Hanyoyi uku da ƴan bindigan Najeriya ke samun makamai

...

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 5

Muhawara ta kaure kan makamai, musamman bindigogi da ƴan fashin daji ke amfani da su a Najeriya, bayan wasu hotuna a shafukan sada zumunta sun nuna wani ɗan fashi dauke da bindiga ƙirar TAR-21/X95 bullpup wadda ta fi AK47.

Wannan ya sanya mutane na nuna fargaba kan irin munanan bindigogin da ƴan bindigar ke amfani da su da kuma dora ayar tambaya kan inda suke samo su.

Ƴan bindiga sun kwashe kusan shekara 10 suna ƙaddamar da hare-hare a arewa maso yammacin Najeriya, inda suke kashe mutane da kuma garkuwa da wasu domin neman kuɗin fansa.

Baya ga kisa da garkuwa da mutane, ƴan bindigan sun yi ƙaurin suna wajen satar ɗalibai a makarantu.

A baya-bayan nan ana zargin ƴan bindigan da sace ɗalibai mata 25 a jihar Kebbi da kuma ɗalibai da malamai sama da 300 a jihar Neja, ciki har da yara ƴan ƙasa da shekara shida.

Yayin da aka ceto yaran da aka sace a Kebbi, a jihar Neja yara 100 ne aka ceto bayan kimanin 50 da suka kuɓuta tun da farko, yayin da har yanzu sama da 150 ke hannun masu garkuwar da su.

Matsalar ta fi ƙamari ne a jihohin Zamfara, Katsina, Sokoto, Kaduna, Neja da kuma Kebbi, inda ayyukan ƴan bindigan suka yi sanadiyyar kisan dubban mutane da tarwatsa da dama daga muhallansu.

Lamarin ya durƙusar da noma, wanda shi ne ginshiƙi a tattalain arziƙin mazauna jihohin.

Masanin tsaro a yankin Sahel, kuma shugaban kamfanin Beacon Consulting mai nazari kan tsaro, Kabiru Adamu ya bayyana wa BBC cewa akwai manyan hanyoyi uku da ƴan bindigan na Najeriya ke samun makaman da suke amfani da su.

Shigowa daga ƙasashen waje

Kan iyakar Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Masana sun daɗe suna bayyana kwararowar makamai zuwa cikin Najeriya a matsayin daya daga cikin abubuwa da ke iza wutar rashin tsaro a ƙasar.

Wani rahoton cibiyar bincike ta Majalisar Dinkin Duniya kwance ɗamara ya ce "safarar makamai ta haramtacciyar hanya da shigowar haramtattun kuɗi na da alaƙa mai ƙarfi da iza wutar laifukan da ke barazana ga wanzuwar ƙasar."

Kabiru Adamu ya ce "ana shigowa da makamai ta iyakokin Najeriya ta ruwa ko ta ƙasa ko kuma ta sama daga ƙasashe daban-daban".

Ya ƙara da cewa kusan ana shigowa da makami cikin Najeriya daga dukkanin manyan ƙasashen duniya zuwa cikin kasar.

Sai dai ya ce abu ɗaya da suka lura da shi, shi ne ba a cika ganin makamai ƙirar Amurka ba.

Ya bayyana cewa irin makaman da ke shigowa ta wɗannan hanyoyi sun haɗa da AK-47 da dangoginta da bindigar G3 da ma wasu manya-manya.

"Irin waɗannan makamai sun fi fitowa ne daga nahiyar Turai da Asia da kuma ƙasashe na kusa-kusa kamar Turkiyya da sauran su.

"Tsaron iyakokinmu na da rauni shi ya sa akan iya bayar da cin hanci kai-tsaye wajen shigo da makaman, a cewar Adamu.

Sai dai ya nuna cewa ba kai-tsaye ƴan bindigan ke samun makaman daga ƙasashen da ake ƙera su ba.

"Ba ma tunanin cewa kai tsaye ne ƙasashen ke damƙa wa ƴan bindiga waɗannan makaman, suna samun su ne ta ɓarauniyar hanya wadda ake bi ana safarar makamai da mutane," kamar yadda ya yi bayani.

Masanin tsaron ya bayyana cewa duk da hukumomi na ƙoƙari wajen daƙile matsalar, amma "bai fi kashi ɗaya cikin 10 na waɗannan makamai ake samun nasarar hana shiga da su ƙasar ba."

Fashi a hannun jami'an tsaro

Ƴan bindiga sun kai hari a gidan yarin Kuje da ke kusa da Abuja, babban birnin Najeriya a watan Yulin 2022

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ƴan bindiga sun kai hari a gidan yarin Kuje da ke kusa da Abuja, babban birnin Najeriya a watan Yulin 2022

Hanya ta biyu da masanın ya bayyana a matsayin ta samun makamai ga ƴan bindiga ita ce fashi ko sata ko ƙwacewa daga hannun jami'an tsaro.

Wannan na faruwa ne sanadiyyar hare-hare da ƴan bindigan kan kai a kan sansanoni ko kuma jami'an tsaro masu aikin tabbatar da doka.

Kabiru Adamu ya ce akwai wasu nau'in bindigogi da jami'an tsaron Najeriya ke amfani da su, kuma idan aka gan su a wurin ƴan bindiga to "yawanci an samo su ne daga rumbun adanar makamai ko kuma ta hanyar wasu gurɓatattun jami'an tsaro, kamar yadda bincike ya tabbatar."

Kabiru Adamu ya ce "Akai-akai ƴan bindiga na kai hare-hare kan sansanonin soji ko ƴansanda da sauran jami'an tsaro suna kwashe makamai.

Ya ce ta haka ne ƴan bindigan ke samun makamai daga rumbun makaman gwamnatin Najeriya.

Irin bindigogin da ƴan bindigan ke samu daga rumbunan makaman Najeriya su ne bindigar MAT-49 kirar ƙasar Faransa da Heckler G3 ta ƙasar Jamus.

Sai dai ya ƙara da cewa akwai wasu lokutan da akan samu jefi-jefi masu safarar makamai suna samar da MAT-49 ga ƴan bindiga.

Ƙerawa a gida

Mutum riƙe da bindiga ƙirara katako

Asalin hoton, Getty Images

Baya ga shigowa da makamai ta ɓarauniyar hanya da ƙwacewa daga jami'an tsaron Najeriya, wata babbar hanyar da ƴan bindiga a Najeriya ke samun makamai ita ce hanyar ƙerawa a cikin gida.

Sau da yawa jami'an tsaro kan kama bindigogi ƙirar gida a lokacin da suka kai samame ko kuma suka yi artabu.

Yawancin makaman da ake haɗawa a gida sun haɗa da bindigar fistol da kuma AK-47 da ake kwaikwayo da kuma harba-ka-ruga, wadanda ake amfani da su wajen rikice-rikice a tsakanin al'umma.

"Yawancin makaman da ƴan bindiga ke amfani da su wadanda ake ƙerawa a cikin gida ƙanana ne, ko kuma AK-47," in ji Kabiru Adamu.