Abin da ya sa na fice daga jam'iyyar NNPP - Abba Kabir

Kano

Asalin hoton, Sanusi Bature D-Tofa

Lokacin karatu: Minti 2

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar NNPP, inda ya ce ya ɗauki matakin ne saboda ɓarakar da ya ce ta yi wa jam'iyyar katutu.

Abba ya ce rikicin cikin-gida da ya dabaibaye jam'iyyar ta NNPP ya yi yawa, wanda a cewarsa ya sa ya ɗauki wannan matakin na ficewa domin fifita buƙatun al'ummar Kano.

Ficewar na ƙunshe ne a cikin a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Juma'a.

A cikin sanarwar, ya ce gwamnan ya aika wasiƙar ficewa daga jam'iyyar NNPP zuwa shugaban jam'iyyar na mazaɓar Diso-Chiranci ta ƙaramar hukumar Gwale.

A wasiƙar, ya ce, "na rubuta wannan wasiƙar ne domin bayyana maka a hukumance cewa na fice daga jam'iyyar NNPP daga ranar Asabar, 25 ga Janairun 2026," kamar yadda sanarwar ta nuna.

Gwamna Abba ya yi godiya ga jam'iyyar bisa damar da ya ce ya samu ta takara a cikinta.

"Ina matuƙar godiya ga jam'iyyar bisa damar da ta ba ni, da kuma goyon bayan da ƴan jam'iyyar suka ba ni tun daga 2022."

Ƙaramar magana ta zama babba

A ƙarshen shekarar da ta wuce ne aka fara raɗe- raɗin cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf zai ficewa daga jam'iyyar NNPP ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC mai mulki a matakin tarayya.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Lamarin ya ƙara ɗaukar hankali ne lokacin da aka ji cewa gwamnan zai tafi ne ba tare da mataimakinsa da kuma jagoran jam'iyyar, Rabi'u Musa Kwankwaso ba.

Cikin ƙanƙanin lokacin lamarin ya ɗauki zafi, inda mabiya Kwankwasiyya a jihar suka shiga wani halin na ruɗani.

Duk da cewa ba a samu tabbacin ko Abba ya raba gari da ubangidan nasa, Rabi'u Musa Kwankwaso ba, bayanai na nuna cewa tsohon gwamnan na Kano ya kaɗu da batun.

A halin yanzu za a iya cewa kai ya rabu sannan mabiya na cikin ruɗu dangane da wane ɓangaren za su bi, Abba ko Kwankwaso?

Tuni dai jagoran NNPP ɗin ya gargadi ƴan jam'iyyar masu shirin koma wa jam'iyyar APC mai mulki, inda a kwanakin baya aka ruwaito shi yana cewa "babu wani mutum da ya yi butulci kuma ya samu nasara."

A wani bidiyo da ya karaɗa shafukan sada zumunta a kwanakin baya, Kwankwaso ya ce, "Na yi mamakin ganin fuskokin wasunku da dama a nan - ku faɗa wa masu shirin sauya sheƙa cewa babu wani mutum da ya yi butulci kuma ya samu nasara - Wani yana tunanin ya yi butulci na shekara 10 kuma yana ganin kamar ya ci nasara amma idan ka kalle shi za ka ga ya faɗi ƙasa wanwar…" in ji Kwankwaso.

Rikicin jam'iyya

Ana tsaka da maganar, sai kwatsam wata sabuwar ɓaraka ta ɓarke, inda aka fara zargin tsohon shugaban jam'iyyar NNPP na jihar, Hashim Dungurawa da hannu a kitsa rikici, zargin da ya musanta.

Sai duk da haka, jam'iyyar NNPP a mazaɓar Gargari da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa ta ta sanar da korar Dungurawa daga jam'iyyar, duk da cewa na hannun Kwankwaso ne.

Ana cikin haka kuma uwar jam'iyyar ta sanar da rushe shugabancin tun daga matakin mazaɓa har zuwa jihar baki ɗaya, lamarin da ya ƙara haifar da zaune tsaye a siyasar jihar.

Tuni dai aka fara ganin magoya bayan ɓangaren gwamna da na Kwankwaso suna cacar baki a kafofin sadarwa, inda suke kiran juna da 'a ci daɗi lafiya' domin bayyana tsagin Gwamna, da "ƴan wuya ba ta kisa" domin bayyana tsagin Kwankwaso.

Tuni wasu masu riƙe da muƙaman gwamnati suka fara bayyana ficewarsu daga jam'iyyar NNPP.

Yanzu abin jira a gani shi ne yadda ƴan Kwankwasiyya, waɗanda suka daɗe a tare za su iya rabuwa zuwa ga mubaya'a ga Gwamna Abba da masu mubaya'a ga Kwankwaso.