Me ya sa ba a son bai wa wanda ya yi hatsari ruwa?

Haɗari

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Idan mutane suka yi haɗari, a kan samu mutane da suke ba su ruwan sha domin hankalin su ya kwanta, lamarin da masana lafiya suke ganin hakan bai dace ba a mahangar ilimi.

A tattaunawar da muka yi da Dokta Umar Sani Ibrahim, na ɓangaren kula da kiwon lafiyar a al'umma na asibitin koyarwa na Jami'ar Jihar Kaduna, wato Barau Dikko, ya ce bai wa waɗanda suka yi haɗari ruwan sha na da illa.

A cewarsa, akwai wasu abubuwa guda uku da suke faruwa idan an ba wanda ya haɗari ruwa kamar haka:

"Na farko shi ne idan an yi haɗari, akwai yiwuwar wani ya ɗimauce, hankalinsa ya gushe, bai ma san inda yake ba, amma yana maganganu. Irin wannan ruwan sha zai iya shaƙe su.

Ya ƙara da cewa shaƙewar za ta taɓa maƙoshi wato biyowa ta hanyar iska, lamarin da ke janyo wata cuta da ake kira Pneumonitis wadda ke taɓa huhu. Idan ba a yi dace ba, mutum na iya rasa ransa.

"Na biyu akwai hatsarin da babu jini ko wani rauni a zahiri, amma wataƙila akwai rauni a cikin jiki ko fashewar wata gaɓa a cikin jikin. Idan aka ba shi ruwa zai sa zubar jini ta ƙaru."

"Na uku, idan wanda ya yi haɗari ya samu raunin da ke buƙatar za a masa tiyata. Idan ya sha ruwa zai iya ja masa matsala. Idan aka masa allurar rage raɗaɗi.

Taimakon farko

Dokta Umar Sani Ibrahim

Asalin hoton, Dokta Umar Sani Ibrahim

Likitan ya ce a maimakon farawa da ba mutum ruwan sha bayan haɗari, akwai wasu matakan agajin gaggawa da suka fi dacewa.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Dr Umar ya ce abu mafi muhimmanci da zarar ka isa wajen da aka yi haɗari shi ne ƙoƙarin sanar da hukuma, "ko dai ka kira asibiti ko jami'an agajin gaggawa kafin ka fara wani abu."

Ya ce bayan an kira waɗanda abin ya shafa, sai mutum ya kula da kyau da wajen da aka yi haɗarin, "domin yana da kyau ka kula domin kada ka faɗa wani haɗari a ƙoƙarin taimakon wasu."

Likitan ya ƙara da cewa idan haɗarin ya rutsa da mutane da yawa, sai mutum ya natsu ya tantance mutanen.

"Idan akwai waɗanda suke ihu da waɗanda ba sa motsi, da kuma waɗanda suka koma gefe suka yi shiru. To akwai tsarin da muke kira ABCD protpcol."

Likita ya yi abin da ake nufi da haruffan kamar haka:

  • A- Hanyar iska, wato a duba hanyoyin iska.
  • B- Numfashi, wato a duba numfashi.
  • C- A duba yadda jini ke gudana.
  • D- Irin nakasa da aka samu
  • E- Kula da yanayin wurin.

Likitan ya ce idan akwai masu ihu, "sai ka bar su saboda suna numfashi, ka fara duba waɗanda ba sa motsi ko suka yi shiru domin sun fi buƙatar agajin gaggawa saboda a samu damar ware waɗanda za a taimaka musu su fara numfashi."

Ya ce bayan duba numfashi ne za a duba yanayin gudanar jini, wanda a cewarsa yawanci masana harkar lafiya ne suka fi iyawa.

Ya ce yawanci wajen kwashe mutane ne ake samun matsala. "Idan mutum ya ji rauni misali a wuya, dole a bi hankali wajen ɗaga shi. Haka ma idan karaya ce a ƙafa, dole a kula wajen ɗaga shi. Idan ba a kula ba, sai a ƙara tsananta masa ciwo."

Likitan ya ƙara da cewa ko da gama-garin mutane, waɗanda ba su da ilimin kiwon lafiya, za su iya bayar da gudunmuwa musamman wajen kiran asibiti da kula da wurin da sauran abubuwa.

"Abin da ake buƙata shi ne za a iya amfani da rigarsa ko wani ƙyallen a danne wurin da jini ke zuba domin a tsayar da jini kafin zuwan ma'aikatan asibiti da na agaji," in ji shi.

Dr Umar ya ƙara da cewa bai dace ba a riƙa gaggawar cire ƙarfe ko wani abu da ya caki wanda ya yi haɗari.

"A riƙa bari sai an je asibiti likitoci su cire. Babu laifi a yanke wanke ke jikin misali mota ko wani abu, amma wanda yake jikin mutun, a bari sai an je asibiti likita cire da kan shi."