KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 25/01/2026

Wannan shafi ne da ke kawo mu ku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Yusuf Mohammed da Abdullahi Bello Diginza

  1. Ana ci gaba da zanga-zanga a sassan Amurka bayan jami'an tsaro sun harbe wani mutum

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Jami'an shige da fice na Amurka sun harbe wani mutum har lahira a Minneapolis, lamarin da ya haifar da zanga-zanga da kuma tofin Allah tsine daga sassa daban daban na ƙasar.

    Ɗaruruwan masu zanga-zangar ne suka fito cikin sanyi don nuna adawa da harbin Alex Pretti, wanda danginsa suka bayyana a matsayin ma’aikacin jinya mai shekaru 37 da haihuwa, yayin wata arangama da aka yi da safiyar Asabar.

    Bidiyo da yawa daga wurin da abin ya faru sun nuna hatsaniya tsakanin jami'an shige da fice na tarayya da Pretti.

    Hukumomin tarayya da na jiha sun ba da rahotanni masu cin karo da juna kan yadda lamarin ya auku, wanda ya zo kasan makonni uku bayan wani jami'in hukumar shige da fice (ICE) ya kashe wata mata mai suna Renee Good a cikin motarta a birnin Minneapolis.

  2. Gwamnatin Kano ta gargaɗi masu amfani da shafukan sada zumunta kan aibata Kwankwaso

    Gwamnan Kano

    Asalin hoton, Abba Kabir/FB

    Gwamnatin Kano ta gargaɗi masu amfani da shafukan sada zumunta game da aibata jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwanso.

    Gwamnan jihar, Alhaji Abba Kabir Yusuf ne ya yi gargaɗi kwana guda bayan raba gari da jam'iyyar NNPP da Sanata Kwankwaso ke jagoranta.

    Yayin wani jawabi da ya gabatar a taron bayar da kyaututtuka da gwamnatinsa ta shirya wa masu amfani da shafukan sada zumunta ranar Asabar a jihar, Gwamna Abba ya bayyana Kwankwaso a matsayin shugaban da ya cancanci girmamawa saboda sauye-sauyen da ya samar wa Kano.

    A ranar Juma'a ne Abba Kabir ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar NNPP da ake zaɓe shi matsayin gwamna a cikinta a 2023.

    A ranar Asabar ma wasu ƴan majalisar dokokin jihar 22 ƙarƙashin jagorancin kakakin majalisar jihar, Hon. Jibril Ismail Falgore, suka sanar da bin sahun gwamnan wajen barin jam'iyyar NNPP.

  3. An fara kaɗa ƙuri'a a zagayen ƙarshe na zaɓen Myanmar

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    An fara kaɗa ƙuri'a a zagaye na uku kuma na ƙarshe na zaɓe a yankuna da dama na ƙasar Myanmar wadanda ba sa ƙarƙashin ikon ƴan tawaye.

    A cewar wata tawagar BBC da ta ziyarci rumfunan zaɓe da dama yayin da aka gudanar da zaɓen, akwai yanayi na fargaba, inda mutane da dama ke jin an matsa musu su fito.

    Ƴan jarida sun ce jami'an leƙen asiri na soji na biye da su yayin da suke ƙoƙarin yaɗa labaran yaƙin neman zaɓe.

    Ana sa ran jam'iyyar da ke goyon bayan sojoji za ta samu gagarumin rinjaye, a zaɓen da Majalisar Dinkin Duniya da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama suka bayyana a matsayin mara adlaci ko daidaito.

    Ƙasar Myanmar dai ta faƊa cikin rikicin cikin gida tun bayan da sojoji suka hamƁarar da gwamnatin farar hula kusan shekaru biyar da suka gabata.

  4. Sassan Amurka na fuskantar yanayin hunturu mai tsanani

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Mummunar iska mai ƙanƙara ta haifar da ruwan sama a jihohin New Mexico da kuma Texas a yayin da kuma ta ke ci gaba da yaɗuwa zuwa sassan da ke arewa maso gabashin ƙasar.

    Mutane miliyan ɗari biyu iskar za ta iya shafa, sannan kuma masu hasashen yanayi sun yi gargaɗin cewa za a iya samun sanyin da zai kai ƙasa da maki ɗaya a ma'aunin celcius.

    Tuni aka ɗauke wutar lantarki musamman a Texas da Louisiana sannan kuma mutane fiye da dubu 100 na zaune a cikin duhu.

    An dai sauke tashi da saukar jirage kusan dubu 13 a faɗin ƙasar.

  5. Sojoji sun kama matar da ake zargin tana kai wa ƴan Boko Haram wiwi

    ...

    Asalin hoton, DHQ

    Dakarun rundunar ɗguiwa ta arewa maso gabas, Operation HADIN KAI, sun kama wata mata mai shekaru 65 da haihuwa, bisa zarginta da safarar miyagun ƙwayoyi ga ƴan ƙungiyar Boko Haram da ke kai hare-hare a sassan jihar Borno.

    Wata sanarwa da jami'in yaɗa labarai na rundunar, Laftanar Kanar Sani Uba ya fitar ta ce an kama wanda ake zargin ne a karamar hukumar Askira uba da ke jihar Borno, a ranar 23 ga watan Junairu, 2026, yayin wani samame da rundunar ta kai sakamakon bayanan sirri da ta tattara.

    Sanarwar ta ƙara da cewa ana zargin matar ne da zama babbar mai samar da tabar wiwi ga ƴan Boko Haram da ke aiki a faɗin yankin da ya haɗa da Askira Uba da Rumirgo da Gwahi da Wamdiyo, da Uvu da kuma Gaya.

