'Ba zan huta ba, sai mun ceto mutanenmu da aka sace'

Gwamna Uba Sani

Asalin hoton, X/UBA SANI

Bayanan hoto, Gwamna Uba Sani
Lokacin karatu: Minti 3

Gwamnan jihar Kaduna Malam Uba Sani ya ce gwamnatinsa za ta yi duk abin da ya dace domin ceto mutanen da aka yi garkuwa da su a ƙauyen Kurmin Wali da ke ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar.

Gwamnan ya ce yana bibiyar ƙoƙarin da jami'an tsaro ke yi game da batun, kuma ba zai gajiya ba har sai an yi nasarar ceto dukkan mutanen da aka sace.

A ranar Lahadi wasu mahara suka shiga ƙauyen Kurmin Wali inda rahotanni ke cewa sun yi garkuwa da mutane fiye da 170 tare da jefa al'ummar yankin cikin ruɗani.

Da farko ƴansanda da jami'an gwamnatin jihar Kaduna sun musanta faruwar lamarin amma daga baya suka fitar da sanarwar da ke tabbatar da shi, duk da cewa kawo yanzu babu haƙiƙanin bayani kan ko mutane nawa ne aka sace a ƙauyen.

Amma a hirar shi da BBC a Kaduna, gwamna Uba Sani ya ce gwamnatinsa ta karkata ne ga aikin ceto mutanen, don haka sanin yawan su wani abu ne da zai iya zuwa daga baya domin a cewarsa masu ''siyasantar'' da batun tsaro ne ke mayar da hankali kan yawan mutanen da aka sace.

''Mu a jihar Kaduna, ba mu siyasantar da batun tsaro, waɗanda ma suka mayar da batun na siyasa, za su ji kunya'' in ji gwamna Uba Sani.

Dangane da ƙoƙarin yin rufa-rufa a lokacin da labarin sace mutanen ya fito kuwa, gwamnan ya ce a iya sanin shi hukumomin tsaro sun yi aikin su ne da zuciya ɗaya kuma ya gamsu da ƙoƙarin da suke yi domin ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.

Ya ƙara da cewa ''Na zauna da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu, na zauna da ministan tsaro Janar Christopher Musa wanda ɗan Kaduna ne, na zauna da DG SSS da kuma shugaban ƴansandan Najeriya, domin da su ne za mu haɗa kai cikin gaggawa a dawo mana da mutanenmu da aka sace.''

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Gwamna Uba Sani ya kuma jaddada cewa duk da dai kawo yanzu waɗanda suka sace mutanen ba su kira ko sun gindaya abin da suke neman a yi masu ba, gwamnatinsa na da tsari na rashin biyan kuɗin fansa, domin haka ya kore wannan batu.

''Mu muna da tsari, ba mu biyan kuɗin fansa,'' In ji gwamnan.

Ya kuma buƙaci jama'ar jihar su taimakawa jami'an tsaro da bayanai domin samun nasarar aikin su na ceto mutanen da aka sace. ''Al'umma su tashi tsaye su ci gaba da ba jami'an tsaro haɗin kai, domin shi harkar tsaro gwamnati kaɗai ba ta iya yin shi''

Ya kuma bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa ba za ta gajiya ba har sai ta yi nasarar ceto dukkan mutanen da aka sace. ''A matsayina na gwamna, ba zan kwanta ba, ba zan bacci ba da yardar Allah, za mu tsaya tsayin daka mu ga kowa ya dawo gida lafiya ba tare da wata matsala ba.''

Ɗaya daga cikin waɗanda aka sace a harin na Kumin Wali, Maigirma Shekarau ya ce ana cikin tafiya da su ne ya samo damar sulalewa ya ɓoye a wani gida ya ɓoye har ƴanbindigar suka tafi.

"Yadda abin ya faru shi ne muna cikin coci ne sai muka ji ana ta ihu. Da muka fito sai muka ga ƴanbindiga sun kewaye garin, sai suka kwashe suka shiga daji da mu," in ji shi.

Maigirma ya ce da suka fara tafiya, sai "suka tsaya suka fara mana tambayoyi da duka. Bayan sun gama tambayoyin ne sai muka ci gaba da tafiya."

Ya ce da suka isa wani gari da ake kira Sabon Gida, "dama sun kori mutanen garin babu kowa. A nan ne na samu dama na sulale na shiga wani ɗaki tare da wata yarinya da na riƙe. Bayan kusan awa biyu sai na fito na nemo hanya na dawo gida" in ji Magirma.

Shi ma ya tabbatar da adadin waɗanda aka kwashe, sannan ya ƙara da cewa suna cikin tashin hankali, "domin ba mu san halin da ƴan'uwanmu suke ciki ba."