ƙasar Oman - da ke shirin karɓar baƙuncin tattaunawar nukiliyar Iran ɗin - ta ce hare-haren na Isra'ila mataki ne na takalar faɗa mai hatsari, wanda ke barazana ga ƙoƙarin tattaunawa da kuma zaman lafiya a yankin.
Japan ma ta yi allawadai da harin na Isra'ila inda ta yi kira ga ɓangarorin biyu su kai zuciya nesa. Ta ce zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya yana da matukar muhimmanci ga Japan.











