Abin da na gano a bincikena kan auratayya a Kano - Sarki Sanusi

..

Asalin hoton, Sanusi/X

Lokacin karatu: Minti 4

Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya ce dole ne a gyara zamantakewar aure a tsakanin ma'auarata a jihar Kano kasancewar matsalar ce ta fi damun al'ummar jihar Kano.

Sarkin na Kano ya ce ƙararrakin ciyarwa su ne kaso mafi yawa na shari'o'in aure da aka fi samu cikin kotunan jihar a shekarun baya-bayan nan.

Wannan wani ɓangare ne na kundin binciken digiri na uku na dokar shari'ar Musulunci da Khalifa Muhammadu Sanusi ya rubuta bayan kammala karatunsa a Jami'ar London.

Binciken da Sarki Sanusi ya yi

"Na yi rubutana ne akan abun da ake kira "Taqnin" da Larabci wato rubuta doka a tsarin layi kaza ko sakin layi kaza a shari'ar aure ta Musulunci da yadda za a yi amfani da wannan doka wajen gyare-gyare a cikin rayuwar al'umma."

"Na yi wannan ne a kan wata doka da muka nemi mu fitar da ita a Kano a wancan lokacin da muka zauna. Mun ma kafa kwamiti da ya haɗa da malamai na zaure da na jami'a da lauyoyi. An yi doka wadda ta shafi aure da saki da gado da waƙafi da wasiyya..."

"To na ɗauki wannan dokar wadda a kanta na gina sai kuma na ɗauki dokar ƙasar Morocco a 2014 sai na yi "muƙarana" a tsakaninsu."

"Babban abin da muka so mu duba na farko shi waɗanne matsaloli ne suka damu ma'aurata a Kano kuma ta wace hanya wannan dokar za ta iya warware waɗannan matsalolin. Kuma wannan dokar da muka yi a yadda muka yi ta ko ta isa ko tana buƙatar mu yi mata kwaskwarima. Sannan akwai wani abu da za mu iya koya daga wajen Morocco. Ko kuma su za su iya amfana da dokarmu." In ji Sarki Muhammadu Sanusi.

Bincike kan matsalar ciyarwa

..

Asalin hoton, Sanusi/X

Yayin binciken Sarkin Muhamamdu Sansusi ya ce ya ɗauki shari'o'i kan al'amuran aure daga kotuna da dama na Kano da kuma hukumar Hizba domin yin nazari.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Mun ɗauko bayanai kamar daga wurare guda biyar: Na farko dai akwa kotunan shari'a a Kano, inda muka ɗauki guda tara, uku a Kano ta tsakiya, uku daga Kano ta Arewa da kuma uku daga Kano ta Kudu...kuma mun ɗauki shari'o'insu na shekara biyar inda muka samu shari'a kamar 12,000 waɗanda sun shafi harkar aure."

"Sannan muka karkasa su cikin babi-babi na fiƙihu na abin da ya shafi harkar aure kamar a ciyarwa ko cutarwa da saɓani da aibi da zamantakewar mata a cikin harkar auratayya da yawa."

"Sannan muka je Hizba mu ka ɗauki shari'o'in da ake kai wa gaban Hizba. Sannan muka je littafin gaban Sarki. Shi ma muka duba shekara biyar na irin ƙararrakin da mata ke kawowa a gaban sarki...ta nan ne muka gane mene ne ke damun mata. Shi ne mafi yawa abin da ake fama da shi ne ciyarwa.

"Kuma wannan yana da alaƙa da talauci. Kashi 41 cikin 100 na dukkan shari'un da aka kawo gaban alƙali ya shafi ciyarwa. Ko dai ciyarwa lokacin aure ko bayan saki."

"Mun kuma gano ra'ayin wasu malamai kamar Ibnu Hazm Azzahiri a littafinsa "Muhalla". Shi ra'ayinsa shi ne idan miji ba zai iya ciyar da matarsa ba. Kuma ita ma ba ta da halin ciyar da kanta. Kuma ɗansa ko mahaifinsa ba za su iya ba. To duk wani mutumin da yake da gadon wannan matar...to a ɗora masa nauyin ciyar da ita." Kamar yadda Sarki Sanusi ya yi ƙarin haske.

Dukan mata

..

Asalin hoton, Sanusi/x

Wani abu kuma bayan matsalar ciyarwa shi ne dukan mata da zagi da cin mutunci inda aka samu fiye da kashi 30 na ƙararrakin da ake kai wa gaban alƙalai.

"A Morocco an bai wa mata damar zuwa su ce a raba aure saboda "shiqaq" wato matsalolin saɓani. To amma wannan ƙofar da aka buɗe ba ta hanyar "Kuli'i" sai ya janyo ya buɗe ƙofar mutuwar aure masu yawa.

Auren kananan yara

Sarki Muhammadu Sanusi ya ce wani abun da ya fahimta shi ne idan ana son a kawo ƙarshen yi wa ƙananan yara aure dole ne sai gwamnati ta taka muhimmiyar rawa.

"Har yanzu ina kan ra'ayin lallai ya kamata a bar yarinya sai ta girma a yi mata aure. Kuma a cikin bincike abubuwa da dama sun bayyana. Misali a ƙasarmu ma ba ma rubuta ranar haihuwa. Saboda haka ko an yi dokar, idan mahaifin yarinya ya ce shekarar ƴarsa 18, wane ne kai ka ce ba haka ba ne ba."

"Saboda haka kafin a magance matsalar auren ƙananan yara dole ne sai an haɗa da wa'azi da gina makarantu da ajiye malamai da tallafawa talakawa."

Sako ga matasa

Sarki Sanusi ja hankalin matasa game da matuƙar muhimmancin tattalin lokaci a rayuwarsu ta hanyar neman ilmi da shiga al'amura masu ma'ana tun suna kan ganiyarsu maimakon shafe tsawon lokaci a shafukan sada zumunta.

"Matasa suna ɓata lokacinsu kuma idan aka duba za ka ga matasan Kudu ba haka suke yi ba. Matasan Yarabawa da Igbo suna can suna karatu suna ilimi. Idan namu ba su yi hankali ba to za su zama bayin wadancan tunda mu za mu tafi ne. Saboda haka cigaban ƙasarmu ya dogara ne kan ilimin yaranmu maza da mata..." A kalaman Sarki Muhammadu Sanusi.