Mu kwana lafiya
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Haruna Kakangi, Ibrahim Yusuf Mohammed, Aisha Babangida da Ahmad Bawage
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.

Babban kamfanin samar da lantarki na Ukraine ya ce halin da fannin samar da makamashi na ƙasar ke ciki na ci gaba da munana, bayan hare-haren baya bayan-nan da Rasha ta kai da jirage marasa matuka da makamai masu linzami.
Kamfanin ya ce ana gyara cikin gaggawa a wasu daga cikin tashoshin samar da makamashi.
Ƙungiyar Tarayyar Turai za ta aika wa Ukraine ɗaruruwan injunan janaretoci domin dawo da lantarki a asibitoci da matsugunai da kuma wasu muhimman wurare.
Ukraine ta ce ta kai hari kan wani wurin ajiye man fetir wanda ke samar wa sojojin Rasha mai.

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Hukumar kare hakkin ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi kiran a gudanar da bincike cikin gaggawa kan yadda aka yi amfani da karfi wajen fatattakar masu zanga-zangar kin jinin gwamnati a Iran.
Ƙasashe 25 cikin 47 da ke hukumar sun amince da matakin tsawaita lokacin da aka ba masu bincike, domin su duba zargin cin zarafin ɗan'adam.
Yayin buɗe wani taron gaggawa da aka yi a Geneva, shugaban hukumar ya buƙaci mahukunta a Iran da su sake nazari, su janye tare da kawo karshen cin zalin da suke yi.

Asalin hoton, Wiltshire Police
Wani ɗan Birtaniya ya amsa aikata laifukan cin zarafin lalata da dama a kan matarsa a tsawon shekaru 13.
Philip Young wanda ya fito daga yankin kudu maso gabashin Ingila ya amsa laifin yin fyaɗe, da kuma bai wa matarsa mai suna Joanne Young wani magani domin ya fi ƙarfinta - sai dai a yanzu sun rabu da matar.
An kuma tuhumi wasu maza huɗu da laifin yin lalata da Joanne Young - ciki har da fyaɗe da cin zarafi - sai dai sun musanta duka zarge-zargen.
Mutum na biyar zai gurfana a gaban kotu nan gaba kaɗan.

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin tallafa wa jami'o'i a faɗin ƙasar nan, don bunƙasa harkokin noma da samar da ababen more rayuwa, a wani ɓangare na koƙarin karfafa samar da abinci da rage talauci da kuma cigaban tattalin arziki.
Karamin ministan aikin gona, dakta Aliyu Abdullahi ne ya bayyana haka, lokacin da ya karɓi bakuncin wata tawaga daga jami’ar ilimi ta tarayya da ke Kontagora, inda ya ce tallafin da ma'aikatar su za ta bai wa manyan makarantu zai mayar da hankali ne wajen koyar da sana’o’in hannu da horo kan aikin gona da sauransu.
Ya ce haɗin gwiwar da za su yi da jami'o'i za ta fi mayar da hankali kan samun dabarun aikin gona na zamani, inda za a yi amfani da fasaha don inganta samun riba da kuma ɗorewar ɓangaren.
Ministan ya kuma nuna damuwa kan raguwar malamai da za su koyar da aikin gona, inda ya ce lamarin ya sanya an kafa wata ƙungiyar manoma matasa, da zimmar tabbatar da cewa an kwaɗaita wa matasa harkar noma ta hanyar horo na zamani.

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Ƴansanda a jihar Telangana da ke Indiya na bincike kan kashe ɗaruruwan karnukan da ba su da ubangida a watan da ya gabata.
An ruwaito mutuwar sama da karnuka 350. An kama mutum tara zuwa yanzu.
Masu gwagwarmaya sun ce an saka wa karnukan guba ko kuma yi musu allurai, sai dai ƴansanda sun ce suna jiran sakamakon bincike.
Mazauna yankin sun ce kashe karnukan yana alaƙa da alkawura da ƴan takara suka yi lokacin yaƙin neman zaɓe cewa za su kakkaɓe karnukan da ba su da masu shi, har ma da birrai.

