Darasin da muka koya daga Gasar Kofin Nahiyar Afirka ta 2025

Asalin hoton, Getty Images/Reuters
- Marubuci, Rob Stevens
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport Africa
- Lokacin karatu: Minti 7
Za a shafe tsawon lokaci ana tunawa da yadda aka ƙare gasar kofin nahiyar Afirka ta 2025 da ta gudana a Moroko.
An samu hargitsi a yayin da aka kusa tashi daga wasan ƙarshe, lokacin da bugun fenaritin da aka bai wa Moroko ya kai ga cewa ƴan wasan Senegal sun fice daga filin wasa, lamarin da ya haifar da jinkiri na sama da minti 16.
Daga baya ɗan wasa Brahim Diaz ya ɓarar da fenaritin.
Mai horas da tawagar Atlas Lions ta Moroko, Walid Regragui ya bayyana lamarin a matsayin "abin kunya", amma har yanzu Hukumar ƙwallon Ƙafa ta Afirka ba ta sanar da wani hukunci ba kan lamarin.
To sai dai akwai abubuwa da dama game da gasar.
Rikicin da aka samu a lokacin wasan na ƙarshe bai kamata ya ɗauke hankulan al'umma daga abubuwa da dama da suka faru a gasar ba, wadda a lokacinta ne aka ci ƙwallaye mafi yawa.
Sashen wasanni na BBC Africa ya duba wasu daga cikin darussan da aka koya a lokacin gasar ta Moroko.
Kayan aiki masu kyau
Babu shakka ƙasar Moroko ta shirya gasa mai ƙayatarwa, filayen wasan masu kyau, inda filin wasa na Yarima Moulay Abdellah da ke babban birnin ƙasar ya zama abin kallo.
Karɓar baƙuncin wannan gasa ta Afcon wani ɓangare ne na shirye-shiryen ƙasar na karɓar baƙuncin Gasar Kofin Duniya ta 2030, inda za ta yi haɗin gwiwa da Spain da kuma Portugal.
Ƙasar ta arewacin Afirka ta zuba jari sosai a baya-bayan nan tare da goyon bayan Sarki Mohammed na VI, wanda ya ce kayan da ƙasar ta samar ya nuna "juriyarta da kuma ƙwarewa wajen shiri kamar kowace ƙasa a duniya."
Ana sa ran ƙasar za ta ƙara inganta kayan da ta samar, inda yanzu haka ake shirin yin gyare-gyare ga filin wasa na Mohammed V da ke birnin Casablanca da wasu a biranen Fes da Marrakesh da Agadir - haka nan kuma ake ci gaba da aikin gina filin wasa na Benslimane mai ɗaukar ƴan kallo 115,000.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Filayen wasan sun kasance masu inganci, duk da irin ruwan da ake tafkawa, wanda ya zama babban ƙalubale ga ƙasar.
"Muna alfahari da ci gaban da muke da shi harkar ƙere-ƙere," kamar yadda Omar Khyari na Hukumar ƙwallon ƙafa ta Kamaru ya shaida wa sashen wasannin motsa jiki na BBC.
"Muna farin ciki ganin cewa wannan ya nuna wa duniya cewa ita ma Afirka za ta iya yin wasu abubuwan fiye ma da wasu ƙasashen duniya."
Ƴan jarida daga Gabashin Afirka sun yi mamakin abin da suka gani, sai dai zai yi wahala ƙasashen da za su ɗauki baƙuncin gasara a gaba, wato Kenya da Tanzaniya da Uganda su iya samar da kaya masu kyawu kamar wannan.
Shugaban Hukumar ƙwallon ƙafa ta Kenya, Hussein Mohammed ya amince cewa Moroko ta "ciri tuta" a batun karɓar baƙuncin gasar Afcon, sannan ya ce Kenya na ɗaukar matakan da suka dace domin samar da kayan aiki masu kyau a gasar 2027.
Har yanzu ba a sanar da takamaiman lokacin da za a buga gasar da Kenya da Tanzaniya da kuma Uganda za su ɗauki baƙunci ba.
Ƙaruwar samun kuɗi

Asalin hoton, Reuters
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka ta ce kudin da take samu a lokacin gasar sun ƙaru da kimanin kashi 90%, inda kuɗin tikitin kallon wasa ya taka muhimmiyar rawa, inda ya ƙaru daga dala miliyan 11 a shekarar 2023 a ƙasar Ivory Coast zuwa dala miliyan 55 a Moroko.
Haka nan an samu ƙarin kamfanoni masu ɗaukar nauyi zuwa 23, sannan kuma darajar gasar ta ƙaru sanadiyyar tallata gasar a shafukan sada zumunta.
A shekarar da ta gabata hukumar CAF ta yi hasashen samun ƙarin kudaden shiga sama da dala miliyan 114 a lokacin gasar, daga dala miliyan 75 a shekaru biyu da suka gabata.
Da wannan ƙarin kudade da kuma shaharar gasar, za a yi mamakin me ya sa CAF ta yanke shawarar mayar da gasar zuwa shekara hurhuɗu daga shekarar 2028 daga shekara bibbiyu - da kuma ko abu ne mai yiwuwa a samu irin waɗannan kuɗaɗe idan aka yi gasar a wata ƙasa, ba Moroko ba, wadda za ta karbi baƙuncin gasar cin kofin Afirka ta mata baya ga ta maza.
Asisat Oshoala, ɗaya daga cikin fitattun ƴan wasa mata na Najeriya ta bayyana Moroko a matsayin "shalkwatar" ƙwallon ƙafar Afirka, ta ce komawa ƙasar kowane lokaci abu ne mai "gundura".
Tambayar ita ce, shin Caf za ta so ta yi a wani wuri ba Moroko ba?
Alƙalancin wasa

