KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 22/01/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Yusuf Mohammed da Aisha Babangida da Haruna Kakangi

  1. Sojojin Sudan ta Kudu na ficewa daga babban birnin ƙasar Juba

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Akwai rahotanni da ke nuna cewa sojojin gwamnatin Sudan ta Kudu na ficewa daga babban birnin ƙasar, Juba, suna nufar arewa zuwa Jihar Jonglei, inda aka shafe kwanaki ana fafatawa da dakarun ‘yan adawa.

    A jiya, babban ƙungiyar ‘yan adawa masu ɗauke da makamai a ƙasar, wato SPLA-IO, ta bayyana cewa ta ƙwace wani muhimmin gari a wani sabon farmaki da take cewa an ƙaddamar da shi ne domin matsawa zuwa Juba.

    Sai dai hukumomin yankin sun ce sun fatattaki ƴan ƙungiyar SPLA-IO.

    Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya ƙara ƙamari ne bayan da aka tsare shugaban ƙungiyar ‘yan adawa, Riek Machar, a gidan yari tare da gurfanar da shi a gaban kotu a watan Maris na bara.

    Ana tuhumar Machar da cin amanar ƙasa da wasu manyan laifuka, kuma har yanzu yana tsare a hannun gwamnati.

  2. Ba za a bai wa waɗanda ba ƴan APC ba muƙamin siyasa – Shugaban APC

    ....

    Asalin hoton, X/Nentawe Yilwatda

    Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa duk naɗe-naɗen siyasa bayan zaɓukan 2027 za su kasance ne ga masu biyayya ga jam’iyyar APC kawai, ba ga ƙwararru ko mutanen da ba ƴan APC ba.

    Nentawe ya faɗi hakan ne a Abuja, yayin wani taro wanda ƙaramin ministan ayyuka, Bello Goronyo, ya shirya.

    Shugaban na jam'iyyar APC na ƙasa ya jaddada cewa "mulki lamari ne na siyasa, kuma duk wanda aka naɗa dole ne ya kasance yana goyon bayan jam’iyyar da ta kawo shi kan mulki".

    Wani bidiyo na jawabin nasa ya bazu sosai a kafafen sada zumunta a ranar Laraba, lamarin da ya haifar da muhawara mai zafi a tsakanin ‘yan siyasa da mambobin jam’iyya da ƙungiyoyin farar hula a faɗin ƙasar.

    A cewar Nentawe, "Duk wanda aka naɗa a gwamnati dole ne ya kasance a fili yana shiga harkokin siyasa tare da yin aiki kafada da kafada da jam’iyya."

    "Ya ce babu wani batun 'ƙwararre' idan ana magana kan muƙaman siyasa."

    Ya ƙara da cewa zai tsaya tsayin daka wajen kare matsayinsa na cewa duk wanda bai shirya yin aiki tare da APC ba, bai kamata a ba shi muƙami ba.

  3. Mutum biyu sun mutu a zaftarewar ƙasa a New Zealand

    ...

    Mutum biyu ne suka mutu yayin da ake fargabar wasu da dama sun ɓace a cikin tarkacen ƙasa sakamakon zaftarewar ƙasa a Tsibirin New Zealand ta Arewa.

    An tabbatar da mutuwar mutanen ne a Welcome Bay, yayin da ma’aikatan ceto ke ci gaba da bincike cikin ɓaraguzai a wani wurin sansanin shakatawa a dutsen Maunganui.

    Hukumomi sun ce babu “alamar masu rai” a wuraren da suka lalace sakamakon zaftarewar ƙasar.

    Zaftarewar ƙasar ta faru ne sakamakon ruwan sama mai ƙarfi da aka samu kwanakin baya, wanda ya haddasa ambaliyar ruwa da kuma katsewar wutar lantarki a Tsibirin.

    Hukumomi sun bayyana cewa za su ci gaba da bincike da aikin ceto yayin da suke ƙoƙarin tabbatar da tsaro ga duk masu ceto da sauran mutane a wurin.

  4. Mutane da dama sun ɓace bayan zaftarewar ƙasa a New Zealand

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Mutane da dama, ciki har da aƙalla ƙaramin yaro guda, sun ɓace bayan zaftarewar ƙasa a wani sansani a da ke kusa da Dutsen Maunganui, na ƙasar New Zealand.

    Masu aikin ceto suna wurin, suna ta ƙoƙarin tono waɗanda suka maƙalae a ƙarƙashin tarkace.

    Wasu mutum biyu kuma sun ɓace sannan mutum ɗaya ya samu munanan raunuka bayan zaftarewar ƙasa a kusa da Papamoa.

    Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ya yi ɓarna a akasarin yankunan tsibirin da ke arewacin ƙasar, inda bidiyo da aka wallafa a intanet ke nuna ɗimbin wuraren da ambaliyar ruwa ta mamaye.

