Abin da ya sa na koma aji biyu a jami'a - Sarki Sanusi II

Muhammadu Sanusi II
Lokacin karatu: Minti 6

A wani abu da ba a saba gani ba, Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, wanda kuma tsohon shugaban Babban Bankin Najeriya ne ya koma makaranta, inda ya fara karatun digiri na farko a fannin shari'a a jami'a mallakin jihar Kano.

Tun bayan komawarsa, al'umma sun yi ta mamakin yadda zai ɗauki karatu a wata jami'a da ke cikin jihar Kano, watanni bayan kammala digirin-digirgir daga wata jami'a a birnin Landan da ke Birtaniya.

Sai dai hotunan da suka karaɗe shafukan sada zumunta da ke nuna sarkin a cikin ajin ɗaukar karatu sun janyo cece-ku-ce sosai tsakanin al'umma.

Sarautar Sarkin Kano na daga cikin mafiya daraja, wadda kuma ake girmamawa a ƙasar Hausa da kuma fadin Najeriya.

Ba Najeriya kawai ba, Sanusi II, wanda shi ne Khalifan mabiya ɗariƙar Tijjaniya a ƙasar na da ɗimbin tasiri a ƙasashe maƙwafta, musamman na yammacin nahiyar Afirka.

Duk waɗannan na daga cikin abin da ya sa wasu ke ganin basaraken ya yi ƙasaitar da ta wuce ya shiga cikin ɗalibai masu ƙarancin shekaru domin yin karatun digiri na farko.

Sai dai a tattaunawarsa da BBC ranar Alhamis bayan kammala ɗaukar karatu a jami'ar ta Northwest University da ke birnin Kano, Muhammadu Sanusi II ya ce ya daɗe yana sha'awar karanta harkar shari'a.

Karatu - daga haihuwa ne har mutuwa

Sarki Sanusi na biyu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sarki Sanusi na biyu

Sarkin ya bayyana cewa duk da cewa ya riga ya samu digirin digirgir (PhD) a fannin shari'a, har yanzu yana da sha'awar yin karatun lauya.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A cewarsa, samun wannan dama daga Jami'ar Northwest wata ni'ima ce da bai kamata ya watsar ba.

"Duk da cewa na yi PhD a shari'a, ina da sha'awar na karanci lauya. Wannan dama ce da na samu, kuma kullum ina faɗa cewa shekaru ko muƙami bai kamata su hana mutum neman ilimi ba," in ji Sarki Sanusi II.

Ya ƙara da cewa duk lokacin da aka samu damar ƙarin ilimi, ya dace a rungume ta, domin ilimi ba ya ɓata lokaci ko ƙoƙari.

Da aka tambaye shi abin da ya ƙara masa sha'awar karatun wannan fannin, Sarkin ya bayyana cewa doka ita ce ginshiƙin rayuwar al'umma.

"Dukkanin tsarin ƙasa da tsarin al'umma ba ya yiwuwa sai da shari'a. Idan babu doka, da oda, masu ƙarfi za su yi abin da suka ga dama, marasa ƙarfi kuma ba su da haƙƙi, babu inda za su je a bi musu haƙƙinsu," kamar yadda Sarki Sanusi ya bayyana.

A cewarsa, kasuwanci da mu'amala da aure da ma zaman lafiya gaba ɗaya ba za su yiwu ba idan babu doka. "Saboda haka fahimtar doka na daga cikin abubuwan da suka fi muhimmanci a rayuwar kowane mutum, ba tare da la'akari da matsayinsa ba." in ji Sarkin.

Me ya sa Sarki Sanusi II ya zaɓi jami'a a Najeriya?

Game da dalilin zaɓar jami'a a cikin gida maimakon waje, Sarkin ya bayyana cewa bai ga wani bambanci a ingancin ilimi ba.

"Jami'o'inmu babu abin da ya same su. Malaman suna nan, ƙundin tsarin karatun duka ɗaya ne," ya ce.

"Ko a lokacin da na je Birtaniya na kammala digiri na na uku, hutun karatu aka bani daga sarauta, wanna kuma ina sarauta ta a Kano, ba ajiya sarautan nayi ba,lokacin karatu, da safe ina zuwa aji, da yamma kuma ina zaman fada, ina gudanar da harkokin masarauta ba tare da wata tangarda ba." in ji shi.

Komawar Sarkin Kano zuwa aji ya wuce neman ilimi kawai. A cewarsa, akwai darasi a cikin abin da mutum yake aikatawa.

"Na zo ne domin na koya, amma kuma a cikin abin da mutum ya aikata akwai darasi da mutane za su ɗauka. Kowa da abin da zai fahimta," in ji shi.