Asalin hoton, AFP
Gwamnatin ƙasar Japan ta dakatar da ayyukanta a cibiyar samar da makamashin nukiliya mafi girma a duniya ƴan sa'o'i kaɗan bayan da ta fara aiki.
An dai fara aiki a cibiyar samar da makamshin nukiliya mai lamba shida ne ranar Laraba wanda ita ce tashar nukuliya ta farko da aka sake buɗewa tun bayan bala'in da ya afku a Fukushima a shekarar 2011.
Ƙasar Japan ta rufe duka tashoshin nukiliyarta guda 54 bayan wata girgizar ƙasa mai ƙarfin 9.0 ta haifar da fashewa a cibiyar nukiliya ta Fukushima shekaru 15 da suka gabata, lamarin da ya haddasa bala'in nukiliya mafi muni a tarihi.
Tun da farko dai an shirya buɗe tashar nukiliyar ce a ranar Talata, amma an mayar da shi baya saboda tangarɗar na'ura.
A wata mai zuwa ne dai ake sa ran tashar za ta fara aiki gadan-gadan.

Asalin hoton, Joyce Liu / BBC
Fiye da yaran Sudan miliyan 8 ne suka rasa kusan kwanaki 500 na maklaranta tun bayan ɓarkewar yakin basasa a ƙasar a shekarar 2023.
A cewar ƙungiyar bayar da agaji ta Save the Children, kusan rabin adadin yaran da ke zuwa makaranta a ƙasar ke nan.
Da take magana yayin wani taron manema labarai , shugabar ƙungiyar Save the Children Inger Ashing ta ce, '‘ƙasashen duniya na gazawa wurinj taimakawa yaran Sudan’'.
Ƙungiyar ta ce wannan rufewar makarantun na ɗaya daga cikin mafi tsayi, wanda ya zarce rufewar COVID19 a shekarar 2019.
Jihar Darfur ta Arewa ce yankin da lamarin ya fi shafa inda kashi 3 cikin 100 kacal na makarantu sama da 1,100 ne aka buɗe.
Yammacin Kordofan, Darfur ta Kudu da kuma yammacin Darfur na biye da mafi ƙarancin makarantu da ke aiki da kashi 15%, da13% da 27%, bi da bi.
"Duk inda na je yayin ziyarar na, na ji saƙo iri ɗaya daga yara: suna so su kasance a makaranta," in ji Ashing.
An rufe yawancin makarantun da abin ya shafa, sun lalace ko kuma a halin yanzu ana amfani da su a matsayin matsugunan iyalai da suka yi gudun hijira.

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar NNPP, inda ya ce ya ɗauki matakin ne saboda ɓarakar da ya ce ta yi wa jam'iyyar katutu.
Abba ya ce rikicin cikin-gida da ya dabaibaye jam'iyyar ta NNPP ya yi yawa, wanda a cewarsa ya sa ya ɗauki wannan matakin na ficewa domin fifita buƙatun al'ummar Kano.
Ficewar na ƙunshe ne a cikin a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Juma'a.
A cikin sanarwar, ya ce gwamnan ya aika wasiƙar ficewa daga jam'iyyar NNPP zuwa shugaban jam'iyyar na mazaɓar Diso-Chiranci ta ƙaramar hukumar Gwale.
Latsa nan don karanta cikakken labarin...

Asalin hoton, Getty Images
Babban layin wutar lantarki na Najeriya ya lalace karon farko a shekarar 2026 a yau Juma’a, ƴan makonni kaɗan bayan wani abu makamancin haka ya faru a ranar 29 ga watan Disamba, 2025, wanda ya haifar da katsewar wutar lantarki a sassa daban-daban na faɗin ƙasar.
Lantarkin da ake samar wa ya ragu sosai daga megawatts sama da 4,500 zuwa ƙasa da megawatts 24 cikin yan sa'o'i kaɗan.
Zuwa yanzu dai ba a iya tantance musabbabin faɗuwar layin wutan ba, inda ake jiran samun cikakken bayani daga jami’an kamfanin rarraba wutan lantarki na ƙasa (TCN).

