Gaske ne wasu 'yan siyasa na da hannu a matsalar tsaron Najeriya?

Asalin hoton, Getty Images
Tun bayan kalaman da tsohon hafsan hafsoshin Najeriya ya yi cewa ƴan siyasar ƙasar na da hannu a matsalar tsaro, ƴan Najeriya ke tambaya dangane da gaskiyar al'amarin.
Janar Lucky Irabor, mai ritaya, a wata hira da aka yi da shi a gidan talbijin na Channels, ya bayyana cewa matsalolin tsaron da Najeriyar ke fama da su a yanzu haka, na da nasaba da yadda wasu yan siyasa ke daukar nauyin abubuwan da ke faruwa don cimma wata manufa tasu ta siyasa.
Ya yi zargin cewa akwai masu shigar burtu a gwamnati, da ke nuna tamkar suna bayar da gudummuwa wajen yaki da matsalar tsaro, amma kuma su ne ruwa su ne tsaki wajen haddasa tashe-tashen hankali masu nasaba da kisa da satar jama'a a fadin kasar.
Janar Lucky Irabor ya kuma ce galibin matsalolin tsaron da kasar ke fama da suna da nasaba da yadda wasu 'yan siyasa ke daukar nauyin wadannan masu kai hare-hare.
Kalaman tsohon babban hafsan tsaron Najeriyar Janar Lucky Irabor na zuwa a irin wannan lokaci da matsalar tsaro ta dabaibaiye kusan ko'ina a jahohin arewacin kasar.
A watan Nuwamban da ya gabata ma babban mashawarcin shugaban Najeriya a bangaren sadarwa Daniel Bwala ya ce nan gaba kadan gwamnatin kasar za ta fallasa sunayen masu daukar nauyin ayyukkan ta'addanci.
Akwai ƙamshin gaskiya - Kabiru Adamu
Masana lamurran tsaro sun ce akwai alamun ƙamshin gaskiya a wadannan kalamai masu kusanci da juna.
Akwai dai zarge-zarge masu karfi da masana lamurran tsaro suka dade suna yi na cewa galibin tashe-tashen hankali a shiyyoyin arewa maso gabas da arewa maso yamma na da sa hannun 'yan siyasa.A hirarsa da BBC Dakta Kabiru Adamu shugaban kamfanin harkokin tsaro na Beacon Security and Intelligence Limited, ya ce akwai shaidu cikakku da suka tabbatar da haka.
Kazalika, wasu 'yan siyasar Najeriyar sun bayyana cewa ba za a rasa baragurbin masu daukar nauyin 'yan ta'adda ba.
Martanin ƴan siyasa
Sai dai a cewar Sanata Umaru Tsauri ya kamata gwamnati ta fallasa sunayen 'yan siyasar da ake zargi.
"Ai lokaci ya yi da ya kamata gwamnati ta bayyana sunan ƴan siyasar da suke ɗaukar nauyin ƴan ta'adda domin Najeriya ta gaba da komai. Mun daɗe muna ji ana faɗin haka to yanzu lokaci ya yi da za a faɗi sunayensu."
Wannan zargin dai na zuwa ne daidai lokacin da galibin jihohin arewacin kasar ke fuskantar farmakin 'yan bindiga ɗaya bayan ɗaya.
Hakan ne kuma ya sa shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu sanya dokar ta-baci a bangaren tsaro inda bayan ajiye aiki da ministan tsaron kasar Muhammad Badaru Abubakar ya yi, cikin kwana daya shugaban ya maye gurbinsa da tsohon hafsan hafsoshin tsaron kasar Janar Christopher Musa mai ritaya, wanda yanzu yake jiran amincewar majalisar dattawan kasar.











