Shin mece ce manufar Isra’ila kan gwamnatin Iran?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Amir Azimi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Editor, BBC Persian
- Lokacin karatu: Minti 3
Bayan burin Isra'ila na lalata abin da ta kira barazanar nukiliyar Iran ta hanyar hare-haren da ta kai ranar Juma'a, Benjamin Netanyahu yana da babbar manufa - sauyin mulki a Tehran.
A karkashin wannan yanayi, yana iya fatan hare-haren da ba a taba ganin irin su ba su haifar da tarzomar da za ta kifar da Jamhuriyar Musulunci.
Cikin wata sanarwa ranar Juma'a ya bayyana cewar ''lokaci ya yi da al'ummar Iran za su haɗa kai don martaba tutar ƙasar da tarihinta, sannan kuma su ƙwaci ƴancinsu daga mulkin zalunci."
Ƴan Iran da dama na takaicin yadda tattalin arziƙin ƙasar ya taɓarɓare da rashin ƴancin faɗin albarkacin baki da rashin ƴancin mata da kuma murƙushe ƙananan ƙabilu.
Harin Isra'ila na yi wa shugabancin Iran barazana.
Hare-haren sun kashe kwamandan dakarun juyin juya halin a Iran (IRGC) da babban hafsan sojojin ƙasar da wasu manyan kwamandojin IRGC, kuma har yanzu Isra'ila na ci gaba da hare-haren. Iran ta mayar da martani a jiya, inda IRGC suka ce sun kai wa sansanonin sojoji da filayen jiragen sama hare-hare.
Yanayin ya yi ƙamari ƙwarai, bayan ramuwar gayyar da Iran ta kai da makamai masu linzami. Netanyahu ya ce ''wasu hare-haren na nan tafe''.
Akwai yiwuwar kai wa shugabannin Iran hari.
Isra'ial za ta iya hasashen hare-hare da kashe mutane da dama zai haifar wa da gwamnati kalubale kuma zai buɗe kofar tarzoma.
Wannan shi ne burin Netanyahu.
To amma fa babu tabbas zai yi nasara.
Masu riƙe da manyan muƙamai a Iran, mutane ne da suke iko da sojoji da tattalin arziƙi.
Ba sa buƙatar yin juyin mulki, amma za su iya amfani da mummunan rikici wajen karɓe mulki.

Asalin hoton, EPA-EFE/Shutterstock
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wani abu da zai iya yiwuwa shi ne rushewar gwamnatin Iran da shigar ƙasar cikin ruɗani.
ƙasar mai ywan al'umma kusan miliyan 90, duk tashin hankalin ya samu Iran zai yi tasiri a faɗin Gabas ta Tsakiya.
Dakarun adawa a Iran sun watse a shekarun baya-bayan nan.
Bayan zanga-zangar da aka gudanar a shekara ta 2022 mai taken "Woman Life Freedom", wasu ƙungiyoyin adawa sun yi yunƙurin kafa gamayyar ƙungiyoyin waɗanda basa goyon bayan gwamnatin Musulunci da ƴan fafutuka.
Amma ba su yi nasara ba saboda rabuwar kai da aka samu game da wanda zai jagoranci gamayyar ƙungiyoyin da kuma abinda zai biyo baya idan an hamɓarar da gwamnati.
Isra'ila za ta iya kallon shugabannin waɗannan ƙungiyoyi a matsayin mafita.
Misali tsohon Yariman Iran Reza Pahlavi, ɗan tsohon Sarkin Iran, wanda aka hamɓarar a shekara ta 1979.
Ya yi gudun hijira kuma yana ta ƙoƙarin neman goyon baya daga ƙetare.
A baya-bayan nan ya ziyarci Isra'ila.
Duk da cewar ya samu goyon bayan wasu mutane a Iran, babu tabbas ko karɓuwar tasa zara rikiɗe har a samu sauyun gwamnati.
Akwai kuma Mujahideen-e Khalq (MEK) ƙungiyar adawa, wadda ke goyon bayan hamɓarar da gwamnatin Musulunci to amma tana adawa da mulkin sarautar gargajiya.
An ƙirƙire ta a matsayin ta masu tsattsauran ra'ayin Addinin Islama, a baya ta yi yiwa sarki zazzafar adawa.
Bayan juyin juya halin, MEK ta koma Iraq ta haɗu da Saddam Hussein a farkon shekara ta 1980 lokacin da ya yaƙi Iran, abinda ya sanya farin jinin su ya ɓace.
Ƙungiyar ta ci gaba da ayyukanta kuma tana da ƙawaye a Amurka wasu daga ciki makusantan tawagar Donald Trump.
Alamu sun nuna farin jininta ya ragu a fadar white House a yanzu idan aka kwatanata da lokacin wa'adin mulkin Trump na farko, lokacin da jami'an Amurka da suka haɗa da Mike Pompeo da John Bolton da Rudy Giuliani kan halarci tarukan ƙungiyar MEK har su yi jawaban goyon baya.
Za a iya cewa ya yi wuri a bayyana irin ta'adin da harin ranar Juma'a ya yi,amma lokacin musayar wuta a shekarun baya tsakanin Isra'ila da Iran, babu alamun da suka nuna ƴan Iran zasu yi amfani da damar da aka samu don hamɓarar da gwamnati.
Kodayake abubuwan da suka faru a baya, ba irin harin ranar Juma'a ba ne.
Kawo karshen gwamnatin Iran
Duk da hare-haren da ta kai Isra'ila, kamar Iran ba ta da mafita.
Wasu za su iya ganin mafita ita ce, a ci gaba da tattaunawa da Amurka.
To amma komawa tattaunawa kamar yadda Trump ya buƙata, zaɓi ne mai wahala ga shugabannin Iran domin hakan na nufin sun amince an yi nasara a kan su.
Mafita ta biyu kuwa ita ce, ta ci gaba da kai wa Isra'ila hare-haren ramuwar gayya.
Wannan ita ce mafitar ta za ta fi ƙarbuwa.
Kuma wannan ne abinda shugabannin Iran suka yiwa magoya bayansu alƙawari, to amma ci gaba da hare-hare, zai ƙara janyo hari daga Isra'ila
A baya Tehran ta yi barazanar kaiwa sansanin sojin Amurka da ofisoshin jakadanci da wasu muhimman yankuna hari.
Ɗaukar wannan mataki ba zai zama mai sauƙi ba, don kaiwa Amurka hari zai janyo ta cikin rikicin, abinda Iran ba zata so ba.