Asalin hoton, Getty Images
Wata kotu a Afirka ta Kudu ta yi watsi da ƙarar da hukumar tarihi ta ƙasar ɗaukaka ta na neman dakatar da sayar kayayyakin tarihi daban-daban da ke da alaƙa da marigayi Nelson Mandela.
Kayayyakin guda 70 sun haɗa da makullin ɗakin gidan yari da ke tsibirin Robben, inda aka ɗaure Mandela na tsawon shekara 18 daga cikin shekaru 27 da ya yi a kurkuku, da tabarau nau'in Aviator da ɗaya daga cikin shahararrun rigunansa. Daman an shirya fitar da su zuwa Amurka ne don yin gwanjo su.
Kayayyakin mallakar babbar ƴarsa, Makaziwe Mandela da Christo Brand, wani mai kula da fursunoni a tsibirin Robben a lokacin da Mandela ke tsare.
A ƙoƙarin da suke yi na dakatar da sayar da kayan, hukumomi sun ce suna daga cikin kayayyakin tarihi na ƙasar, don haka a bisa doka akwai kariya daga fitar da su zuwa ƙasashen waje.
Ɗiyar Mandela ta so ta yi amfani da kudaɗen kayan ne wajen gina wani lambun tunawa da marigayi tsohon shugaban ƙasar a garin Qunu da ke yankin Mthatha na lardin Eastern Cape.

Asalin hoton, Ukraine Emergency Services
Hukumar ba da agajin gaggawa ta Ukraine ta ce mutane huɗu ciki har da wani yaro ɗan shekara biyar ne suka mutu a wani harin da jiragen yaƙin Rasha suka kai a Ukraine.
Ta ce an kai harin ne a a ƙauyen Cherkaske, a gundumar Kramatorsk a gabashin Ukraine.
Ta kuma ƙara da cewa jami’an agajin gaggawa sun tsamo gawarwakin mutane biyu ciki har da yaro daya daga ɓaraguzan wani gidan da ya ruguje.
Ofishin mai shigar da ƙara na yankin Donetsk ya bayyana cewa biyu daga cikin mutanen da aka kashe wani mutum ne mai shekaru 32 da ɗansa mai shekara 5, yayin da wasu mutane biyar suka jikkata - ciki har da mahaifiyar yaron da ya mutu.

Asalin hoton, US Embassy in Nigeria
Amurka da Najeriya sun yi taron farko a Abuja domin ƙarfafa hadin gwiwar tsaro da kare fararen hula daga ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai ƴanbindiga.
Taron dai an yi shi ne da nufin tabbatar da cewa dukkan mabiya addinai za su iya gudanar da addininsu cikin aminci.
Hakan ya biyo bayan ayyana Najeriya a matsayin ƙasar da ake da damuwa a kanta, musamman saboda kisan kiyashin da ake zargin ana yi wa kiristoci, ikirarin da hukumomin Najeriyar suka musanta.
Amurka ta yi maraba da ƙoƙarin Najeriya na magance matsalar rashin tsaro, musamman a jihohin Arewa ta tsakiya.
Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu ne ya jagoranci tawagar Najeriyar da ta ƙunshi ma’aikatu da hukumomi 10, yayin da mataimakiyar sakataren harkokin wajen Amurka Allison Hooker ta jagoranci tawagar Amurka da ke da wakilaiu daga hukumomin tarayya takwas.
Sanarwar hadin gwiwa da aka fitar ranar Alhamis ta jaddada ƙudurin gwamnatocin biyu na tabbatar da ƴancin addini da kare ƴancin faɗin albarkacin baki da gudanar da taron lumana.
Sanarwar ta ƙara da cewa, ‘’Tawagar ta Amurka ta godewa Najeriya kan matakan gaggawa da ta ɗauka na ƙarfafa tsaro ga al’ummomin Kirista da mabiyan sauran addinai da ke cikin haɗari sakamakon ayyukan ta'addanci.''
Ƙasashen biyu dai na musayar bayanan sirri domin tunkarar matsalar ta'addanci daga ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba miliyoyi da muhallansu a arewacin Najeriya.

