AU ta yi allawadai da kisan fiye da mutum 50 a Zamfara

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar Tarayyar Afirka ta yi allawadai da abin da ta kira munanan hare-haren ƴan bindiga da aka kai a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya, inda aka kashe fiye da fararen hula 50 tare da sace mata da yara da dama.
A sanarwar da shugaban hukumar ƙungiyar, Mahmoud Ali Youssouf ya fitar a ranar Lahadi, ya bayyana harin a matsayin babban take hakkin bil’adama da kuma barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Rahotanni sun nuna cewa harin ya faru ne a ƙauyen Dutsin Dan Ajiya da ke ƙaramar hukumar Anka, inda ‘yan bindiga sama da 150 suka mamaye garin da yamma a kan babura
Sun kuma tare hanyoyin shiga da fita domin hana mutane tserewa sannan suka riƙa harbi ba tare da kakkautawa ba kafin nan suka ƙone gidaje.
Majiyoyin yankin sun ce maharan sun shafe sa’o’i suna kai farmaki tun daga daren Alhamis har zuwa safiyar Juma’a.
Wasu mazauna sun bayyana cewa sun sanar da jami’an tsaro tun da suka hango maharan na tahowa, amma ba su samu ɗauki cikin lokaci ba.
Ƙungiyar ta nuna cikakken goyon baya ga gwamnatin Nijeriya da al’ummarta, tare da jajanta wa iyalan waɗanda suka rasu da kuma yi wa waɗanda suka jikkata fatan samun sauƙi cikin gaggawa.
Ta kuma bukaci a saki mutanen da aka sace nan take ba tare da wani sharaɗi ba, tare da kira ga ƙarin haɗin gwiwar tsaro domin kare jama’a da hana sake aukuwar irin waɗannan hare-hare.
Zuwa yanzu dai gwamnatin Nijeriya ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.