Ya tuna cewa tun a shekarar 1978 ya fara karatu a Jami'ar Ahmadu Bello (ABU), inda a lokacin yake aji biyu. Yau kuma, bayan kusan shekaru 47, ga shi ya sake zama ɗalibi. Wannan, a ganinsa, hujja ce cewa neman ilimi ba ya da iyaka.

"Duk mutumin da yake ganin ya fi ƙarfin ya je ya nemi ilimi, ba zai yi shi ba. Jahilci ba ya tafiya sai mutum ya saukar da kansa ya je ya nemi ilimi," ya ƙara da cewa.

Sarkin ya jaddada cewa ilimi ba ya faɗuwa a ƙasa, ko a wane lokaci aka same shi. Ya kawo misali da karatun shari'a da ya yi a Sudan, wanda a wancan lokaci wasu ke ganin ba shi da alaƙa da harkar banki. Amma daga baya, lokacin da ya zama Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), wannan ilimi ya taimaka masa sosai wajen fahimtar dokoki da tsare-tsaren kuɗi.

Sarkin Kanan ya jaddada cewa rayuwa tana da awa 24 a rana, amma mutane da dama na ɓata lokacinsu.

"Daga haihuwa har zuwa kabari, mutum ba ya taɓa girma da neman ilimi," ya ce.

Tarihin Muhammadu Sanusi II

An haifi Muhammadu Sanusi II a jihar Kano da ke arewacin Najeriya a ranar 31 ga watan Yuli a shekarar 1961.

Sanusi II ya yi karatun firamare ne a makarantae St. Annes da ke Kaduna, sannan ya koma King's College da ke Legas, inda ya yi sakandare tsakanin 1973 zuwa 1977.

Ya samu digirinsa na farko a fannin tsimi da tanadi a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya a 1981, sannan ya yi digiri na biyu a shekarar 1983, inda ya koyar da wani ɗan lokaci.

Ya koma Jami'ar Khartoum da ke Sudan, inda ya karanci nazarin addinin musulunci.

Bayan ya koyar da tsimi da tanadi tsawon shekara biyu a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, sai ya soma aikin banki a shekarar 1985 tare da Icon Limited, daga bisani kuma yai aiki tare da bankin UBA da kuma First Bank.

Ya kai matsayin Babban Darakta a bankin First bank a watan Janairun shekarar 2009, daga bisani kuma aka naɗa shi gwamnan babban bankin Najeriya na 10 a watan Yunin shekarar 2009.

Sanusi II ya yi karatun digirinsa na uku wato PhD a ɓangaren shari'a a London, inda ya yi nazari a kan "Codification of Islamic Family Law as an Instrument of Social Reform: A Case Study of the Emirate of Kano and a Comparison with the Kingdom of Morocco."

A zamanin Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, shugaban ya dakatar da shi daga matsayin gwamnan Babban Bankin Najeriya a ranar 20 ga watan Fabrairun shekarar 2014 bayan da aka zarge shi da sakaci wajen harkar kuɗi.

Mahaifinsa Muhammadu Lamido Sanusi ya riƙe muƙamin babban sakatare a ma'aikatar harkokin ƙasashen wajen Najeriya, bayan ya riƙe mukamin Jakadan Najeriya a ƙasashen Canada da Belgium da China.

Kuma jika ne ga Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na ɗaya.

Sarauta, tsigewa da komawa sarauta

A ranar 8 ga watan Yunin 2014 ne aka naɗa Sanusi a matsayin Sarkin Kano domin maye gurbin marigayi Ado Bayero, lamarin da ya haifar da taƙaddama har aka yi zanga-zanga a Kano.

Sai dai a ranar 9 ga watan Maris na shekarar 2020, gwamnan jihar Kano na wancan lokacin, Umar Ganduje ya tsige sarkin a matsayin Sarkin Kano.

A lokacin ne gwamnatin jihar ta naɗa Aminu Ado Bayero a matsayin wanda zai maye gurbinsa, sannan a wata wasiƙa, Sarki Sanusi II ya amince da cirewar.

Gwamnatin jihar ta mayar da sarkin zuwa jihar Nasarawa, duk da cewa ya so ne a kai shi Legas tun da farko.

Daga baya ya koma birnin na Legas da zama.

A wata sabuwar, a ranar 23 ga Mayun 2024, bayan Abba Kabir Yusuf ya lashe zaɓen gwamnan jihar, ya sake naɗa Muhammadu Sanusi II a matsayin sarki a karo na biyu, tare da rushe sauran sababbin masarautu.