Asalin hoton, Kebbi State government
Fadar shugaban Najeriya ta sanar da cire sunan tsohon gwamnan jihar Kebbi, Usman Sa’idu Dakingari a matsayin wanda aka naɗa mukamin jakadan Najeriya a ƙasar Turkiyya.
Wata sanarwa da ta fito daga mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru Bayo Onanuga a jiya Alhamis, ta ce shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin jakadu huɗu da majalisar dattawa ta tabbatar a watan Disamban da ya gabata.
Sanarwar ta ce an naɗa Ambasada Ayodele Oke jakadan Najeriya a Faransa da Kanar Lateef Are zuwa Amurka, da Ambasada Amin Dalhatu, tsohon wakilin Najeriya a Koriya ta Kudu, a matsayin jakada zuwa Burtaniya.
An sanya sunan Dakingari a matsayin jakadan da aka naɗa a Turkiyya.
Amma da safiyar Juma'a, wata sanarwa ta sake fitowa daga fadar shugaban ƙasa inda ta ce "Shugaba Tinubu ya amince da naɗa jakadu uku, amma har yanzu babu jakada zuwa Turkiyya".
Sanarwar dai ba ta bayar da wani dalili da ya sa ba a sanya sunan Dakingari ba.
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da shugaba Tinubu ke shirin kai ziyarar aiki ƙasar Turkiyya a ƙarshen wannan makon.

Asalin hoton, FABRICE COFFRINI/AFP via Getty Images
Amurka ta fice a hukumance daga Hukumar lafiya ta duniya (WHO), inda ta hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta rasa ɗaya daga cikin manyan masu bam ta tallafi.
Shugaban Amurka Donald Trump ya rattaba hannu kan wata doka mai nuna alamar janyewar shekara guda da ta gabata, bayan da ya soki hukumar da cewa ta kasance mai “kishin China” a lokacin ɓarkewar cutar ta Korona.
Ma'aikatar lafiya ta Amurka ta ce ta ɗauki wannan matakin ne saboda abin da ta kira yadda hukumar da tafiyar da batun cutar, rashin iya yi wa tsare-tsarenta garambawul da kuma tasirin siyasa daga ƙasashe mambobin hukumar.
Hukumar ta WHO ta yi watsi da wannan iƙirarin kuma daraktan ta Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana janyewar a matsayin asara ce ga Amurka da duniya.
Hukumar ta yi nuni da ƙoƙarin da take yi a duniya na yaƙi da cutar shan inna, da taimakon da ta ke bai wa masu cutar HIV, da mace-macen mata masu juna biyu, da yarjejeniyar da ta ƙulla na yaki da shan taba sigari.

Asalin hoton, EPA
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce tattaunawar da ake yi tsakanin ɓangarorin uku da ke gudana a Hadaddiyar Daular Larabawa a yau za ta mayar da hankali ne kan matsayin yankin Donbas na gabashin Ukraine.
"Batun Donbas muhimmin abu ne" ya shaida wa manema labarai ta sakon murya.
Da yake magana game da tattaunawar da za a yi a Abu Dhabi ya ce: "Wannan mataki ne da mu ke fatan zai kawo ƙarshen yaƙin - amma abubuwa daban-daban na iya faruwa."
Shugaban na Ukraine ya kuma ce ya tattauna batun Donbas da shugaba Trump a Davos jiya.
A cewarsa, shugabannin biyu sun kuma "kammala tattauna batun tabbatar da tsaro" ga Ukraine tare da tattaunawa matakan kariya daga harin makamai masu linzami don kakkabo makamai masu linzami da Rasha ke harba ma ta.
"Ina fatan samun sakamako mai kyau," in ji shi.

