'Jini faca-faca a jikina' - matar da ta kuɓuce daga hannun ƴan bindiga a Kajuru

- Marubuci, Madina Maishanu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa
- Aiko rahoto daga, Kurmin Wali
- Lokacin karatu: Minti 6
Makaken bandeji ne manne a kan Sarah Peter sanadiyyar jinin da ya riƙa zuba daga kan nata bayan wani ɗan bindiga ya buga mata makami.
Sarah, wadda ba sunanta na gaskiya ke nan ba, na a cikin cocin da aka kai wa hari ranar Lahadi a jihar Kaduna, da ke arewacin Najeriya, inda maharan suka yi musu ƙawanya sannan suka kwashe mutane zuwa cikin daji a ƙafa.
Matar mai shekara 60, wani ɗan bindiga ne ya dake ta da gindin bindiga domin matsa mata don ta yi sauri.
"Jini ne ta ko'ina,'' in ji ta, yayin da take taɓa wurin da aka ji mata rauni a kai.
"Na sha wahala," kamar yadda ta shaida wa BBC, wadda da alama har yanzu ba ta warware daga firgicin da take ciki ba game da abin da ya faru a ranar Lahadi.
Ta ƙara da cewa "sun ci gaba da fizga ta duk kuwa da cewa na shaida musu cewa ba na iya tafiya. Daga nan sai na fakaici idonsu na ɓoye, suka wuce har suka yi nisa. Na gaji sosai, amma haka na jawo jikina har na dawo ƙauyenmu."
To amma har yanzu gwamman mutanen da aka ɗauke daga cocinsu na Cherubin and Seraphim Movement Church da sauran wasu majami'un guda biyu da ke ƙauyen Kurmin Wali, mai nisan kilomita 84 daga birnin Kaduna, na can cikin daji.
Duk da cewa 11 daga cikinsu, ciki har da Sarah, sun samu damar kuɓutowa, kimanin mutum 160 ne babu labarinsu, in ji ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya a yankin.
Su kuma mutanen ƙauyen na cikin kaɗuwa na abin da ya faru da kuma tsoron cewa za a iya sake kai musu wani harin a kowane lokaci.
Har yanzu hukumomi ba su fitar da adadin mutanen da aka sace ba a hukumance.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kurmin Wali ƙauye ne da ke kusa da dajin Rijana, wanda maɓuya ce ga tarin ƴan bindiga waɗanda suka daɗe suna kai samame a ƙauyuka kuma suna garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa a yankin.
Babu wata ƙungiya da ta fito ta ɗauki alhakin kai harin na ranar Lahadi, to amma da alama harin na cikin ire-irensa da ake samu a yankin sanadiyyar matsalolin tsaro da suka zama ruwan dare a yankin.
Biyan kuɗin fansa abu ne da aka haramta a dokokin Najeriya, to amma har yanzu ana kyautata zaton cewa mutane na ci gaba da biyan kuɗin domin ceto waɗanda ake garkuwa da su.
Sai dai a game da mutanen da aka kwashe ranar Lahadin nan, har yanzu ba a kira ba domin neman kuɗin fansa.
Matsalar tsaron Najeriya na ci gaba da jan hankalin duniya tun bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya yi zargin cewa ana kai wa mabiya addinin Kirista hari tare da kashe da dama. A watan da ya gabata, Amurka ta ƙaddamar da hari kan wasu da ake zargin ƴan bindiga ne a arewa maso yammacin Najeriya.
Hukumomi a Najeriya sun musanta cewa Kiristoci ne kawai ake kashewa a dalilin addininsu, inda hukumomin suka ce ana kashe Musulmi da Kirista har ma da mutanen da ba su bin wani addini, a sanadiyyar rashin tsaro.
To amma al'ummar Kurmin Wali na cikin damuwa da fusata.
Wani jagoran al'umma a ƙauyen ya ce sun daɗe suna rayuwa cikin tsoro. Mazauna ƙauyen na buƙatar mahukunta su inganta tsaro a yankin sannan sun zargi gwamnati da ƙoƙarin rufe bakunansu a game da farmakin na ranar Lahadi.

Kusan kimanin kwana biyu bayan kai harin, an bar mutane a cikin ruɗani bayan da hukumomi suka ƙaryata faruwar harin, duk da cewa shaidu sun tabbatar da faruwar lamarin, sai a ranar Talata da yamma ne hukumomi suka fito suka gaskata faruwar lamarin.
"Sun ce mana kada mu yi wa kowa bayani kan abin da ya faru, sun so su tsorata mu, to amma wajibi ne mu fadi abin da ya faru. Haka nan sun yi ta ƙoƙarin hana ƴan jarida shigowa ƙauyen," in ji wani matashi mai kimanin shekara 20, wanda bai so a ambaci sunansa ba.
Babu masanaiya kan dalilin da ya sa da farko hukumomi suka ƙi bari labarin ya fita, to amma gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya shaida wa BBC cewa jami'an tsaro sun so su kammala tattara bayanai ne tukuna kafin fitar da bayani.
To amma, hakan bai fayyace dalilin da ya sa kwamishinan ƴansanda a jihar ta Kaduna ya ƙaryata faruwar harin ba tun da farko, inda a farko ya ce "ƙaryace tsagwaronta, wadda masu yaɗa ƙarya da son tayar da husuma ke bazawa domin kawo tashin hankali".
Ita karan-kanta BBC ta sha wahala wajen shiga ƙauyen na Kurmin Wali, bayan da wani ɗan siyasa da wasu jami'an tsaro suka yi yunƙurin hana hakan.
To amma mun samu damar shiga, inda muka iske al'ummar cikin yanayi na tashin hankali, musamman abinda muka gani a cocin Cherubim and Seraphim Movement, inda za ka iya ganin kujerun roba masu launuka daban-daban a tarwatse, litattafai a warwatse a ƙasa sannan an karairaya wasu kayan kiɗa, tamkar ƴan bindigar ba su daɗe da tafiya ba.
Christopher Yohanna, wanda ke tsaye a gefe yana kallon ƴarsa mai shekara biyu a duniya ya ce shi ma ya samu kuɓuta daga hannun ƴan bindigan.

''Muna cikin coci, sai muka ji ana ta ihu. Lokacin da muka fito da niyyar guduwa sai muka ga ƴan bindiga sun riga sun zagaye ƙauyen."
Ya ci sa'a ba a tafi da shi ba, amma yana cikin damuwa sosai saboda an tafi da matansa biyu da kuma wasu ƴaƴan nasa.
"Rayuwata ba ta da wani amfani idan har iyalina ba su tare da ni," in ji shi.
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya je ƙauyen na Kurmin Wali kwana uku bayan harin, inda ya yi alƙawarin za a kafa sansanin soji, da gina asibiti da kuma samar da hanya zuwa ƙauyen. Haka nan ya sanar da bayar da tallafi ga waɗanda lamarin ya shafa.
"Ba za mu iya kwashe su daga ƙauyen ba, saboda dole ne za su ci gaba da zuwa gonakinsu...amma domin kare su a nan gaba, wajibi ne a samar da sansanin sojoji a tsakanin ƙauyen da dajin Rijana," kamar yadda ya bayyana wa BBC.
Ya kuma ce jami'an tsaro na ci gaba da ƙoƙarin ganin sun ceto mutanen da aka sace.
"Lokacin da muka tattauna (da mazauna ƙauyen), na jaddada musu cewa muna tare da su...ba za mu bari a cutar da kowannensu ba," in ji Uba.