    Binciken farko dai ya nuna cewa wadda ake zargin ta samo tabar wiwin ne daga ƙaramar hukumar Sarti Baruwa ta jihar Taraba kuma an kama ta da ƙunshin ganyen wiwi guda 14 mai nauyin kimanin kilogiram 30.

    ''A halin yanzu dai wadda ake zargin ta na tsare yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike, don ganowa tare da wargaza hanyoyin da ake amfani da su wajen safara da rarraba miyagun ƙwayoyin''. In ji sanarwar

  6. Wani mutum ya hau gidan bene mai hawa 101 ta bango

    ...

    Asalin hoton, EPA

    Wani ɗan ƙasar Amurka mai hawa dutse Alex Honnold ya yi nasarar hawa wani dogon bene a Taiwan ba tare da igiya ko wani kayan kariya ba.

    Ginin mai suna Taipei 101 wanda aka yi masa laƙabi saboda yawan hawan da ya ke da su, ya kai tsawon mita 508.

    Honnold ya shahara bayan da ya kasance mutum na farko da ya hau El Capitan, dutse mai ɗan karen tsawo da ke gandun dajin Yosemite da ke California - kuma ba tare da igiya ko kayan tsaro ba.

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Tun da farko dai an shirya hawan ginin ne a ranar Asabar amma aka jinkirta sakamakon ruwan sama.

    Wannan bajinta na shi dai a watsa shi kai-tsaye a dandalin Netflix.

    Honnold ya kammala hawa ginin ne a cikin awa ɗaya da minti 31.

  7. An haramtawa ƴan jarida shiga zaman kwamitin bincike kan rikicin bayan zaɓe a Tanzania

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    An hana ƴan jarida a Tanzaniya halartar zaman kwamitin bincike kan rikicin da ya biyo bayan zaɓen shugaban ƙasa, yayin da waɗanda rikicin ya rutsa da su ke bayar da shaida.

    Kwamitin da shugaba Samia Suluhu ta kafa, na gudanar da bincike a kan rikicin da nufin gano musabbabin sa da kuma ba da shawarar hanyoyin da za a bi wajen samar da sulhu a ƙasar.

    An buɗe zaman farko ga manema labarai, kuma duka kafafen yaɗa labarai na gida da na waje sun ba da rahoto kan shaidar waɗanda abin ya shafa.

    Sai dai kuma ƴan jarida da wasu kafafen yaɗa labarai sun ce ba a ba su damar halartar tarukan da suka biyo biyo baya ba ranar Asabar.

    A ranar Juma'ar da ta gabata, kafofin yaɗa labarai na cikin gida ne aka bai wa damar shiga zaman kwamitin a birnin Dar es Salaam.

    Wata sanarwa da wata jarida mai zaman kanta 'The Citizen' ta wallafa a shafukan sada zumunta ta ce an ba wa ƴan jarida damar yaɗa labaran zaman da aka yi ranar Juma’a, inda waɗanda abin ya shafa suka bayyana yadda al'amura suka gudana lokacin rikicin.

    Har yanzu ba a tabbatar da ko za a mai do da damar kafofin watsa labarai na shiga zama na gaba ba.

  8. An dawo da Intanet a sassan ƙasar Iran

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata kafar yaɗa labaran Iran ta rawaito cewa gwamnatin ƙasar dawo da intanet din data ɗauke a sassan ƙasar.

    Gwamnatin ta katse intanet ɗin ne a lokacin da aka fara zanga zangar nuna adawa da matakan gwamnati a faɗin ƙasar a ƙarshen watan da ya gabata.

    Jami'ai sun ce za a ɗauki tsawon lokaci kafin duka harkokin Intanet su daidai ta saboda wasu matsaloli na na'ura.

    Ɗaukewar intanet ɗin ya sa an gaza tabbatar da adadin mutanen da aka kashe a lokacin zanga zangar.

    Wata ƙungiyar kare haƙƙin ɗan'adam da ke Amurka ta ce an kashe fiye da mutane dubu huɗu.

  9. Jami'an tsaron Amurka sun harbe wani mai zanga-zanga a Minnesota

    ...

    Asalin hoton, EPA

    Jami’an tsaro na gwamnatin tarayya a Amurka sun bindige wani mutum mai zanga-zanga a birnin Minneapolis ranar Asabar.

    Wannan dai shi ne mutum na biyu da aka kashe a birnin tun lokacin da gwamnatin Trump ta ƙaddamar da wani yaƙi na musammman kan ƴan cirani a jihar ta Minnesota.

    Jami’an yankin sun bayyana sunan mutumin a matsayin Alex Pretti mai shekaru 37, ɗan ƙasar Amurka ne kuma ma'aikacin jinya da ke zaune a Minneapolis.

    Bidiyo da aka wallafa a shafukan intanet sun nuna yadda aka yi taho-mu-gama tsakanin jami'an tsaron kan iyaka da kuma mutumin.

    Ma’aikatar tsaron cikin gida (DHS) ta ce jami’an sun yi harbi ne domin kariyar kai bayan Pretti, wanda suka ce yana da riƙe da bindiga, ya bijirewa yunƙurinsu na ƙwace masa makamai.

    Lamarin, wanda ya zo makonni biyu bayan harbe Renee Nicole Good da wani jami’in shige-da-fice ya yi, ya haifar da ci gaban zanga-zanga tare da kiraye kiraye da shugabannin yankin cewa jami'an tsaron gwamnatin tarayya su fice daga birnin.

  10. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Lahadi.

    Kamar kullum, yau ma za mu kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara kan labaran da mu ke wallafawa.