    An ayyana dokar ta ɓaci a yankin Bay of Plenty da sassa daban-daban na tsibirin, da suka haɗa da Northland da Coromandel da Tairāwhiti, da Hauraki.

    An umurci waɗanda ke zaune a wuraren da lamarin ya shafa da su hanzarta ficewa daga yankunan.

  5. An saka ranar gudanar da zaɓen shugaban ƙasar Guinea-Bissau

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban gwamnatin sojin ƙasar Guinea-Bissau, Janar Horta N’Tam, ya sanar da cewa za a gudanar da zaɓukan shugaban ƙasa da na majalisar dokoki a ranar 6 ga Disamba.

    An bayyana hakan ne ta cikin wata dokar shugaban ƙasa da Janar N’Tam ya rattaɓa wa hannu a ranar jiya, Laraba.

    Wannan sanarwa ta biyo bayan juyin mulkin da aka yi a watan Nuwambar 2025, wanda ya kai ga kifar da tsohon shugaban ƙasa, Umaro Sissoco Embalo, a daidai lokacin da ake shirin bayyana sakamakon zaɓen shugaban ƙasa.

    Wasu masu sa ido daga yankin, ciki har da tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, sun yi zargin cewa an shirya yunƙurin juyin mulkin ne tun da farko.

    A baya, ƙungiyar ECOWAS ta ƙi amincewa da shirin gwamnatin sojin na miƙa mulki cikin shekara guda, inda ta nemi a gaggauta komawa mulkin dimokraɗiyya.

    Yanzu da aka saka ranar zaɓe a 6 ga Disamba, ana sa ido ko hakan zai haifar da sauyi mai ma’ana a ƙasar da ta shahara da yawan juyin mulki.

  6. Mazauna Kurmin Wali sun zargi hukumomi da rufa-rufa bayan sace jama'a

    ...

    Mazauna yankin Kurmin Wali da ke ƙaramar hukumar Kajuru a jihar Kaduna sun zargi hukumomi da ƙoƙarin hana yaɗuwar bayanai bayan sace mutane 177 daga coci uku da aka yi a ranar Litinin.

    Wasu mazauna yankin sun shaida wa BBC a ranar Laraba cewa jami’an gwamnati sun hana mutane magana da kafafen yaɗa labarai, tare da ƙoƙarin toshe hanyoyin shigar ‘yan jarida zuwa cikin al’ummar.

    Wani mazaunin yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro, ya ce jami’ai sun gargaɗi jama’a da su yi shiru kan harin.

    Haka kuma, BBC ta fuskanci matsala wajen isa Kurmin Wali, bayan da jami’an tsaro da na gwamnati suka fara ƙoƙarin hana su shiga yankin.

    Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya ziyarci Kurmin Wali kwana uku bayan harin, inda ya yi alƙawarin kafa sansanin soji a yankin.

    Ya kuma sanar da wasu matakan tallafi ga waɗanda abin ya shafa.

    Sai dai iyalan waɗanda aka sace da al’ummar yankin sun ce suna cikin firgici da tashin hankali.

    Da farko dai, ‘yan sanda da jami’an ƙaramar hukuma sun musanta faruwar hare-haren da sace mutanen, kafin daga bisani suka tabbatar da cewa lamarin ya faru.

  7. An samu wata ƴar jarida da laifin tallafawa ayyukan ta'addanci a Philippines

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    An samu wata ƴar jarida a ƙasar Philippines da laifin bayar da kuɗaɗe dominj tallafawa ayyukan ta'addanci tare da yanke mata hukumcin ɗaurin aƙalla shekara 12 a gidan yari, a wani lamarin da ƙungiyoyin kare ƴancin ƴan jarida suka bayyana a matsayin rashin adalci.

    An kama Frenchie Mae Cumpio, ƴar shekara 26 a watan Fabrairun 2020 bayan da sojoji suka kai farmaki gidanta da tsakar dare inda aka yi zargin sun samu gurneti da bindiga, da kuma tutar ƴan gurguzu a ƙarƙashin gadonta.

    Ƙungiyoyin kare haƙƙi sun yi watsi da tuhume-tuhumen inda suka ce an kama ƴa jaridar ne saboda ta kasance mai sukar ƴan sanda da sojoji.

    Masu lura da al'amura dai na cewa, an ƙara ƙaimi wurin take haƙƙin ƴan jarida da masu fafutuka a ƙarƙashin shugabancin Rodrigo Duterte, wanda ya ƙaddamar da mummunan shirin yaƙi da miyagun ƙwayoyi daga shekarar 2016 zuwa 2022.

    A ranar Alhamis, bayan shafe shekara shida a gidan yari ba tare da shari’a ba, an wanke Cumpio daga tuhumar da ake mata na mallakar makamai da bama-bamai ba bisa ƙa’ida ba, amma an same shi da laifin bayar da kuɗaɗe domin tallafawa ayyukan ta’addanci.

