Fubara ko Wike: Da wa Tinubu zai fi ɗasawa?

Fubara da Wike

Asalin hoton, Rivers State Government Press

Lokacin karatu: Minti 3

Masana lamurran siyasa a Najeriya sun soma tsokaci akan ficewar gwamnan jihar Ribas Siminalayi Fubara daga jam'iyyar PDP zuwa APC.

Masanan na ganin matakin tamkar wani yankan baya ne ga tsohon ubangidansa, kuma ministan babban birnin tarayyar Najeriya Abuja, Nyesom Wike, da suka dade suna samun takun saka tsakaninsu, kasancewar a yanzu Fubara ne zai ci gaba da jan ragamar jam'iyyar APCn jihar.

Mal Kabir Sufi, malami ne a kwalejin share fagen shiga jami'a da ke Kano ya shaida wa BBC cewa, shugaba Bola Tinubu ne ke da riba a wannan sauya sheƙa da Fubara ya yi.

Ya ce," Wannan mataki zai bawa Tinubun damar juya akalar siyasar jihar Ribas ba tare da dogaro da ministan babban birnin tarayyar Najeriya Abuja, Nyesom Wike ba."

"Idan ma akwai wanda ya yi rashi a wannan sauya sheka to bai wuce shi Nyesom Wike da kuma yaransa ciki har da wadanda suke a majalisar dokokin jihar Ribas din".In ji shi.

Mal Kabir Sufi, ya ce," Dama tun bayan janye dokar ta baci da aka yi a jihar Ribas din, ake ganin cewa kafin a janye din an cimma wasu matsaya da gwamnan da kuma bangaren shugabancin kasa musamman na cewa idan zai nemi wa'adi na biyu, to akwai yiwuwar sai dai ya koma jam'iyya mai mulki ta APC."

Masanin siyasar ya ce," Yanzu ba a san wanne mataki shi Wike zai ɗauka akan sauya sheƙar da shi Fubara ya yi ba."

Ya ce, "Ba a sani ba ko an samu wata yarjejeniya a tsakaninsu ba, to amma idan har da masaniyar Wike Fubara ya koma APC, to ba a san yadda dangantakarsu zata kasance ba a yanzu, sannan kuma menene makomar siyasarsa, idan babu masaniyar Wike to ba a san abin da zai yi ba."

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

" A 'yan kwanakin nan abubuwa da dama zasu biyo baya wato bayan sauya shekara Fubara zuwa APC, misali ko zai ka iwa Wike ziyara su tattauna, ko Wike ya yi wasu jawabai ko kuma menene makomar su da suke rike da jam'iyyar a jihar ba." In ji shi.

Shi ma farfesa Abubakar Kari, masanin siyasa a Najeriya kuma malami a jami'ar Abuja, ya shaida wa BBC cewa,"Dama 'yan Najeriya da dama sun yi hasashen cewa hakan zata iya faruwa domin Fubara ta kansa ya ke yi domin tun da 'yan majalisar dokokinsa su 16 suka sauya sheka kwanaki kadan da suka wuce, to ba makawa shi ma sai ya sauya."

Ya ce,"Da bai dauki wannan mataki na sauya sheka ba, to tsige shi a wajen 'yan majalisar ba zai zamo wani abu mai wuya ba."

"A bangaren Wike kuwa, dama ana hasashen cewa idan ma kwangila aka bashi na tarwatsa jam'iyyar PDP, to kusan ya kammalata, domin a yanzu PDP ta shiga wani mawuyacin hali, a don haka tun da ya kammala abin da ake gani an sanya shi ya yi, to da sannu a hankali kimarsa dama darajarsa zata ragu, saboda irin karfin da Wike ke dashi a yanzu, bai kai na lokacin da aka bashi minista ba."In ji Kari.

Tun dai a shekarar 2023, aka fara samun rikici a tsakanin gwamna Fubara da Nyesom Wike, inda har rikicin ya kai ga shugaba Tinubu ya sanya wa jihar Ribas din dokar ta baci ta watanni shida da kuma tilastawa Fubara ya Sauka daga mukaminsa na tsawon watanni.

A bisa al'adar siyasa dai gwamnan jiha shi ne jagoran jam'iyya, kuma idan aka yi la'akari da wannan tsari, a yanzu Fubara ne zai kasance jagoran jam'iyyar APC a jihar ta Ribas.