Masu shiga tsakani na Rasha da Ukraine da kuma Amurka za su yi wata ganawa ta musamman a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a yau Juma'a, a wani taro da jami'ai suka ce shi ne taro na farko da dukkan ƙasashen uku za su halarta tun bayan da Moscow ta ƙaddamar da mamayar da ta ke yi wa Ukraine kusan shekaru huɗu da suka gabata.
Fadar Kremlin ta tabbatar da cewa jami'an Rasha za su halarci tattaunawar bayan ganawar da shugaba Vladimir Putin ya yi da wakilan Amurka a birnin Moscow.
Rasha ta bayyana wannan tattaunawar a matsayin "mai amfani ta kowane fanni", amma ta ce ba za a iya cimma yarjejeniyar zaman lafiya ta dogon lokaci ba har sai an warware matsalolin da ke tattare da mallakar wasu yankuna.
A taron tattalin arzikin duniya da aka yi a birnin Davos, shugaban ƙasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya soki ƙawayen ƙasashen Turai kan rashin nuna jarumta wajen ɗaukar mataki kan Rasha.

Asalin hoton, Seyi Makinde
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde,ya ziyarci shugaban ƙasa Bola Tinubu, inda ya ce ya kai ziyarar ne domin tattaunawa da shugaban kasa kan "wasu batutuwan da suka shafi mulki" ba na siyasa ba.
Ganawar dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun sauye-sauye a siyasance, gabanin babban zaɓen ƙasar na 2027.
A baya-bayan nan dai wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP da suka haɗa da gwamnoni suka fice daga jam’iyyar zuwa APC, inda suka bar Makinde da wasu tsiraru a jam’iyyar ta adawa.
Da aka tambaye shi ko zai koma APC nan ba da jimawa ba, Makinde ya jadada cewa hankalinsa a kwance ya ke a PDP.
Ya ce ''Hankalina a kwance yake a PDP. Waɗansu abubuwa na iya tasowa a ƙasar nan, inda ake buƙatar a yi watsi da batun ɓangaranci, inda ba zai zama batun wataƙila APC ta yi magana ita kaɗai ko PDP ta yi magana ita kaɗai ba.''
Ya yi nuni da cewa, yayin da shi da Shugaban ƙasar ke jam’iyyun siyasa daban-daban, ci gaban Najeriya ya kasance wani aiki ne da ya kamata duka ƴan kasa su damu da shi ba tare da la’akari da ra'ayin siyasa ba.

Asalin hoton, Getty Images
Amurka ta gabatar da shirinta na gina abin da ta kira "Sabuwar Gaza" inda ta ce za ta sake gina yankin Falasdinawan.
Hotunan sun nuna ɗimbin gine-ginen da ke shimfiɗe a bakin tekun Bahar Rum da kuma gidaje a yankin Rafah, yayin da taswirar da ke bayyana tsarin ci gaban sabbin wuraren zama, noma da masana'antu ga mutane miliyan 2.1.
An gabatar da su ne a yayin bikin rattaba hannu kan kaddamar da sabon kwamitin zaman lafiya na Donald Trump da aka gudanar yayin taron tattalin arzikin duniya a birnin Davos.
"Za mu yi nasara sosai a Gaza. Zai zama gagarumin abin mamaki da ban sha'awa," in ji Trump.
Za a gina sabuwar tashar jiragen ruwa da filin saukar jirgin sama kusa da kan iyakar Gaza da Masar.
Za a raba shirin sake gina zirin ne zuwa matakai huɗu, inda za a fara daga Rafah sannan kuma a hankali a ƙarasa zuwa arewacin birnin Gaza.

Asalin hoton, Getty Images
Manyan jami'an Amurka sun yi wata tattaunawa da daddare a birnin Moscow da shugaba Vladimir Putin kan shirin da Amurka ta tsara na kawo ƙarshen yaƙin Ukraine.
Rahotanni sun bayyan cewa jami'in gwamnatin Rasha, Yuri Ushakov, ya bayyana tattaunawar a matsayin "mai aminci'' - amma har yanzu Rasha na ci gaba da matsa ƙaimi kan batutuwan da suka shafi yankunan da ta mamaye kafin a kai ga batun yarjejeniyar zaman lafiya.
Hotuna sun nuna shugaban na Rasha yana gaisawa da wakilin Trump Steve Witkoff, da kuma surukinsa Jared Kushner a ganawarsu a fadar Kremlin.
Kafin ya nufi babban birnin ƙasar Rasha, Witkoff ya bayyana cewa yana da ƙwarin gwiwa game da yiwuwar cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen rikicin.