  8. An kashe ƴan jarida uku a wani harin da Isra'ila ta kai a Gaza

    ...

    Asalin hoton, EPA

    Ma’aikatan bayar da agajin gaggawa sun ce an kashe falasɗinawa ƴan jarida guda uku a wani harin da Isra'ila ta kai a tsakiyar Gaza.

    Hukumar kare haƙƙin farar hula a Gaza ta ce an kashe ƴan jaridan ne bayan an kai wa motarsu hari a yankin al-Zahra inda ta bayyana sunayensu da Mohammed Salah Qashta da Anas Ghneim da kuma Abdul Raouf Shaat. An fahimci cewa suna aiki ne da wata ƙungiyar agaji ta Masar.

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai hari kan wasu da ake zargi da yin amfani da wani jirgi mara matuki da ke da alaka da Hamas... ta hanyar da ke barazana ga dakarunta. Inda ta ƙara da cewa tana kan gudanar da bincike kan lamarin.

    Ma'aikatar lafiya ta Hamas ta sanar da cewa, an kashe wasu mutane takwas, biyu daga cikinsu yara kanana da makaman atilare na Isra'ila a Gaza a ranar Laraba.

    Likitoci sun ce mutane uku ciki har da wani yaro ɗan shekara 10, sun mutu sakamakon Harbin da tankokin yaƙin Isra'ila suka yi a wani wuri a tsakiyar Gaza, kuma wani yaro dan shekara 13 da wata mata sun mutu sakamakon harbin da sojojin Isra'ila suka yi a kudancin yankin Khan Younis, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.

    Aƙalla Falasdinawa 466 ne aka kashe a Gaza tun bayan da aka fara tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas a ranar 10 ga Oktoba, a cewar ma'aikatar lafiya.

  9. 'Ba zan huta ba, sai mun ceto mutanenmu da aka sace'

    ...

    Asalin hoton, X/UBA SANI

    Gwamnan jihar Kaduna Malam Uba Sani ya ce gwamnatinsa za ta yi duk abin da ya dace domin ceto mutanen da aka yi garkuwa da su a ƙauyen Kurmin Wali da ke ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar.

    Gwamnan ya ce yana bibiyar ƙoƙarin da jami'an tsaro ke yi game da batun, kuma ba zai gajiya ba har sai an yi nasarar ceto dukkan mutanen da aka sace.

    A ranar Lahadi wasu mahara suka shiga ƙauyen Kurmin Wali inda rahotanni ke cewa sun yi garkuwa da mutane fiye da 170 tare da jefa al'ummar yankin cikin ruɗani.

    Da farko ƴansanda da jami'an gwamnatin jihar Kaduna sun musanta faruwar lamarin amma daga baya suka fitar da sanarwar da ke tabbatar da shi, duk da cewa kawo yanzu babu haƙiƙanin bayani kan ko mutane nawa ne aka sace a ƙauyen.

    Amma a hirar shi da BBC a Kaduna, gwamna Uba Sani ya ce gwamnatinsa ta karkata ne ga aikin ceto mutanen, don haka sanin yawan su wani abu ne da zai iya zuwa daga baya domin a cewarsa masu ''siyasantar'' da batun tsaro ne ke mayar da hankali kan yawan mutanen da aka sace.

  10. Trump ya ce an tattauna tsarin yarjejeniya kan Greenland bayan ya janye barazanar ƙaƙaba haraji

    Donald Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Donald Trump ya ce Amurka na nazarin yiwuwar ƙulla yarjejeniya kan Greenland bayan tattaunawa da ƙungiyar tsaro ta NATO yayin da ya janye barazanar sanya haraji kan ƙawayensa na Turai da suka yi adawa da shirin Amurka na mallakar tsibirin.

    A saƙonnin da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Trump bai bayar da cikakkun bayanai game da tattaunawar tsakaninsa da NATO ba, amma ɓangarorin biyu sun bayyana tattaunawar a matsayin "mai matuƙar tasiri".

    Sai dai babu wani abin da ya yi nuni da cimma yarjejeniyar da za ta biya buƙatar Trump na "mallakar" Greenland, burin da ya sake jaddadawa a taron tattalin arzikin duniya a Switzerland, yayin da ya yi watsi da batun amfani da ƙarfin soja.

    Bayan ganawa da Sakatare Janar na NATO Mark Rutte a Switzerland, Trump ya shaidawa manema labarai cewa akwai yiwuwar yarjejeniyar za ta iya ƙunsar batun mallakar ma'adinan da ke tsibirin.

  11. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Alhamis.

    Kamar kullum, yau ma za mu kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara kan labaran da mu ke wallafawa.