Asalin hoton, Getty Images
A ɓangaren abubuwa marasa dadi kuwa, an nuna damuwa lokaci zuwa lokaci kan hukunce-hukuncen da alaƙalan wasa suka zartar.
Gabanin karawar kusa da na ƙarshe da Najeriya, ta kai ga cewa har sai da mai horas da Moroko, Walid Regragui ya yi ƙoƙarin yayyafa ruwa kan raɗe-radin da ke cewa alƙalan wasa na taimaka wa Moroko.
"Na kalli wasanni da dama, rikicin da ake samu iri ɗaya a ko ina, ko da a Afirka ne ko Turai," a cewar shi.
Wani babban lamari game da irin wannan taƙaddama shi ne abin da ya faru a wasan ƙarshe, inda alƙalin wasa Jean-Jacques Ndala ya tafiyar da al'amura a tsanake, har sai a kusa da ƙarshen wasan, inda lamurra suka taɓarɓare cikin ƙanƙanin lokaci.
Matakin da lafarin ya ɗauka na bai wa Moroko bugun fenariti ya sanya wasu sun yi tunanin akwai rashin adalci, lamarin da ya kai ga cewa ƴan wasa sun fita daga fili.
Amfani da fasahar VAR wajen taimaka wa alƙalin wasa a baya-bayan nan ya zamo abu mai ruɗani, tun bayan amfani da shi da aka yi a 2023.
A wasu lokutan an kwashe lokaci mai tsawo ana duba VAR ɗin idan aka samu fawul ko kuma ana tunanin akwai fenariti.
Tsaro a wurin ƴan kallo

Asalin hoton, Getty Images
Tawagar Senegal ta nuna damuwa kan rashin tsaro a lokacin da ta isa birnin Rabat, gabanin wasan ƙarshe, inda mutane suka takura su.
Sai kuma hatsaniyar da aka samu a cikin filin wasa, inda magoya baya suka yi artabu da jami'an tsaro a lokacin da Moroko ta samu bugun fenariti.
BBC ta kuma ga yadda a wasu lokutan ake sanya magoya baya cikin kwana a wajen filayen wasanni.
Kula da dandazon mutane abu ne mai matuƙar wahala a kowane wuri, ba a gasar kofin Afirka kawai ba, kamar yadda aka gani a lokacin gasannin cin kofin nahiyar Turai a 2020 da kuma ta Zakarun Nahiyar Turai a 2022.
Haka nan kafin wasan ƙarshe hukumar ƙwallon ƙafa ta Senegal ta koka kan cewa tikitin kallon wasa ƙasa da 4,000 ne aka ware wa magoya bayanta a filin wasa mai ɗaukar mutum 69,000.
Haka nan an zura ido a ga matakin da hukumar CAF za ta ɗauka kan abin da ya faru a lokacin da aka ga yaran da ke ɗakko ƙwallo a filin wasa na ƙoƙarin ɗauke ƙwallen mai tsaron raga na Senegal Edouard Mendy.
Wasu hotunan bidiyo da ke yawa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda magoya bayan Moroko ke murna lokacin da aka sace ƙwallen mai tsaron raga na Najeriya har sau biyu a lokacin karawar kusa da ƙarshe.
Akwai buƙatar sauya doka

Asalin hoton, Getty Images
Akwai yiwuwar hukumar Caf ta duba yiwuwar sauya wasu dokokinta kan bayar da katin gargadi a matakin kifa-ɗaya ƙwala.
Jimillar ƴan wasa 20 ne suka riƙa taka-tsantsan a matakin wasan kusa da ƙarshe saboda suna jin tsoron cewa da zarar suka samu katin gargadi, hakan zai hana su buga wasan ƙarshe.
Kyaftin ɗin SEnegal Kalidou Koulibaly da ɗan wasan tsakiya Habib Diarra sun gaza buga wasan ƙarshe, kuma irin wannan abu ya kusa faruwa da mai tsaron baya na Najeriya Calvin Bassey da na Masar Hossam Abdelmaguid, in da tawagoginsu sun kai wasan na ƙarshe.
Duk da cewa akwai buƙatar ganin an tabbatar da da'a a lokacin gasa, amma masu horaswa da ƴan wasa da kuma magoya baya har ma da kafafen yada labarai za su ganin cewa ƙwararrun ƴan wasansu sun taka rawa a manyan wasanni.










